النساء

تفسير سورة النساء آية رقم 12

﴿ﭑﭒﭓﭔﭕﭖﭗﭘﭙﭚﭛﭜﭝﭞﭟﭠﭡﭢﭣﭤﭥﭦﭧﭨﭩﭪﭫﭬﭭﭮﭯﭰﭱﭲﭳﭴﭵﭶﭷﭸﭹﭺﭻﭼﭽﭾﭿﮀﮁﮂﮃﮄﮅﮆﮇﮈﮉﮊﮋﮌﮍﮎﮏﮐﮑﮒﮓﮔﮕﮖﮗﮘﮙﮚﮛﮜﮝﮞﮟﮠﮡﮢﮣﮤﮥﮦﮧﮨﮩﮪﮫﮬﮭﮮﮯﮰﮱﯓﯔ ﴾

﴿۞ وَلَكُمْ نِصْفُ مَا تَرَكَ أَزْوَاجُكُمْ إِنْ لَمْ يَكُنْ لَهُنَّ وَلَدٌ ۚ فَإِنْ كَانَ لَهُنَّ وَلَدٌ فَلَكُمُ الرُّبُعُ مِمَّا تَرَكْنَ ۚ مِنْ بَعْدِ وَصِيَّةٍ يُوصِينَ بِهَا أَوْ دَيْنٍ ۚ وَلَهُنَّ الرُّبُعُ مِمَّا تَرَكْتُمْ إِنْ لَمْ يَكُنْ لَكُمْ وَلَدٌ ۚ فَإِنْ كَانَ لَكُمْ وَلَدٌ فَلَهُنَّ الثُّمُنُ مِمَّا تَرَكْتُمْ ۚ مِنْ بَعْدِ وَصِيَّةٍ تُوصُونَ بِهَا أَوْ دَيْنٍ ۗ وَإِنْ كَانَ رَجُلٌ يُورَثُ كَلَالَةً أَوِ امْرَأَةٌ وَلَهُ أَخٌ أَوْ أُخْتٌ فَلِكُلِّ وَاحِدٍ مِنْهُمَا السُّدُسُ ۚ فَإِنْ كَانُوا أَكْثَرَ مِنْ ذَٰلِكَ فَهُمْ شُرَكَاءُ فِي الثُّلُثِ ۚ مِنْ بَعْدِ وَصِيَّةٍ يُوصَىٰ بِهَا أَوْ دَيْنٍ غَيْرَ مُضَارٍّ ۚ وَصِيَّةً مِنَ اللَّهِ ۗ وَاللَّهُ عَلِيمٌ حَلِيمٌ﴾

Kuma kunã da rabin abin da mãtanku na aure suka bari idan rẽshe bai kasance gare su ba. Sa'an nan idan rẽshe ya kasance gare su, to, kunã da rubu'i (ɗaya daga cikin kashi huɗu) daga abin da suka barin, daga bãyan wasiyya wadda suka yi kõ kuma bãshi. (Sũ) kuma suna da rubu'i daga abin da kuka bari idan rẽshe bai kasance ba gare ku, idan kuwa rẽshe ya kasance gare ku, to, sunã da sumuni (ɗaya daga cikin kashi takwas) daga abin da kuka bari, daga bãyan wasiyya wadda kuka yi kõ kuwa bãshi.
Idan wani namiji ya kasance ana gãdon sa bisa kalãla, ko kuwa wata mace alhãli kuwa yana da ɗan'uwa kõ 'yar'uwa* to, kõwane ɗaya daga cikinsu yana da sudusi (ɗaya daga cikin kashi shida), sai idan sun kasance mafi yawa daga wannan, to, sũ abõkan tãrayya ne a cikinsulusi (ɗaya bisa uku), daga bãyan wasiyya wadda aka yi kõ kuma bãshi. Bã da yana mai cũtarwa ba, ga wasiyya, daga Allah. Kuma Allah Masani ne Mai haƙuri.

الترجمة الهوساوية

ترجمة معاني القرآن الكريم للغة الهوسا ترجمها أبو بكر محمود جومي، نشرها مجمع الملك فهد لطباعة المصحف الشريف بالمدينة المنورة، عام الطبعة 1434. ملاحظة: ترجمات بعض الآيات (مشار إليها) تم تصويبها بمعرفة مركز رواد الترجمة، مع إتاحة الاطلاع على الترجمة الأصلية

الترجمات والتفاسير لهذه الآية: