Yayibayani ne akanTauhidi da kumafa’idojinsa, da hatsarindakecikinshirka da munafunci da ayyukanjahiliyya, kumayayibayaniakankongiyoyinawannanzamanikamarwadandasukemusunakwai Allah da kwaminisanci, da kumahukuncinshigaciki, hakananyayi Magana akanhakkokinAnnabi, da naiyalanshi da nasahabbanshimasudaraja, yaambacibidi’o’i da bayyanarsu da kumahatsarindakecikinta, da takaitaccanmisaliakanbidi’o’inwannanlokacin.
التفاصيل
KITABUT TAUHID Gabatarwa Mai Fassara Gabatarwar Mawallafi: BABI NA FARKO: Karkatar da aka samu a rayuwar Dan’adam, da kuma takaitaccan bayani akan kafirci da kuma ilhadi da shirka da munafunci. Fasali Na Farko: Fasali Na Biyu: Fasali Na Uku: Fasali Na Hudu: Fasali Na Biyar: BABI NA BIYU: Fasali Na Farko: Fasali Na Biyu: Fasali Na Uku: Fasali Na Hudu: Fasali Na Biyar: Fasali Na Shida: Fasali Na Bakwai: Fasali Na Takwas: Fasali Na Tara: Fasali Na Goma: Fasali Na Goma sha daya: BABI NA UKU: Fasali Na Farko: Fasali Na Biyu: Fasali Na Uku: Fasali Na Hudu: Fasali Na Biyar: Fasali Na Shida: BABI NA HUDU: Fasali Na Farko: Fasali Na Biyu: Fasali Na Uku: Fasali Na Hudu: KITABUT TAUHIDWallafar:Sheikh: Salihu bn Fauzan bin Abdallahil Fauzan.FassararAliyu Muhammad SadisuWanda ya duba:Attahiru Bala Dukku Gabatarwa Mai FassaraDa sunan Allah mai yawan rahama mai yawan jinkai. Dukkan godiya ta tabbata a gareshi, kuma tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad ﷺ da iyalanshi da kuma sahabbanshi baki-daya. Bayan haka, wannan fassarar littafin “Kitabut Tauhid” ne, wanda Shehun malami Dr. Saleh bin Fauzan bin Abdallah Alfauzan ya wallafa, wannan malami fitaccan malami ne mamba ne a majalisar manyan malamai ta kasar Saudi Arebiya, kuma mamba a kwamitin dindindin na fatawa da kuma bincike akan ilimi. Wannan littafi na Tauhidi da wannan malami ya wallafa ya taba bangarori da dama wadanda ake matukar neman bayanan su a daidai wannan lokaci, zaka iya cewa littafin ya zo ne a daidai lokacin da ake matukar bukatarsa. Mawallafin littafin ya fara kawo mukiddima ne sannan ya biyo shi da babi-babi har guda hudu, sannan akar kashin kowanne babi akwai fasali-fasali da malam ya kawo. Babi na farko yana kunshe ne da fasali biyar, a yayinda babi na biyu kuma yake kunshe da fasali-fasali har goma sha-daya, shi kuwa babi na uku yana dauke ne da fasali-fasali har guda shida, ayayin da babi na karshe wato babi na hudu yake dauke da fasalai har guda hudu. Wannan littafi kamar yadda sunansa yake ‘Kitabut Tauhid’, kuma haka na Shehun malamin nan wato Sheikh Muhammad dan Abdulwahhab yake da ‘Kitabut Tauhid’ to amma sun yi tarayyane a suna amma sun sha banban a irin bayanan da suke dauke da shi, duk da bayanaine na tauhidi da kowanne yake da shi, saidai bangarorin da kowa ya dauka ya yi bayani daban-daban ne, saboda haka ana bukatar ka hada su duka ka mallake su, Allah ya anfanar da mu da su baki-daya. Lalle akwaimatukar bukatar a karantar da wannan littafi a makarantu da masallatai da kuma wuraran fadakarwa a kuma yada shi, saboda matukar muhimmancin da yake da shi da kuma yadda ya tabo wadansu bayanai da ake aikatawa a wannan lokacin da suke bukatar irin wadannan malamai su yi bayaninsu. Allah ya sakawa wannan malami da kuma wadanda suka yada wannan littafi Allah ya saka musu da alheri. Dukkan godiya ta tabbata ga Allah, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad ﷺ da iyalanshi da kuma sahabbanshi baki daya. Mai fassara;Aliyu Muhammad Sadisu,Minna,Nigeria.Email. [email protected]***** ****** ******بسم الله الرحمن الرحيم Gabatarwar Mawallafi:Da sunan Allah mai yawan rahama mai yawan jinkai, dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabinsa mai gaskiya kuma amintacce Annabimmu Muhammad da kuma iyalanshi da sahabbanshi baki daya, bayan haka: To wannan littafi an wallafa shi ne akan ilimin tauhidi, kuma hakika na yi la’akarin takaita shi ta yadda lafuzan za su yi sauki, kuma na ciro bayananne daga manyamanyan littattafai masu yawa daga cikin littattafan manyan malamammu musammamma littattafai Shekhul Islam Ibnu Taimiya, da littafan Shehun malami Ibnu Kayyim da kuma littattafan Shekhul Islama Muhammad dan Abdulwahhab da na almajiransa jagororin wannan Da’awah mai tarin albarka. Kuma yana daga cikin abinda kwatakwata babu wani kokwanto akai shi ne: Lalle ilimin sanin ‘Akidar Musulunci’ shi ne babban tushen da ya fi cancantar a kula da shi da wajan koyo da kuma koyarwa da kuma aiki da shi, domin da shi ne ayyuka za su zama karbabbu a wurin Allah, ta zama mai amfani ga wadanda su ka yi su, musamman a wannan zamani da ake fama da akidu iri daban-daban; Akidun masu ilhadi, ga akidun sufaye ga maguzawa masu bautar kabari, ga kuma akidu na bidi’o’I da suka sabawa karantarwar Annabi ﷺ. Dukkanin wadannan akidune masu matukar hadari muddin mutum musulmi bai kasanke yana da shiri na kyakkyawar akidah ba wacce ta ginu akan littafin Allah da Sunnar Annabinsa ﷺ da kuma abinda magabatan wannan al’umma na kwarai suka kasance kai ba to kan in ya yi wasa tuni wadancan akidu za su masu batarwa za su debe shi. Wannan ko yana cikin abinda zai sa a bada cikakkiyar kulawa akan karantar da ingantacciyar akida ga ‘ya’yan musulmi daga tushenta na asali. Allah ya yi dadin tsira ga Annabimmu Muhammad ﷺ da iyalanshi da kuma sahabbanshi.Mawallafi. BABI NA FARKO: Karkatar da aka samu a rayuwar Dan’adam, da kuma takaitaccan bayani akan kafirci da kuma ilhadi da shirka da munafunci.Wannan ko ya kunshi wadannan fasalin ne:Fasali Na Farko: Karkata a rayuwar dan’adam.Fasali Na Biyau: Shirka, bayaninta da nau’ukanta.Fasali Na Uku: kafirci, bayaninsa da nau’ukansa.Fasali Na Hudu: Munafunci, bayaninsa da kuma nau’ukansa.Fasali Na Biyar: Hakikanin abinda ake nufi da wadannan abubuwan:(1) Jahiliyyah.(2) Fasikanci.(3) Bata.(4) Riddah, karkasuwarta da hukunce hukuncenta.**** ***** ***** Fasali Na Farko:Karkata a rayuwar dan’adam. Allah madaukakin sarki ya halicci halitta ne domin su bauta masa, kuma ya sawwake musu abinda zai taimaka musu na arzikinsa, Allah madaukakin sarki yana cewa:(وَمَا خَلَقۡتُ ٱلۡجِنَّ وَٱلۡإِنسَ إِلَّا لِيَعۡبُدُونِ، مَآ أُرِيدُ مِنۡهُم مِّن رِّزۡقٖ وَمَآ أُرِيدُ أَن يُطۡعِمُونِ، إِنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلرَّزَّاقُ ذُو ٱلۡقُوَّةِ ٱلۡمَتِينُ) الذاريات: ٥٦ – ٥٨Ma’ana:“Kuma ban halicci aljan da mutum ba sai domin kawai su bauta mini. Bana neman wani arziki daga gare su kuma bana bukatar da su ciyar da ni. Lalle Allah shi ne kadai mai azurtawa kuma maba’abocin karfi sosai”. Suratuz Zariyat, aya ta:56-58. Mutum a halittar da Allah ya yi masa zai bautawa Allah ne shi dakai inda za’a bar shi, ya zama mai son Allah ya na bauta masa ba ya yi ma sa shirka, sadai abinda ya bata wannan (dabi’ar) kuma yake karkatar da ita shi ne abin shedanun aljanu da na mutane su ke kawata mata na abinda sashin su yake yi wa sashi wahayi na kawatacciyar Magana kawai don rudi, shirka wata aba ce da ta zo daga baya kuma ta kutsa kai ga halittar da Allah ya yi wa mutum, Allah madaukakin sarki yana cewa:(فَأَقِمۡ وَجۡهَكَ لِلدِّينِ حَنِيفٗاۚ فِطۡرَتَ ٱللَّهِ ٱلَّتِي فَطَرَ ٱلنَّاسَ عَلَيۡهَاۚ لَا تَبۡدِيلَ لِخَلۡقِ ٱللَّهِۚ )الروم: ٣٠Ma’ana:“To, ka tsayar da fuskarka ga wannan addini kana mai kaucewa shirka, halittar Allah wacce ya halicci mutane a kan ta, babu mai canza halittar Allah”. Suratur Rum, aya ta: 30.Kuma Ma’aikin Allah ﷺ ya ce:((كُلُّ مَوْلُودٍ يُولَدُ عَلَى اَلْفِطْرَةِ، فَأَبَوَاهُ يُهَوِّدَانِهِ، أَوْ يُنَصِّرَانِهِ أَوْ يُمَجِّسَانِهِ)). رواه البخاري ومسلم.Ma’ana:“Dukkan abin haihuwa ana haihuwarsa ne akan musulunci, to iyayan shi ne su ke yahudantar da shi, ko su Nasarantar da shi (kiristan da shi) ko su majusantar da shi”. Bukhari da Muslim ne su ka ruwaito. Kenan abinda yake asali ga dukkan banu’adam shi ne tauhidi. Addini fa: Shi ne musulunci tun daga zamanin Annabi Adam -Alaihissalam- da kuma dukkanin wadanda suka zo bayan sa na zuriyar sa shekaru masu tarin yawa, Allah madaukakin sarki yana cewa:كَانَ ٱلنَّاسُ أُمَّةٗ وَٰحِدَةٗ فَبَعَثَ ٱللَّهُ ٱلنَّبِيِّۧنَ مُبَشِّرِينَ وَمُنذِرِينَ) البقرة: ٢١٣Ma’ana:“Mutane sun kasance al’umma ce guda daya, to sai Allah ya tayar da Annabawa domin su zama masu bishara da kuma gargadi”. Suratul Bakarah, aya ta: 213. Farkon lokacin da shirka da karkacewa akidar musulunci suka bayyana shi ne lokacin Annabi Nuhu u, saboda haka sai shi Annabi Nuhu u ya kasance farkon Manzo, Allah madaukakin sarki yana cewa:(إِنَّآ أَوۡحَيۡنَآ إِلَيۡكَ كَمَآ أَوۡحَيۡنَآ إِلَىٰ نُوحٖ وَٱلنَّبِيِّۧنَ مِنۢ بَعۡدِهِۦ) النساء: ١٦٣Ma’ana:“Lalle mu munyo wahayi zuwa gareka kamar yadda muka yi wahayi zuwa ga Annabi Nuhu da Annabawan da suka bayansa”. Suratun Nisa’i,aya ta: 163.Abdullahi dan Abbas –Allah ya kara musu yarda- ya ce: “Abida ya kasance tsakanin Annabi Adam da Annabi Huhu –Alaihimassalam- shi ne karni goma (Shekaru dubu)”. Ibnu Kayyim ya ce: “Wannan maganar kuma ita ce daidai yanke”. Domin a Kira’ar Ubayyi dan Ka’ab a ayar Suratul Bakarah din ya karanta ne: “Sai su ka yi sabani to sai Allah ya aika Annabawa”. Kuma abinda zai bada shaida ga wannan Kiri’ar shi fadin Allah madaukakin sarki da ya ce:وَمَا كَانَ ٱلنَّاسُ إِلَّآ أُمَّةٗ وَٰحِدَةٗ فَٱخۡتَلَفُواْۚ) يونس: ١٩)Ma’ana: “Mutane ba su kasance ba sai al’umma guda daya to sai su ka yi sabani”. Suratu Yunus, aya ta: 19. Abinda ya ke nufi –Allah ya yi masa rahama- lalle sanadiyyar turo Annabawa shi ne sabani da aka samu na barin ingantaccan addini da su ka yi, kamar yadda larabawa su ka kasance bayan haka akan addinin Annabi Ibrahin u, har zuwa lokacin da Amru dan Luhai alkhuza’i ya jirkita karantarwar Annabi Ibrahim, ya shigo da gumaka kasashen larabawa har zuwa yankin tsibirin larabawa musamman, sai kuma aka bautawa wadannan gumakan koma bayan Allah, shirka ta watsu a wannan kasa mai tsarki da makwaftanta har zuwa lokacin Allah madaukakin sarki ya aiko Annabi Muhammad ﷺ kuma cikamakin Annabawa to fa sai ya kira mutane zuwa ga kadaita Allah madaukakin sarki da kuma bin karantarwar Annabi Ibrahim u, ya yi jihadi domin daukaka addinin Allah hakikanin jihadi, har tsantsar tauhidi ya dawo haka kuma karantarwar Annabi Ibrahim ﷺ ta dawo, ya karairaya gumaka, Allah madaukakin sarki ya cika wannan addini da aiko shi ﷺ, Allah kuma ya cika ni’imarSa da ya yi wa talikai da aiko shi, kuma shekaru masu daraja suka shude akan karantarwarsa, tun daga farkon wannan al’umma har zuwa lokacin da jahilci ya yadu a shekarun da suka biyo bayan wadancan, wasu bakin abubuwa na wadansu addinai suka shiga, wannan ya sa shirka ta dawo a wurare da dama cikin wannan al’umma ta sanadiyyar masu kira akan bata da kuma sanadiyyar yin gini akan kaburburu wai don girmama waliyyai da kuma salihai, kuma ai son su da ake yi har aka gina wuraran ziyara na musamman akan kaburburan na su, haka aka rike su gumakan da ake bautawa koma-bayan Allah da nau’ukan abubuwan bauta da ake neman kusanci ga Allah da su, kamar: rokon su, da neman agajinsu da yi musu yanka da yi musu alwashi domin matsayin su. Kuma adaidai nan sai aka kira shirka da sunan tawassali da mutanan kwarai da kuma bayyanar da son su, wai ai ba bauta musu ake yi ba, kamar yadda suke cewa. Sun manta cewa wannan ai shi ne zancan mushirikan farko inda suka ce:مَا نَعۡبُدُهُمۡ إِلَّا لِيُقَرِّبُونَآ إِلَى ٱللَّهِ زُلۡفَىٰ) الزمر: ٣)Ma’ana:“Bakomai ya sa muke bauta musu ba sai domin su kusantar da mu ga Allah kusantarwa”. Suratuz Zumar, aya ta:3 To duk da irin wannan shirka da ta bayyana a rayuwar dan’adam tunda da kuma yanzu, to saidai mafi yawa daga cikin su suna yin Imani ne da tauhidin kadaita Allah da ayyukansa, amma kuma suna yiwa Allah shirka a tauhidin kadaita shi wurin bauta, kamar yadda Allah madaukakin sarki yake cewa:وَمَا يُؤۡمِنُ أَكۡثَرُهُم بِٱللَّهِ إِلَّا وَهُم مُّشۡرِكُونَ) يوسف: ١٠٦)Ma’ana: “Mafi yawansu basa yin Imani da Allah sai suna masu shirka”. Suratu Yusuf, aya ta:106. Babu wanda ya yi musun akwai Allah sai mutane ‘yankadan, kamar Fir’auna da ‘Yandahariyya, da kuma masu akidar gurguzu a wannan lokaci, kuma sudumma musun da suka yi girman kai ne, inko bahaka ba ai suna da matukar bukatar tabbatar da samuwar Allah a cikin zukatan su, kamar yadda Allah madaukakin sarki ya ce:وَجَحَدُواْ بِهَا وَٱسۡتَيۡقَنَتۡهَآ أَنفُسُهُمۡ ظُلۡمٗا وَعُلُوّٗاۚ)النمل: ١٤)Ma’ana: “Kuma sun yi musu da ita(ayoyin), kuma zukatan su sun tabbatar da su, kawai don zalunci da kuma girman kai”. Suratun Namli, aya ta:14. Zukatan su sun tabbatar musu cewa lalle dukka abinda aka halitta to dole akwai wanda ya halicce shi, kuma duk abinda ka gani samamme to dole akwai wanda ya samar da shi, kuma tsarin kasantuwar wannan duniya wacce take akwai kwarewa wurin samar da ita to lalle akwai wanda yake kula da ita kuma gwani-mai hikima kuma mai iko masani, kuma dukkan wanda ya ce ba haka ba, to kodai mara hankali ko mai girman kai da ya yar da hankalin na sa kuma ya wawantar da kansa, to ko wannan ai ba’a la’akari da shi. **** **** **** Fasali Na Biyu: Shirka, bayaninta da nau’ukanta.Bayani Akan Shirka. Idan aka ce shirka to ita ce: “Sanya wa Allah tarayya a halittarsa da kuma bauta masa”. Mafi yawan shirka anfi samunta ne a wurin bautawa Allah ta yadda mutum zai bautawa Allah tare da wanin Allah din, ko ma yakarkatar da wani abu na nau’ukan ibada ga wanin Allah; kamar yanka da alwashi da tsoro da kauna da so. Ita shirka ita ce mafi girman zunubai saboda abubuwa kamar haka:1. Domin ita shirka kamanta abinda aka halitta ne da wanda ya yi halittar a binda ya kebanci bautawa Allah kadai, saboda haka dukkan wanda ya hada Allah da wani (awurin bauta) to hakika ya kamanta wannan din da Allah, Allah madaukakin sarki na cewa:لقمان: ١٣(إِنَّ ٱلشِّرۡكَ لَظُلۡمٌ عَظِيمٞ)Ma’ana: “Lalle shirka zalunci ce mai girma”. Suratu Lukman, aya ta:13. Idan kuma akace zalunci shi ne: Sanya abu a inda ba nan ne wurin sa ba’. To dukkan wanda ya bautawa wanin Allah to hakika ya sanya ibada a inda ba nan ne wurinta ba, kuma ya karkatar da ita daga wanda ya cancanta, yin haka kuma shi ne mafi girman zalinci.2. Lalle Allah ya bayar da labarin cewa lalle shi ba ya gafartawa ga dukkan wanda ya yi shirka muddin bai tuba ba, Allah madaukakin sarki yana cewa:النساء: ٤٨(إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَغۡفِرُ أَن يُشۡرَكَ بِهِۦ وَيَغۡفِرُ مَا دُونَ ذَٰلِكَ لِمَن يَشَآءُۚ)Ma’ana:“Lalle Allah ba ya gafartawa idan aka yi masa shirka, kuma yana gafarta abinda bai kai shirk aba ga wanda ya so”. Suratun Nisi’i, aya ta:48. 3. Lalle Allah ya bayar da labarin cewa lalle shi ya haramta aljanna ga dukkan wanda ya yi shirka, kuma shi wanda zai dawwamane a wutar jahannama har abada, Allah madaukakin sarki na cewa:المائدة: ٧٢(إِنَّهُۥ مَن يُشۡرِكۡ بِٱللَّهِ فَقَدۡ حَرَّمَ ٱللَّهُ عَلَيۡهِ ٱلۡجَنَّةَ وَمَأۡوَىٰهُ ٱلنَّارُۖ وَمَا لِلظَّٰلِمِينَ مِنۡ أَنصَارٖ)Ma’ana:“Lalle shi fa dukkan wanda ya yi wa Allah shirka to hakika Allah ya haramta masa aljanna kuma makomarsa ita ce wuta, kuma azzalumai ba su da mataimaka”. Suratul Ma’idah, aya ta: 72.4. Lalle ita shirka tana bata dukkanin ayyuka, Allah ,madaukakin sarki yana cewa: الأنعام: ٨٨(وَلَوۡ أَشۡرَكُواْ لَحَبِطَ عَنۡهُم مَّا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ)Ma’ana: “Da ace sun yi shirka to da dukkan abinda suka kasance sun aikata da ya baci”. Suratul An’am, aya ta:88. Kuma Allah yana cewa:﴿وَلَقَدۡ أُوحِيَ إِلَيۡكَ وَإِلَى ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِكَ لَئِنۡ أَشۡرَكۡتَ لَيَحۡبَطَنَّ عَمَلُكَ وَلَتَكُونَنَّ مِنَ ٱلۡخَٰسِرِينَ٦٥﴾الزمر65 Ma’ana:“Kuma hakika an yo wahayi zuwa gareka da kuma zuwa ga dukkanin wadanda suka zo kafin kai (cewar) tabbas idan har ka yi shirka to wallahi da aikinka yabaci kuma da kakasance cikin asararru”. Suratuz Zumar, aya ta: 65.5. Lalle shi mushiriki jininsa da dukiyarsa halasce, Allah madaukakin sarki yana cewa:﴿فَإِذَا ٱنسَلَخَ ٱلۡأَشۡهُرُ ٱلۡحُرُمُ فَٱقۡتُلُواْ ٱلۡمُشۡرِكِينَ حَيۡثُ وَجَدتُّمُوهُمۡ وَخُذُوهُمۡ وَٱحۡصُرُوهُمۡ وَٱقۡعُدُواْ لَهُمۡ كُلَّ مَرۡصَدٖۚ فَإِن تَابُواْ وَأَقَامُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتَوُاْ ٱلزَّكَوٰةَ فَخَلُّواْ سَبِيلَهُمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٞ٥﴾ التوبة 5Ma’ana:“To ku yaki mushirikai duk inda kuka same su kuma ku kama su kuma ku tare su kuma ku tsaya musu a dukkan madakata”. Suratut Taubah, aya ta:5.Ma’aikin Allah ryana cewa: ((أمرت أن أقاتل الناس حتى يقولوا: لا إله إلا الله، فإذا قالوها عصموا مني دماءهم وأموالهم إلا بحقها)). رواه البخاري ومسلم.Ma’ana:“An umarce ni da in yaki mutane har sai sun ce: Babu abin bautawa da cancanta sai Allah, to idan suka fadeta sun kare jininsu da dukiyarsu daga gareni sai dai da hakkinta (ita Kalmar shahadar)”. Bukhari da Muslim ne suka ruwaito.6. Lalle ita shirka itace mafi girman duk wani laifi, Ma’aikin Allah ﷺ ya ce:((ألا أنبئكم بأكبر الكبائر؟ قلنا: بلى يا رسول الله. قال: الإشراك بالله، وعقوق الوالدين))رواه البخاري ومسلم.Ma’ana:“Shin ba na baku labarin laifi mafi girma ba? Sai muka ce (in ji sahabbai) Ya ma’aikin Allah, sai ya ce: Shirka da Allah, da sabawa iyaye”. Bukhari da Muslim ne suka ruwaito. Babban Shehun Malami Ibnu Kayyim ya ce: Allah mai girma da daukaka ya bayar da labari akan dalilin halittar halittu baki daya da kuma dukkanin al’amura, shi ne domin a sanshi da sunayansa da kuma siffofinsa kuma a bauta masa shi kadai kada a hadashi da wani ko wani abu (kada a yi shirka kenan). Kuma mutane su tsayu da adalci wanda yake da shi adalcinne samma da kassai suka tsayu, kamar yadda Allah madaukakin sarki ya fada:﴿لَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا رُسُلَنَا بِٱلۡبَيِّنَٰتِ وَأَنزَلۡنَا مَعَهُمُ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡمِيزَانَ لِيَقُومَ ٱلنَّاسُ بِٱلۡقِسۡطِۖ وَأَنزَلۡنَا ٱلۡحَدِيدَ فِيهِ بَأۡسٞ شَدِيدٞ وَمَنَٰفِعُ لِلنَّاسِ وَلِيَعۡلَمَ ٱللَّهُ مَن يَنصُرُهُۥ وَرُسُلَهُۥ بِٱلۡغَيۡبِۚ إِنَّ ٱللَّهَ قَوِيٌّ عَزِيزٞ٢٥﴾الحديد Ma’ana:“Hakika mun aiko manzannimmu da hujjoji kuma munsaukar da littafi a tare da su da kuma ma’auni domin mutane su tsayu da adalci”. Suratul Hadid, aya ta: 25. Sai Allah madaukakin sarki ya bayar da labarin cewa shi ne wanda ya aiko manzannin sa kuma shi ne wanda ya saukar da littattafai domin mutane su tsayu da adalci, yanako daga cikin mafigirman adalci Tauhidi, shi ne ma adalcin bakidaya kuma shi ne turakunsa, kuma lalle ita shirka zalunci ce, kamar yadda Allah madaukakin sarki ya ce: ﴿وَإِذۡ قَالَ لُقۡمَٰنُ لِٱبۡنِهِۦ وَهُوَ يَعِظُهُۥ يَٰبُنَيَّ لَا تُشۡرِكۡ بِٱللَّهِۖ إِنَّ ٱلشِّرۡكَ لَظُلۡمٌ عَظِيمٞ١٣﴾Ma’ana:“Lalle shirka zalunci ce mai girma”. Suratu Lukman, aya ta:13. Ita shirka ita ce zalunci mafi girma, tauhidi kuma shi ne adalci mafi girma, to ko dukkan abinda ya kasance mafi girman a wurin kore tauhidi to ko shi ne mafi girman laifi – hardai zuwa inda (Shi Ibnu Kayyim) ya ke cewa: To tunda shirka ta kasance mai kore wannan abinda ake Magana (wato tauhidi) sai ta kasance mafi girman laifuffuka gaba daya, kuma Allah ya haramta aljanna ga dukkan mushiriki (wanda ya yi shirka) kuma ya halatta jininsa da dukiyarsa da iyalansa ga masu tauhidi, kuma ya hallatawa masu tauhidi su ka ma su a matsayin bayi tunda sun ki su tsayu akan bauta masa shi Allah madaukakin sarki, kuma Allah maukakin sarki ya ki ya karbi wani daga wanda ya yi masa shirka, ko ya karbi cetonsa, ko ya amsa masa addu’a alahira, ko ya biya masa wata bukata ta sa alahira, domin shi wanda ya yi shirka ya fi kowa jahiltal Ubangiji, ta yadda ya sanyawa Ubangiji kishiya a cikin halittarsa, wannan kuwa shi ne makurar jahilci – kamar kuma yadda yake shi ne makurar zalunci, dukka in ka duba wanda ya yi shirka bai zalinci Ubangjinshi ba, abin sani kawai kanshi ya zalunta”. Nan maganar Ibnu Kayyim ta kare (Daga Jawabul Kafi.7. Ita shirka tawayace da kuma aibi wanda Ubangiji mai girma da daukaka ya tsarkake kansa daga barin su, to dukkan wanda ya yi wa shirka to hakika ya tabbatarwa da Allah abinda ya tsarkake kansa daga barinsu, wannan ko itace makurar jayayya da Allah madaukakin sarki kuma ita ce makurar girman kai da sabawa Allah.Nau’ukan Shirka: Shirka tanada nau’uka biyu:Nau’i Na Farko: Babbar shirka, wannan ko tana fitar da mutum daga musulunci, kuma tana tabbatar da mai ita a wuta idan har ya mutu akan ta bai tuba ba, ita ce kuwa; Karkatar da wani abu na nau’ukan ibada ga wanin Allah, kamar kiran wanin Allah da kuma neman kusancin wanin Allah ta hanyar yanke-yanke da yin alwashi ga wanin Allah kamar yin su ga kabarurruka da aljanu da shaidanu. Haka nan kuma da jin tsoron matattu ko aljanu ko shaidanu don kada su cutar da shi ko su sanya masa rashin lafiya, haka nan kuma da kaunar wanin Allah akan abinda ba wanda yake da iko akai sai Allah, kamar biyan bukatu da yaye bakinciki irin wanda ake yi a yau akabarurrukan da aka gina kamar kabarurrukan waliyyai da salihan bayi, Allah madaukakin sarki yana cewa:﴿وَيَعۡبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ مَا لَا يَضُرُّهُمۡ وَلَا يَنفَعُهُمۡ وَيَقُولُونَ هَٰٓؤُلَآءِ شُفَعَٰٓؤُنَا عِندَ ٱللَّهِۚ قُلۡ أَتُنَبُِّٔونَ ٱللَّهَ بِمَا لَا يَعۡلَمُ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَلَا فِي ٱلۡأَرۡضِۚ سُبۡحَٰنَهُۥ وَتَعَٰلَىٰ عَمَّا يُشۡرِكُونَ١٨﴾ [يونس:Ma’ana:“Kuma suna bautawa wanin Allah abinda bazai cutar da su ba (idan sunki bauta masa) kuma bazai anfanar da su ba (idan sun bauta masa) kuma suna cewa; Wadan nan sune masu cetommu a wurin Allah”. Suratu Yunus, aya ta:18.Nau’i Na Biyu: Karamar shirka, wannan bata fitar da mutum daga musulunci, saidai tana ragewa mutum tauhidi, kuma hanyace ta zuwa babbar shirka. Ita wannan shirka karamar ta kasu kashi biyu:Kashi Na Farko: Shirkar da take a bayyane, sune kuwa lafuzzan da kuma ayyuka. To su lafuzzan sun hada da rantsuwa da wanin Allah, Ma’aikin Allah ﷺ ya ce: “Duk wanda ya rantse da wanin Allah to hakika ya kafurta ko ya yi shirka”. Bukhari da Muslim suka ruwaito. Da kuma fadin ‘Haka Allah ya so haka kuma ka so’. Ma’aikin Allah ﷺ ya cewa wani mutum da mutumin ya ce: ‘Haka Allah ya so haka kuma ka so’. Sai Ma’aikin Allah ﷺ ya ce: “Yanzu ka sanya ni kishiya ga Allah?!. Ka ce: Hakan Allah ya so, shi kadai”. Da kuma fadin; ‘Da badin Allah ba da kuma wane’. Abinda yafi kyau a fada shine: Haka Allah ya so sannan kuma haka wane ya so’, ko kuma; Da badin Allah ba sannan da kuma wane. Domin ka san tasirin “Sannan” a cikin Magana, domin tana sanya ganin daman bawa ya bi ganin daman Allah madaukakin sarki, kamar yadda Allah ya ce:﴿وَمَا تَشَآءُونَ إِلَّآ أَن يَشَآءَ ٱللَّهُ رَبُّ ٱلۡعَٰلَمِينَ٢٩﴾ [التكوير: 29]Ma’ana:“Kuma dukkan abinda kuke so (ba ya tabbata) saidai in Allah Ubangijin talikai ya so”. Suratut Takwir, aya ta: 29. Da kuma fadin; Ba ni da kowa sai Allah sai kuma kai’. Da fadin; wannan daga albarkatun Allah ne da kuma albarkatunka. Amma ta abinda ya shafi ayyuka kuwa to sune kamar sanya kwabo ko zare domin dauke bala’i ko kuma kauda shi, haka kuma kamar sanya laya domin gudun kambun baka da wanin haka, (to wannan yana zama shirka karama ne) idan ya kudurce a zuciyarsa cewa su wadannan sabubba ne na daukewar bala’i ko kauda shi to anan ne shirka take karama, domin lalle Allah madaukakin sarki bai sanya wadannan su ne sabubba ba, amma idan ya kudurce cewa: Tabbas suna kauda bala’i ko kuma suna dauke bala’in da karankansu to wannan ya zama shirka da take babba, domin ya zama ratayuwa ne da wanin Allah madaukakin sarki. Kashi Na Biyu: Daga cikin shirka da take karama, boyayyiyar shirka, wannanko suna shafar niyyoyi ne da kuma nufi, kamar riya, da fada domin a ji, kamar mutum ya aikata aiki wanda ake neman kusancin Allah da shi kuma ya nemi yabon mutane akan aikin, kamar ya kyautata sallarsa ko ya yi sadaka domin a yabe shi a gode mishi, ko kuma ya yi zikiri ya gyara muryarsa da karatun Alkur’ani domin ya jiyar da mutane su kuma su gode masa su yabeshi, ita riya idan ta hadu da aiki to ta bata aikin, Allah madaukakin sarki yana cewa:﴿قُلْ إِنَّمَا أَنَا بَشَرٌ مِثْلُكُمْ يُوحَى إِلَيَّ أَنَّمَا إِلَهُكُمْ إِلَهٌ وَاحِدٌ فَمَنْ كَانَ يَرْجُو لِقَاءَ رَبِّهِ فَلْيَعْمَلْ عَمَلًا صَالِحًا وَلَا يُشْرِكْ بِعِبَادَةِ رَبِّهِ أَحَدًا١١٠﴾Ma’ana:“To dukkan wanda ya kasance yana fatan haduwa da Ubangijinsa to ya aikata aiki na kwarai kuma kada ya yi shirka a bautawa Ubangijinshi da wani”. Suratul Kahf, aya ta: 110.Kuma Ma’aikin Allah ﷺ ya ce: “Mafi girman abinda nake ji muku tsoro shi ne; Shirka karama, sa sahabbai suka ce: Ya ma’aikin Allah mecece shirka karama? Sai ya ce: Riya”. Ahmad da Dabarani suka ruwaito shi. Yana cikin hakan yin aiki domin kwadayin wani abu na duniya, kamar wanda zai yi aikin Hajji ko ya dinga kiran sallah ko limanci domin kudi, ko kuma ya koyi ilimi na shari’a ko kuma ya yi jihadi domin kudi, Ma’aikin Allah ﷺ ya ce: “Bawan dinare ya yi asara, bawan dirhami ya yi asara (kamar ka ce; bawan Naira ko Dala ko Riyal)….. idan anbashi ya yi shiru, idan kuma ba’a bashi ba ya yi fushi”. Bukhari da Tirmizi suka ruwaito. Imam Ibnu Kayyim –Allah ya yi masa rahama- yana cewa: “Amma ita shirka a nufi da kuma niyyoyi (jam’in niyyah)to wannan kogine da bashi da gaba, kadan ne wanda zai tsira daga ciki, to dukkan wanda ya nufaci wanin Allah da aikin shi ya yi niyyar wani abu da ba neman kusanci ga Allah ba da neman sakamakon daga wurin Allah ba to hakika ya yi shirka a niyyarsa da kuma ikonsa, shi abinda yake Ikhlasi (wato yi domin Allah) shi ne ya tsarkake ayyukansa da maganganun sa da ikonsa da kuma niyyarsa domin Allah, to wannan shi ne tsantsar bin tafarkin Annabi Ibrahim wanda Allah ya umarci bayinsa baki yada da bi, kuma baya karbar aiki daga wurin kowa in bai bi wannan tafarkin ba, wannan kuma shine tsantsar musulunci, kamar yadda Allah madaukakin sarki ya ce:﴿وَمَنْ يَبْتَغِ غَيْرَ الْإِسْلَامِ دِينًا فَلَنْ يُقْبَلَ مِنْهُ وَهُوَ فِي الْآخِرَةِ مِنَ الْخَاسِرِينَ٨٥﴾Ma’ana:“Dukkan wanda ya bi abinda ba musulunci a matsayin addini to ba za’a taba karba daga wurinsa ba, kuma shi a lahira yana cikin asararru”. Suratu Ali Imran, aya ta: 85. Kuma wannan shi ne addinin Annabi Ibrahim u, hanyar da duk wanda ya kauda kai daga barinta to shi wanda ya wawantar da kanshi ne”. Aljawabul Kafi, shafi na:115.Daga bayanan da suka gabata ya bayyana cewa akwai banbance banbance tsakanin shirka babba da kuma shirka karama, su ne kuma kamar haka:1. Babbar shirka tana fitarwa daga musulunci, karamar shirka kuma bata fitarwa daga musulunci.2. Babbar shirka tana dawwamar da mai ita a wuta, karamar shirka kuma ba ta dawwamar da mai ita a wuta in ya shiga.3. Babbar shirka tana bata ayyuka baki daya, amma karamar shirka bata bata ayyuka baki daya, saidai kawai ita riya da ma aikin da aka yi shi domin duniya wannan aikin kawai shine ya ke baci.4. Babbar shirka tana halattar da jinin mutum da kuma dukiyarsa, amma shirka karama bata halatta su.**** **** **** Fasali Na Uku:Kafirci Ta’afrifin Sa Da Kuma Nau’ukansa.1. Ta’arifinsa: Shi kafirci a gungarin bakin larabci shine: Lillibewa da kuma suturcewa. Amma kafirce a shar’ance shine: Kishiyar Imani, domin kafirci shine: Kin yin Imani da Allah da manzannin Allah, daidai ne shin hakan ya hada da karyatawa ko bai hada da karyatawa ba, shin shakkune ko kokwanto ko ma kau-da-kai, ko kuma hassada ko girman kai ko bin san zuciya da take hana bin sakon Allah, duk da cewa mai karyatawa kafircinsa ya fi girma, haka kuma mai musu mai kuma karyatawa domin kawai hasada tare da samun yakini akan gaskiyar manzannin.2. Nau’ukansa: Kafirci yana da nau’uka biyu:Nau’i Na Farko: Kafirci babba, wanda yake fitarwa daga addinin musulunci, shi kuma ya kasu kashi biyar: Kashi Na Farko: Kafircin Karyatawa, dalili akan haka fadin Allah madaukakin sarki:﴿وَمَنْ أَظْلَمُ مِمَّنِ افْتَرَى عَلَى اللَّهِ كَذِبًا أَوْ كَذَّبَ بِالْحَقِّ لَمَّا جَاءَهُ أَلَيْسَ فِي جَهَنَّمَ مَثْوًى لِلْكَافِرِينَ٦٨﴾Ma’ana:“Babu mai girman zalinci kamar wanda ya kirkiri karya ya jinginawa Allah ko kuma ya karyata gaskiya alokacin da ta zo masa. Ashe jahannama bata zamo makoma ga kafiraiba”. Suratul Ankabut, aya ta:68.Kashi Na Biyu: Kafircin Kinyarda da kuma girmankai tare da gasgatawa, dalili akan wannan fadin Allah madaukakin sarki:﴿وَإِذْ قُلْنَا لِلْمَلَائِكَةِ اسْجُدُوا لِآدَمَ فَسَجَدُوا إِلَّا إِبْلِيسَ أَبَى وَاسْتَكْبَرَ وَكَانَ مِنَ الْكَافِرِينَ٣٤﴾Ma’ana:“Kuma alokacin da muka ce da mala’iku; Ku yi sujuda ga Adam, sai suka yi sujudar saidai iblisu ya ki kuma ya yi girman kai kuma ya kasance cikin kafirai”. Suratul Bakara, aya ta: 34.Kashi Na Uku: Shi ne Kafircin Zato, dalili kuwa shi ne dafin Allah madaukakin sarki:﴿وَدَخَلَ جَنَّتَهُ وَهُوَ ظَالِمٌ لِنَفْسِهِ قَالَ مَا أَظُنُّ أَنْ تَبِيدَ هَذِهِ أَبَدًا٣٥ وَمَا أَظُنُّ السَّاعَةَ قَائِمَةً وَلَئِنْ رُدِدْتُ إِلَى رَبِّي لَأَجِدَنَّ خَيْرًا مِنْهَا مُنْقَلَبًا٣٦ قَالَ لَهُ صَاحِبُهُ وَهُوَ يُحَاوِرُهُ أَكَفَرْتَ بِالَّذِي خَلَقَكَ مِنْ تُرَابٍ ثُمَّ مِنْ نُطْفَةٍ ثُمَّ سَوَّاكَ رَجُلًا٣٧ لَكِنَّا هُوَ اللَّهُ رَبِّي وَلَا أُشْرِكُ بِرَبِّي أَحَدًا٣٨﴾Ma’ana:“Kuma ya shiga gonarsa alhali yana mai zalintar kansa, ya ce; ba na zaton wannan (gonar) zata kare har abada. Kuma ba na zaton alkiyama zata ta shi, kuma ma har idan aka maida ni ga Ubangijina (idan ma da gaskene) to tabbas zan sami abinda ya fita a makoma. Sai abokinsa ya ce masa alokacin yana tattaunawa da shi; Yanzu zaka kafircewa wanda ya halicceka daga kasa sannan kuma daga dugon maniyyi sannan ya daidaita kaka zama mutum. Saidai ni Shi Allah shi ne Ubangijina kuma bazan taba yi wa Ubangijina shirka da wani ba”. Suratul Kahf, aya ta: 35-38.Kashi Na Hudu: Kafirci Na Kaudakai, dalilin wannan shine fadin Allah madaukakin sarki:﴿مَا خَلَقْنَا السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ وَمَا بَيْنَهُمَا إِلَّا بِالْحَقِّ وَأَجَلٍ مُسَمًّى وَالَّذِينَ كَفَرُوا عَمَّا أُنْذِرُوا مُعْرِضُونَ٣﴾Ma’ana:“Kuma wadanda suka kafirce dangane da abinda aka yi musu gargadi masu kaudakai ne”. Suratul Ahkaf, aya ta:3Kashi Na Biyar: Kafirci Na Munafunci, dalili kuwa shi ne fadin Allah madaukakin sarki:﴿ذَلِكَ بِأَنَّهُمْ آمَنُوا ثُمَّ كَفَرُوا فَطُبِعَ عَلَى قُلُوبِهِمْ فَهُمْ لَا يَفْقَهُونَ٣﴾Ma’ana:“Wancan (abinda ya same su) saboda cewa lalle su sun yi Imani sannan suka kafirce sai aka rufe zukatansu to su kan ba za su taba fahimta ba”. Suratul Munafikun aya ta:3.Nau’i Na Biyu: Kafirci Karami, wannan ba ya fitarwa daga musulunci, shi ne kuwa kafirci na ayyuka, wadansu zunubaine da ya zo acikin Alkur’ani da Hadisi da ambatonsu da sunan kafirci, amma ba ta kai ga matsayin kafircin da yake babba ba, kamar butulcewa ni’ima da Allah madaukakin sarki ya ce:﴿وَضَرَبَ اللَّهُ مَثَلًا قَرْيَةً كَانَتْ آمِنَةً مُطْمَئِنَّةً يَأْتِيهَا رِزْقُهَا رَغَدًا مِنْ كُلِّ مَكَانٍ فَكَفَرَتْ بِأَنْعُمِ اللَّهِ فَأَذَاقَهَا اللَّهُ لِبَاسَ الْجُوعِ وَالْخَوْفِ بِمَا كَانُوا يَصْنَعُونَ١١٢﴾Ma’ana:“Kuma Allah ya buga misalin wata alkarya wacce ta kasance amintacciya kuma natsattsiya arzikinta yana zuwa mata a yalwace daga ko’ina, sai ta kafircewa ni’imomin Allah”. Suratun Nahl, aya ta:112. Hakadai misalin yake na musulmi ya yaki musulmi a hadisin da Ma’aikin Allah ﷺ ya ce: “Zagin musulmi fasikanci ne, kuma yakarsa kafirci ne”. Bukhari da Muslim suka ruwaito. Da kuma fadin Ma’ikin Allah ﷺ: “Kada ku koma a bayana kuna kafirai, sashinku yana kasha sashi”. Bukhari da Muslim suka ruwaito. Kuma yana ciki yin rantsuwa da wanin Allah, Ma’aikin Allah ﷺ ya ce: “Duk wanda ya rantse da wanin Allah ya kafirta ko kuma ya yi shirka”. Bukhari da Muslim suka ruwaito. Kuma Allah madaukakin sarki ya sanya wanda ya aikata “Kabira” babban laifi cewar muminine, Allah madaukakin sarki yana cewa:﴿يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا كُتِبَ عَلَيْكُمُ الْقِصَاصُ فِي الْقَتْلَى الْحُرُّ بِالْحُرِّ وَالْعَبْدُ بِالْعَبْدِ وَالْأُنْثَى بِالْأُنْثَى فَمَنْ عُفِيَ لَهُ مِنْ أَخِيهِ شَيْءٌ فَاتِّبَاعٌ بِالْمَعْرُوفِ وَأَدَاءٌ إِلَيْهِ بِإِحْسَانٍ ذَلِكَ تَخْفِيفٌ مِنْ رَبِّكُمْ وَرَحْمَةٌ فَمَنِ اعْتَدَى بَعْدَ ذَلِكَ فَلَهُ عَذَابٌ أَلِيمٌ١٧٨﴾Ma’ana:“Ya ku wadanda suka yi Imani!, an wajabta muku yin kisasi (ramuwa) a wadanda aka kashe”. Suratul Bakarah, aya ta: 178. Allah madaukakin sarki bai fitar da wanda ya yi kisa daga cikin masu imani ba, ya ma sanya shi dan’uwa ga ‘yan’uwan wadanda za’a yi wa ramuwa, sai Allah madaukakin sarki ya ce:﴿ فَمَنْ عُفِيَ لَهُ مِنْ أَخِيهِ شَيْءٌ فَاتِّبَاعٌ بِالْمَعْرُوفِ وَأَدَاءٌ إِلَيْهِ بِإِحْسَانٍ ﴾Ma’ana:“To dukkan wanda aka yafewa wani abu na abinda ya shafi dan’uwansa to (ya) bi da kyautatawa da kuma bayarwa ga reshi da ihsani (kyautatawa)”. Suratul Bakarah, aya ta: 178. Abinda ake nufi ‘yan’uwantaka ta addini ba tare da wani kokwanto ba. Allah madaukakin sarki yana cewa:Ma’ana:“Kuma idan wadansu jama’u biyu daga cikin muminai suna yaki to ku sulhunta tsakaninsu”. Suratul Hujurat, aya ta:9. Har zuwa inda Allah madaukakin sarki yake cewa:﴿وَإِنْ طَائِفَتَانِ مِنَ الْمُؤْمِنِينَ اقْتَتَلُوا فَأَصْلِحُوا بَيْنَهُمَا فَإِنْ بَغَتْ إِحْدَاهُمَا عَلَى الْأُخْرَى فَقَاتِلُوا الَّتِي تَبْغِي حَتَّى تَفِيءَ إِلَى أَمْرِ اللَّهِ فَإِنْ فَاءَتْ فَأَصْلِحُوا بَيْنَهُمَا بِالْعَدْلِ وَأَقْسِطُوا إِنَّ اللَّهَ يُحِبُّ الْمُقْسِطِينَ٩﴾Ma’ana:“Abin sani kawai muminai ‘yan’uwan juna ne, to ku sulhunta tsakanin ‘yan’uwanku”. Suratul Hujurat, aya ta:10. Nan maganar ta kare daga littafin Sharhin Dahawiyyah, atakaice.A takaice banbance-banbancen da ke tsakanin kafirci babba da kuma kafirci karami:1. Lalle kafirci babba yana fitar da mutum daga musulunci kuma yana bata ayyuka, shi kuma kafirci karami ba ya fitarwa daga musulunci kuma ba ya bata ayyuka, saidai yana rage rage ayyukai gwargwadon shi karamin kafincin, kuma yana sa mai shi ya dandani narkon azaba.2. Lalle babban kafirci yana tabbatar da mai shi a wuta, amma shi karamin kafirci ba ya tabbatar da mai shi a wutar idan har ya shigeta, kuma (In Allah ya ga dama) yana yafewa maishi ta yadda ba ma zai shiga wutarba.3. Lalle kafirci babba yana halatta jinni da kuma dukiya, shi kuwa kafirci karami ba ya halatta jinni kuma ba ya halatta dukiya.4. Lalle kafirci babba yana wajabta tsantsar kiyayya tsakanin mai shi da kuma muminai, domin ba ya halatta ga muminai su so shi ko da ya kasance kuddakut su ke. Amma kafircin da yake karami ba ya hana jibinta kai tsaye, domin mai irin wannan aiki za’a so shi kuma za’a jibinceshi agwargwadon abinda yake da shin a imani, kuma za’a ki shi ayi adawa da shi a gwargwadon abinda yake da shi na laifuffuka.**** ***** **** Fasali Na Hudu: Munafunci Ta’arifinsa Da Kuma Nau’ukansaTa’arifinsa: Agundarin bakin larabci an ciro kalmarne daga Nufaka’u, wato daya daga cikin mafitar yanyawa daga raminta, ta yadda idan aka nemeta ta wata mafitar sai ta fita ta daya mafitar.Amma ashar’ance idan aka ce munafunci to shine: Bayyanar da musulunci da kuma boye kafirci da sharri. Ankira mai wannan haline da wannan suna na “Munafunci” domin yana shiga musulunci ta wata kofa ya kuma fice ta wata kofar daban, akan hakane Allah madaukakin sarki ya fadakar a inda ya ce: ﴿الْمُنَافِقُونَ وَالْمُنَافِقَاتُ بَعْضُهُمْ مِنْ بَعْضٍ يَأْمُرُونَ بِالْمُنْكَرِ وَيَنْهَوْنَ عَنِ الْمَعْرُوفِ وَيَقْبِضُونَ أَيْدِيَهُمْ نَسُوا اللَّهَ فَنَسِيَهُمْ إِنَّ الْمُنَافِقِينَ هُمُ الْفَاسِقُونَ٦٧﴾Ma’ana:“Lalle munafukai sune wadanda suke fasikai”. Suratut Taubah, aya ta:67.Wato wadanda suka fita daga shari’ah, kuma Allah madaukakin sarki ya sanya munafukai wadanda suka fi kafirai sharri, sai Allah ya ce:﴿إِنَّ الْمُنَافِقِينَ فِي الدَّرْكِ الْأَسْفَلِ مِنَ النَّارِ وَلَنْ تَجِدَ لَهُمْ نَصِيرًا١٤٥﴾Ma’ana:“Lalle munafukai suna can karkashin wuta”. Suratun Nisa’i, aya ta:145. Kuma Allah madaukakin sarki ya ce:﴿إِنَّ الْمُنَافِقِينَ يُخَادِعُونَ اللَّهَ وَهُوَ خَادِعُهُمْ وَإِذَا قَامُوا إِلَى الصَّلَاةِ قَامُوا كُسَالَى يُرَاءُونَ النَّاسَ وَلَا يَذْكُرُونَ اللَّهَ إِلَّا قَلِيلًا١٤٢﴾Ma’ana:“Lalle munafukai suna yaudarar Allah alhali shi yake yaudararsu”. Suratun Nisa’i, aya ta: 142. Da kuma fadin Allah madaukakin sarki:﴿يُخَادِعُونَ اللَّهَ وَالَّذِينَ آمَنُوا وَمَا يَخْدَعُونَ إِلَّا أَنْفُسَهُمْ وَمَا يَشْعُرُونَ٩ فِي قُلُوبِهِمْ مَرَضٌ فَزَادَهُمُ اللَّهُ مَرَضًا وَلَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ بِمَا كَانُوا يَكْذِبُونَ١٠﴾Ma’ana:“Suna yaudarar Allah da wadanda suka yi imani kuma ba kowa suke yaudaraba sai kawunan su kuma ba su sani ba. A cikin zukatansu akwai cuta sai Allah ya karamusu wata cuta, kuma suna da azaba mai radadi saboda abinda suka kasance suna karyatawa”. Suratul Bakarah, aya ta:9-10. Nau’ukan Munafunci: Munafunci yana da nau’uka guda biyu:Nau’i Na Farko: Munafuncin Zuci (na akida), wannan ko shi ne babban munafunci wanda mai shi yake bayyana musulunci ya kuma boye kafirci, wannan nau’i yana fitar da mai shi daga musulunci bakidaya, kuma mai shi ya kasance a can kasan wuta – kuma tabbas Allah madaukakin sarki ya wasafta masu wannan munafunci da dukkanin siffofi na sharri- na kafirci da rashin imani da izgili da addini da kuma masu addinin, da yi musu dariya, da kuma yadda suke karkata gaba daya ga makiya addini domin tarayya da su wurin kin musulunci, kuma wadannan suna nan a kowanne zamani, musammamma alokacin da musulunci yake kara karfi ta yadda ba za su iya fito-na-fito da shi ba a bayyane, to su sai su bayyana cewar sun shiga musuluncin domin su kulla masa makirci su kuma kullawa Musulmai makirci a boye, kuma domin su rayu tare da Musulmai su kuma baiwa jininsu da dukiyarsu kariya. Sai munafuki ya bayyana imaninsa da Allah da kuma mala’ikunsa da littattafansa da kuma manzanninsa da lanar lahira, wanda yake kuma a boye ya tsame kansa daga hakan bakidaya ya kuma karyata su duka, kwatakwata bai yi imani da Allah ba kuma bai yi imani da cewa Allah ya yi Magana da ya saukar ga wani mutum da ya sanya shi manzo ba, da yake shiryar da mutane da izinin sa shi Allah ba, kuma ya na tsoratar da su bala’iba da kuma tsoratar da su ukuba. Hakika Allah ya tona asirin wadannan munafukai, ya tona asirinsu a cikin Alkur’ani mai girma, ya kuma bayyanawa bayinsa al’amuran munafukai domin su kasance sun kaucewa al’amuran da kuma masu al’amuran (wato munafukai), kuma ya lissafa bangarorin al’umma guda uku a farkon suratul Bakarah: Muminai, da kafirai da kuma munafukai. Dangane da muminai ya ambaci ayoyi guda hudu, kafirai kuma ayoyi biyu, amma dangane da munafukai ayoyi guda goma-sha uku ya ambata, saboda yawansu da kuma yadda ake jarraba muminai da su da tsananin ba’insu ga musulunci da kuma Musulmai, domin bala’in da musulunci ya samu kanshi a ciki ta sanadiyyarsu tana da tsanani sosai, domin su suna jingina kansu da shi da kuma cewar wai suna taimakonsa, kuma suna jibintarshi, alhali kuma su ne makiyansa na hakika, suna bayyanar da kiyayyarsu akoyaushe, shi jahili yana zaton ai hakan ilimine da kuma kawo gyara, alhali kuwa wannan shine makurar jahilci da kuma barna. Wannan munafuncin yanada nau’uka shida:1. Karyata Manzan Allahr.2. Karyata wani sashi na abinda Manzon ﷺ ya zo da shi.3. Kin Manzonr.4. Kin wani sashi na abinda Manzon ﷺ ya zo da shi.5. Boye son addinin da Manzon ﷺ ya zo da shi ace kullun kasa yake yi.6. Kyamar taimakawa addinin da Manzon ﷺ ya zo da shi.Nau’i Na Biyu: Munafunci Na Aiki, shi ne aikata wani aiki daga cikin ayyukan munafukai tare da yin imani a zuciya, to wannan ba ya fitarwa daga musulunci, saidai shima hanyace ta fita daga musuluncin. To mai wannan zai kasance yana da imani kuma yana da munafunci, idan hakan ya yawaita to mai shi zai kasance tsantsar munafiki, dalili akan haka shi ne fadin Ma’aikin Allahr:“Abubuwa hudu duk wanda ya kasance da su to ya kasance tsantsar munafuki, wandako ya kasance yana da daya daga cikin su to ya kasance yana da kaso guda na munafunci har sai ya barta. Idan an amince masa ya yi ha’inci, idan kuma ya bada labari ya yi karya, idan kuma aka yi alkawari da shi ya warware, idan kuma aka yi rikici da shi ya yi zalinci”. Bukhari da Muslim ne suka ruwaito. To dukkan wanda wadannan halaye guda hudu suka taru awajansa to hakika ya tara sharri, kuma siffofin munafukai sun hadu akan shi , wanda ko ya kasance daya yake da ita to ya kasance yana da halayya guda daya daga cikin halayar munafunci, domin yadda al’amarin yake dabi’u na alheri da dabi’u na sharri sukan taru ga bawa, da dabi’un imani da kuma dabi’un kafirci da munafunci, sai ya cancanci lada (ta dabi’un alheri) ya kuma cancanci ukuba (ta dabi’un sharri) gwargwadon yadda ya tsayu da abubun da suke janyo hakan. Daga cikin haka akwai kasalar kin yin sallar a cikin jam’i a masallaci, to wannan yana daga cikin siffar munafukai, munafunci sharri ne kuma mai matukar hadari, sahabban Ma’aikin Allah ﷺ sun kasance suna tsoron fadawa cikinsa, Ibnu Mulaika ya ce: Na riski mutum talatin daga cikin Sahabban Manzon Allah ﷺ kowannensu yana jiwa kansa tsoron munafunci. Bambance-bambancen da ke tsakanin munafunci babba da kuma munafunci karami:1. Lalle shi munafunci babba yana fitarwa daga musulunci, amma munafunci karami ba ya fitarwa daga musulunci.2. Lalle shi munafunci babba shene zuciya ta sabawa zahiri a imani, amma munafunci karami shi ne zahiri ya sabawa badinin mutum a abinda ya shafi ayyuka banda itikadi.3. Lalle shi munafunci babba baya kasancewa daga mumini, amma munafunci karami takan yiwu ya kasance daga mumini.4. Lalle munafunci babba a mafiyawancin lokaci meshi baya tuba, ko ma da ya tuban to tabbas malamai sun karawa juna sani kan karbar tubanshi a gaban hukuma (ta musulunci). Sabanin karamin munafunci, domin meshi yakan tuba zuwa ga Allah kuma Allah ya karbi tubansa, Shehul Islam Ibnu Taimiyah yana cewa: Sauda yawa wani kaso daga cikin Kason munafunci yakan bijirowa mumini sannan kuma sai Allah ya karbi tubansa, kuma a wani lokaci wani abu yakan gangarowa zuciyarsa (mumini) abinda yake haifar da munafunci sai Allah ya kore masa shi, shi mumini ana jarrabarshi da wasawasi na shaidan da kuma wasawasi na kafirci wadanda zuciyarsa za ta yi masa kunci akan haka, Sahabban ma’aikin Allah ﷺ sun ce: Ya Ma’aikin Allah, wallahi dayammu ya kan ji azuciyarsa irin abinda wallahi ya fado daga sama zuwa kasa ya fi masa sauki akan ya fadi wannan abin, sai ma’aikin Allah ﷺ ya ce: “Wannan shine hakikanin Imani”. Muslim da Ahmad suka ruwaito. A wata ruwayar kuma: “Abin yana da matukar girma ace ya fada, sai ma’aikin Allah ﷺ ya ce: “Dukkan godiya ta tabbata ga Allah wanda ya mayar da makircinsa ga wasawasi”. Abudawud ne da Ahmad suka ruwaito. Ma’ana: Samuwar wannan wasawasi tare da irin wannan kyama mai girman gaske da kuma tunkude shi da aka yi daga barin zuciya, yana cikin hakikanin imani”. Ya kare.Amma masu babban munafunci Allah madaukakin sarki ya fada dangane da su:﴿صُمٌّ بُكْمٌ عُمْيٌ فَهُمْ لَا يَرْجِعُونَ١٨﴾Ma’ana:“(Su) Kuramene kuma bebayene kuma makafine su kan basa taba dawowa”. Suratul Bakarah, aya ta:18. Ma’ana su dawo su yi musulunci a zuciyarsu. Kuma ya fada dangane da su:﴿أَوَلَا يَرَوْنَ أَنَّهُمْ يُفْتَنُونَ فِي كُلِّ عَامٍ مَرَّةً أَوْ مَرَّتَيْنِ ثُمَّ لَا يَتُوبُونَ وَلَا هُمْ يَذَّكَّرُونَ١٢٦﴾Ma’ana:“Shin ba sa gani ne cewar lalle su ana jarrabarsu a kowacce shekara sau daya ko sau biyu, sannan ba sa tuba kuma su dun ba sa daukar wa’azantarwa”. Suratut Taubah, aya ta: 126. Shehul Islam Ibnu Taimiyah ya ce: Hakika malamai sun karawa juna sani akan abinda ya shafi karbar tubansu a zahiri, domin kasancewar hakan ba’a iya ganewa, domin su ai akoyaushe musulunci suke bayyanawa”. Majmu’ul Fatawa, Juzu’i na 28, shafi na 434-435. **** **** **** Fasali Na Biyar:Bayani Akan Hakikanin: Maguzanci – Fasikanci – Bata – Riddah: Raberabenta, Hukunce-hukuncenta.1. Maguzanci (Jahiliyyah): shi ne rayuwar da larabawa suka kasance a cikinta kafin zuwan musulunci, na abinda ya shafi jahiltar Allah da manzanninsa da hukunce-hukuncen addini, da alfahari da dangantaka da girmankai da takama da sauransu. Wato an jinginasu ga jahilci wanda yake kishiya ne ga ilimi ko rashin bin ilimin. Shehul Islam Ibnu Taimiya yana cewa: To dukkan wanda bai san gaskiya ba to jahiline na tsakatsaki, idan kuwa ya kudurce sabanin gaskiya to wannan ya tara jahilci wani kan wani, to idan ka gane haka su mutane kafin aiko Manzan Allah ﷺ su kasance a jahiliyyah (maguzanci) wadanda aka jingina su ga jahilci, domin abinda suka kasance a kai na zantattuka da ayyuka to abinda ya haifar musu da shi shine jahilcin, to wanda yake aika hakan ya zama jahili. To haka yake dukkan wanda yake sabawa abinda manzanni suka zo da shi, yahudanci yake bi ko Nasaranci to shi bamaguje ne, to a wannan lokacin ne ake da gamammiyar jahiliyyah, to saidai bayan aiko Manzan Allah ﷺ jahiliyyah tana kasancewa ne a wasu birane banda wasu, kamar yadda suke a kasashen kafirai, kuma ta kan kasance ga wani mutum ban da kuma wani, kamar mutum kafin ya musulunta ya kasance ne a jahiliyyah koda yana garuruwan Musulmai, to ammadai alokaci kacokan babu jaliyyah kuma tun bayan aiko da manzan Allah Annabi Muhammad ﷺ domin yadda al’amarin yake wata tawaga ba zata gushe ba daga al’ummarsa suna tsaye akan gaskiya har zuwa ranar tashin alkiya. Amma takaitacciyar jahiliyyah ta kan kasance a wasu kasashen Musulmai a daidaikun mutane masu tarin yawa, kamar yadda ma’aikin Allah ﷺ ya ce: “Abubuwa hudu suna cikin al’ummata na al’amuran jahiliyyah ne”. Muslim da Ibnu Majah suka ruwaito. Kuma ya fadawa Abuzarr, ya ce: “Lalle kai mutum ne da kake da jahiliyyah”. Bukhari da Muslimne suka ruwaito shi, dadai makamantan haka. Nan maganar Ibnu Taimiyah ta tsaya. Atakaicedai: Ita jahiliyyah an jinginata ne ga jahilci shine kuwa rashin ilimi, kuma ita jahiliyyah ta ka su kasha biyu:1. Gamammiyar Jahiliyyah, wannan itace ta kasance kafin aiko manzan Allah ﷺ kuma wannan ta kare.2. Kebantacciyar Jahiliyyah, wannan tana kasancewa ne ga wasu kasashe da kuma wasu garuruwa da kuma daidaikun wasu mutane, wannanko ba zata gushe ba tana nan. Da wannan ne kuskuren wadanda suke game jahiliyyah a wannan zamani suke cewa: ‘Jahiliyyar wadannan shekarun da makamantansa’. Abinda yake daidai da za’a ce: Jahiliyyar wasu a wadannan shekarun, ko mafi rinjayan wadannan shekarun, amma a game to wannan bai yi ba, kuma bai halatta a fada ba, domin da aiko Ma’aikin Allah ﷺ to gamammiyar jahiliyyah ta kau.2. Fasikanci. Shi fasikanci a gundarin bakin larabci shine; Fita. Amma abinda ake nufi da shi a shar’ance Shi ne : Ficewa daga barin yiwa Allah biyayya (wato kin bin Allah), wannan ko ya shafi gamammiyar ficewa, wato sai acewa kafiri fasiki, da kuma takaitacciyar ficewa wato sai acewa mumini mai aikata babban laifi fasiki. Shi fasikanci ya kasu kashi biyu:Kashi Na Farko: Fasikancin da yake fitar da mutum daga musulunci, wannan ko shine kafirci, sai ka ji ankira fasiki da kafiri, hakika Allah madaukakin sarki ya ambaci iblis sai yac e:﴿وَإِذْ قُلْنَا لِلْمَلَائِكَةِ اسْجُدُوا لِآدَمَ فَسَجَدُوا إِلَّا إِبْلِيسَ كَانَ مِنَ الْجِنِّ فَفَسَقَ عَنْ أَمْرِ رَبِّهِ أَفَتَتَّخِذُونَهُ وَذُرِّيَّتَهُ أَوْلِيَاءَ مِنْ دُونِي وَهُمْ لَكُمْ عَدُوٌّ بِئْسَ لِلظَّالِمِينَ بَدَلًا٥٠﴾Ma’ana:“To sai ya fita (ya ki bin) umarnin Ubangijinsa”. Suratul Kahf, aya ta: 50. Wannan fasikancin na shi ya kasance kafirce ne, kuma Allah madaukakin sarki yana cewa:﴿وَأَمَّا الَّذِينَ فَسَقُوا فَمَأْوَاهُمُ النَّارُ كُلَّمَا أَرَادُوا أَنْ يَخْرُجُوا مِنْهَا أُعِيدُوا فِيهَا وَقِيلَ لَهُمْ ذُوقُوا عَذَابَ النَّارِ الَّذِي كُنْتُمْ بِهِ تُكَذِّبُونَ٢٠﴾Ma’ana:“Kuma wadannan da suka yi fasikanci to makomarsu ita ce wuta”. Suratus Sajadah, aya ta: 20. Abinda yake nufi kafirai, abinda yake nuni akan hakan kuwa shine fadin Allah madaukakin sarki:﴿وَأَمَّا الَّذِينَ فَسَقُوا فَمَأْوَاهُمُ النَّارُ كُلَّمَا أَرَادُوا أَنْ يَخْرُجُوا مِنْهَا أُعِيدُوا فِيهَا وَقِيلَ لَهُمْ ذُوقُوا عَذَابَ النَّارِ الَّذِي كُنْتُمْ بِهِ تُكَذِّبُونَ٢٠﴾Ma’ana:“Aduk lokacin da suka yi nufin su fita daga cikinta (wutar) sai amayar da su cikinta, kuma ace da su; Ku dandani azabar wuta wacce kuka kasance kuna karya ta ta”. Suratus Sajadah, aya ta: 20. Kuma ana kiran mailaifi daga cikin al’ummar Musulmai da fasiki, saidai kuma bai fitar da shi daga musulunci ba, Allah madaukakin sarki yana cewa:﴿أَوْ كَظُلُمَاتٍ فِي بَحْرٍ لُجِّيٍّ يَغْشَاهُ مَوْجٌ مِنْ فَوْقِهِ مَوْجٌ مِنْ فَوْقِهِ سَحَابٌ ظُلُمَاتٌ بَعْضُهَا فَوْقَ بَعْضٍ إِذَا أَخْرَجَ يَدَهُ لَمْ يَكَدْ يَرَاهَا وَمَنْ لَمْ يَجْعَلِ اللَّهُ لَهُ نُورًا فَمَا لَهُ مِنْ نُورٍ٤٠﴾Ma’ana:“Kuma dukkanin wadanda suke jifan ‘ya’ya mata (da zina) sannan kuma basu kawo shaidu hudu mazaba to ku yi musu bulala tamanin, kuma kada ku sake karbar shaidarsu har abada, kuma wadannan sune fasikai”. Suratun Nur, aya ta:4. Kuma Allah madaukakin sarki yana cewa:﴿الْحَجُّ أَشْهُرٌ مَعْلُومَاتٌ فَمَنْ فَرَضَ فِيهِنَّ الْحَجَّ فَلَا رَفَثَ وَلَا فُسُوقَ وَلَا جِدَالَ فِي الْحَجِّ وَمَا تَفْعَلُوا مِنْ خَيْرٍ يَعْلَمْهُ اللَّهُ وَتَزَوَّدُوا فَإِنَّ خَيْرَ الزَّادِ التَّقْوَى وَاتَّقُونِ يَا أُولِي الْأَلْبَابِ١٩٧﴾Ma’ana:“To dukkan wanda ya dauki damarar aikin hajji a cikin su to babu batsa babu kuma fasikanci kuma babu jayayya a hajji”. Suratul Bakarah, aya ta:197. Malamai suke a tafsirin fasikanci a wannan ayar da cewa; Shi ne laifuffuka.3. Bata: Idan akace bata shine kaucewa hanyar da take daidai, kenan bata kishiya ne na shiriya, Allah madaukakin sarki ya ce:﴿مَنِ اهْتَدَى فَإِنَّمَا يَهْتَدِي لِنَفْسِهِ وَمَنْ ضَلَّ فَإِنَّمَا يَضِلُّ عَلَيْهَا وَلَا تَزِرُ وَازِرَةٌ وِزْرَ أُخْرَى وَمَا كُنَّا مُعَذِّبِينَ حَتَّى نَبْعَثَ رَسُولًا١٥﴾Ma’ana:“Dukkan wanda ya shiryu to abin sani kawai yana shiryuwane ga karankansa, wanda duk kuma ya bata to abin sani kawai yana bata akansa”. Suratul Isra’i, aya ta: 15.Ita bata tana zuwa da ma’anoni da dama:1. Wani lokacin yana zuwa da ma’anar kafirci, Allah madaukakin sarki ya ce: ﴿يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا آمِنُوا بِاللَّهِ وَرَسُولِهِ وَالْكِتَابِ الَّذِي نَزَّلَ عَلَى رَسُولِهِ وَالْكِتَابِ الَّذِي أَنْزَلَ مِنْ قَبْلُ وَمَنْ يَكْفُرْ بِاللَّهِ وَمَلَائِكَتِهِ وَكُتُبِهِ وَرُسُلِهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ فَقَدْ ضَلَّ ضَلَالًا بَعِيدًا١٣٦﴾Ma’ana:“Kuma dukkan wanda ya kafircewa Allah da mala’ikunsa da littattafansa da manzanninsa da ranar karshe to hakika wannan ya bata bata mai nisan gaske”. Suratun Nisa’i, aya ta: 136.2. Wani lokacin kuma yana zuwa da ma’anar shirka, kamar yadda Allah madaukaukin sarki ya ce:﴿إِنَّ اللَّهَ لَا يَغْفِرُ أَنْ يُشْرَكَ بِهِ وَيَغْفِرُ مَا دُونَ ذَلِكَ لِمَنْ يَشَاءُ وَمَنْ يُشْرِكْ بِاللَّهِ فَقَدْ ضَلَّ ضَلَالًا بَعِيدًا١١٦﴾Ma’ana:“Kuma dukkanin wanda ya yi wa Allah shirka to hakika ya bata bata kuma mai nisa”. Suratun Nisa’i, aya ta:116.3. Wani lokaci kuma bata tana zuwa da ma’ana sabawa Allah wacce batakai kafirci ba, kamar yadda ake cewa; Batattun kungiyoyi’. Wato wadanda suka sabawa daidai.4. Wani lokacin bata tana zuwa da ma’anar kuskure, daga cikin haka ne maganar Annabi Musa u take:﴿قَالَ فَعَلْتُهَا إِذًا وَأَنَا مِنَ الضَّالِّينَ٢٠﴾Ma’ana: “Ya ce; Na aikata ta ne alokacin ina mai rashin sani”. Suratus Shu’ara’i, aya ta:20.5. Wani lokacin kuma tana zuwa da ma’anar Mantuwa, kamar yadda Allah madaukakin sarki ya ce:﴿يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِذَا تَدَايَنْتُمْ بِدَيْنٍ إِلَى أَجَلٍ مُسَمًّى فَاكْتُبُوهُ وَلْيَكْتُبْ بَيْنَكُمْ كَاتِبٌ بِالْعَدْلِ وَلَا يَأْبَ كَاتِبٌ أَنْ يَكْتُبَ كَمَا عَلَّمَهُ اللَّهُ فَلْيَكْتُبْ وَلْيُمْلِلِ الَّذِي عَلَيْهِ الْحَقُّ وَلْيَتَّقِ اللَّهَ رَبَّهُ وَلَا يَبْخَسْ مِنْهُ شَيْئًا فَإِنْ كَانَ الَّذِي عَلَيْهِ الْحَقُّ سَفِيهًا أَوْ ضَعِيفًا أَوْ لَا يَسْتَطِيعُ أَنْ يُمِلَّ هُوَ فَلْيُمْلِلْ وَلِيُّهُ بِالْعَدْلِ وَاسْتَشْهِدُوا شَهِيدَيْنِ مِنْ رِجَالِكُمْ فَإِنْ لَمْ يَكُونَا رَجُلَيْنِ فَرَجُلٌ وَامْرَأَتَانِ مِمَّنْ تَرْضَوْنَ مِنَ الشُّهَدَاءِ أَنْ تَضِلَّ إِحْدَاهُمَا فَتُذَكِّرَ إِحْدَاهُمَا الْأُخْرَى وَلَا يَأْبَ الشُّهَدَاءُ إِذَا مَا دُعُوا وَلَا تَسْأَمُوا أَنْ تَكْتُبُوهُ صَغِيرًا أَوْ كَبِيرًا إِلَى أَجَلِهِ ذَلِكُمْ أَقْسَطُ عِنْدَ اللَّهِ وَأَقْوَمُ لِلشَّهَادَةِ وَأَدْنَى أَلَّا تَرْتَابُوا إِلَّا أَنْ تَكُونَ تِجَارَةً حَاضِرَةً تُدِيرُونَهَا بَيْنَكُمْ فَلَيْسَ عَلَيْكُمْ جُنَاحٌ أَلَّا تَكْتُبُوهَا وَأَشْهِدُوا إِذَا تَبَايَعْتُمْ وَلَا يُضَارَّ كَاتِبٌ وَلَا شَهِيدٌ وَإِنْ تَفْعَلُوا فَإِنَّهُ فُسُوقٌ بِكُمْ وَاتَّقُوا اللَّهَ وَيُعَلِّمُكُمُ اللَّهُ وَاللَّهُ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيمٌ٢٨٢﴾Ma’ana:“Domin in dayar ta manta to sai dayar ta tunasar da ‘yar’uwarta”. Suratul Bakarah, aya ta: 282.6. Kuma bata ta na zuwa da ma’anar abinda ya bace ba’a gani ba, kamar yadda ake cewa; rakumi ya bace.8. Riddah Da Raberabenta Da Kuma Hukunce-hukuncenta.Riddah: Abakin larabci idan akace ridda to ana nufin “Komawa baya”. Allah madaukakin sarki yana cewa:﴿يَا قَوْمِ ادْخُلُوا الْأَرْضَ الْمُقَدَّسَةَ الَّتِي كَتَبَ اللَّهُ لَكُمْ وَلَا تَرْتَدُّوا عَلَى أَدْبَارِكُمْ فَتَنْقَلِبُوا خَاسِرِينَ٢١﴾Ma’ana:“Kada ku koma da bayanku”.Amma ridda ayaran shara’a ita ce: “Kafirci bayan musulunci”. Allah madaukakin sarki yana cewa:﴿يَسْأَلُونَكَ عَنِ الشَّهْرِ الْحَرَامِ قِتَالٍ فِيهِ قُلْ قِتَالٌ فِيهِ كَبِيرٌ وَصَدٌّ عَنْ سَبِيلِ اللَّهِ وَكُفْرٌ بِهِ وَالْمَسْجِدِ الْحَرَامِ وَإِخْرَاجُ أَهْلِهِ مِنْهُ أَكْبَرُ عِنْدَ اللَّهِ وَالْفِتْنَةُ أَكْبَرُ مِنَ الْقَتْلِ وَلَا يَزَالُونَ يُقَاتِلُونَكُمْ حَتَّى يَرُدُّوكُمْ عَنْ دِينِكُمْ إِنِ اسْتَطَاعُوا وَمَنْ يَرْتَدِدْ مِنْكُمْ عَنْ دِينِهِ فَيَمُتْ وَهُوَ كَافِرٌ فَأُولَئِكَ حَبِطَتْ أَعْمَالُهُمْ فِي الدُّنْيَا وَالْآخِرَةِ وَأُولَئِكَ أَصْحَابُ النَّارِ هُمْ فِيهَا خَالِدُونَ٢١٧﴾Ma’ana:“Dukkan wanda ya yi riddah daga cikin ku ya bar addininshi ya kuma mutu yana kafiri to wadannan ayyukansu sun baci a duniya da kuma lahira, kuma wadannan sune ‘yan wuta, su kuma masu dawwama ne a cikin ta”. Suratul Bakarah, aya ta: 217.Rabe-raben Riddah: Ridda tana samuwane ta hanyar aikata daya daga cikin abubuwan da suke warware musulunci, kuma su abubuwan da suke warware musulunci suna da yawa, amma adunkule za su koma cikin abubuwa hudu:1. Riddah ta hanyar Magana, kamar mutum ya zagi Allah madaukakin sarki, ko ya zagi manzan Allah ﷺ ko mala’ika ko daya daga cikin manzannin Allah, ko ya yi da’awar sanin ilimin gaibu, ko kuma ya yi da’awar annabta, ko kuma ya gasgakata wanda ya yi da’awara annabtar, ko rokon wanin Allah ko neman taimakon wanin Allah a abinda babu mai iko akansa sai Allah, ko kuma neman tsari daga wurin wanin Allah.2. Riddah ta hanyar aiki, kamar yin sujjada ga gumaka ko bishiyoyi ko duwatsu ko kaburburuka ko kuma yi musu yanka. Ko kuma jefa Alkur’anai a wurare masu kazanta ko yin sihiri ko kuma koyon sihirin ko kuma koyar da shi, kuma yin hukunci da abinda Allah bai saukarba kuma yana ganin tabbacin halaccin hakan.3. Ridda ta hanyar kudurin zuci, kamar mutum ya kudurce yi wa Allah tarayya, ko kuma tabbas zina da giya da kudin ruwa duk halasne, ko kuma waina haramunce, ko kuma ya dunga ganin ai sallah ba wajibi bace, dadai wanin haka wanda tuni an yi ijima’i akan halaccinsu ko haramcinsu ko kuma wajibcinsu ijima’in da yake yankakken ijima’i wanda irinsa ba zai yi wu a jahilce shi ba.4. Ridda ta hanyar yin kokwanto a wani abu da ya gabata, kamar mutum ya yi shakkun cewa shirka haramunce, ko ya yi shakkun haramcin zina ko giya, ko kuma ya yi shakkun halaccin waina, ko ya yi shakkun manzancin manzan Allah ﷺ ko ya yi shakku akan manzancin wani daga cikin Annabawa, ko ya yi shakkun gaskiyar Annabin ko ya yi shakkun addinin musulunci, ko kuma ya yi shakkun dacewar addinin musulunci a wannan zamanin.Hukunce hukuncen Riddah: Hukunce hukuncen da suke tabbata bayan an tabbatar da ita riddar:1. Za’a nemi wanda ya yi riddar ya tuba, idan ya tuba ya dawo musulunci cikin kwanuka uku, za’a karbi tubansa kuma za’a kyaleshi.2. Idan kuma ya ki ya tuba to ya zama wajibi a kashe shi, saboda fadin Ma’aikin Allah ﷺ: “Duk wanda ya canza addininsa to ku kashe shi”. Bukharida da Abudawud suka ruwaito.3. Za’a hana shi taba dukiyarshi cikin kwanakin da ake neman ya tuba, to idan ya musulunta dukiyar ta zama ta shi, idan kuma bai musulunta ba to ta zama ganimace ga baitul mali daga lokacin da aka kashe shi ko kuma ya mutu akan riddah. Wasu malamai kuma suka ce daga lokacin da ya yi riddar za’a tura dukiyar tasa ga bukatun al’ummar musulmi.4. Yankewar gado tsakaninsa da makusantansa, shi ba zai gaje su ba, suma kuma ba za su gaje shi ba.5. Idan ya mutu ko aka kashe shi a riddar da ya yi to ba za a yi masa wankaba kuma ba za’a yi masa sallah ba sannan kuma ba za’a binne shi a makabartar Musulmaiba, kawai dai za’a binne shi ne a makabartar kafirai, ko kuma aje a sami wani wurin da ba makabartar Musulmaiba a binne shi.**** **** **** BABI NA BIYU:Maganganu Da Ayyuka Da Suke Kore Tauhidi Ko Kuma Su Rage Shi.A wannan babi akwai fasali fasali kamar haka:Fasali Na Farko: Da’awar sanin ilimin gaibu wajen duba hannu ko kasa ko taurari .Fasali Na Biyu: Sihiri (Asiri) da bokanci da kuma duba.Fasali Na Uku: Gabatar da hadayoyi da masu neman kusanci da masu alwashi suke yi a wurarn ziyara da kabarburuka da kuma girmamasu.Fasali Na Hudu: Girmama mutum mutumi da kuma kafe shi domin tunawa da shi.Fasali Na Biyar: Izgili da addini da kuma wulakantar da alfarmarsa.Fasali Na Shida: Hukunci da abinda Allah ba shi ya saukar ba.Fasali Na Bakwai: Da’awar cancantar shar’antawa ko halastawa ko haramtawa.Fasali Na Takwas: Shiga kungiyoyin Ilhadi da kuma kungiyoyi na jahiliyyah.Fasali Na Tara: Mahanga ta ci gaba a rayuwa.Fasali Na Goma: Layu da kuma tofetofe.Fasali Na Goma sha daya: Rantsuwa da wanin Allah da kuma tawassuli da neman taimako ga wani mahaluki da ba Allah ba. ***** ***** ***** Fasali Na Farko:Da’awar sanin ilimin gaibu wajen duba hannu ko kasa ko taurari da waninsu.Abinda ake nufi da gaibu. Shi ne abinda ya boyu ga mutane na al’amuran da zasu faru a nan gaba da kuma abinda basa ganinsa, kuma hakika tabbas Allah kadaine ya kebanta da saninsa, Allah madaukakin sarki yana cewa:﴿قُلْ لَا يَعْلَمُ مَنْ فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ الْغَيْبَ إِلَّا اللَّهُ وَمَا يَشْعُرُونَ أَيَّانَ يُبْعَثُونَ٦٥﴾Ma’ana:“Kace: Babu wani wanda yasan gaibu a sammai da kassai sai Allah kadai”. Suratun Naml, aya ta: 65. Babu wanda ya san gaibu sai Allah mai girma da daukaka shi kadai, hakika kuma Allah yana tsinkayar da manzanninsa a abinda ya so na gaibinshi domin wata hikimarsa da kuma maslaha, Allah madaukakin sarki yana cewa:﴿عَالِمُ الْغَيْبِ فَلَا يُظْهِرُ عَلَى غَيْبِهِ أَحَدًا٢٦ إِلَّا مَنِ ارْتَضَى مِنْ رَسُولٍ فَإِنَّهُ يَسْلُكُ مِنْ بَيْنِ يَدَيْهِ وَمِنْ خَلْفِهِ رَصَدًا٢٧﴾ Ma’ana:“(Shi Allah) masanin gaibine, kuma baya bayyanar da gaibinsa ga kowa. Saidai kawai ga wanda ya so na wani manzo”. Suratul Jinn, aya ta:26-27. Abin nufi ba ya tsinkayar da wani abu na gaibi saidai kawai ga wanda ya zaba da isar da manzancinsa to sai ya bayyanar masa da abinda ya so ba gaibi, domin shi manzon zai kafa hujja da shi akan annabtarsa ta hanyar bayyanar da mu’ujuzozi wacce daga cikinta ba da labari na gaibi wanda Allah ya tsinkayar masa da shi. Wannan ko yana game manzo cikin mala’iku da kuma manzo cikin mutane, amma Allah ba ya tsinkayar da waninsu, su kadai kawai yake tsinkayarwa. To dukkanin wanda ya yi da’awar sanin ilimin gaibi takowacce hanya cikin hanyoyi –in banda wanda Allah ya cire na manzanninsa- to shi tintirin makaryaci ne kuma kafiri ne. sawa’un ya yi wannan da’awar ta hanyar karatu a tafin hannu ne ko zane a kasa ko bokanci ko ta hanyar sihiri ko taurari ko ma wanin haka. Domin wannan ana samunshi wurin masu rufa ido da shaidanu na bada labarin wasu wurare da ba’a sansu ba ko ma wuraran da ba sa wannan wurin.Ko kuma bada rabarai na musabbabin wadansu cututtuka, sai su ce: wane ya aikata maka abu kaza-da-zaka wanda ya sa ka yi wannan rashin lafiyarne ta sanadiyyar haka, wannan fa anfanine da aljanu da kuma shaidanu, suke kuma bayyanawa mutane lalle wannan yana samuwane a gare su ta hanyar aikata irin wadan nan abubuwa don nuna yaudara da wayacewa…’ Shehul Islam Ibnu Taimiya yana cewa: “Su bokaye kamar kace dayansu yana da aboki a cikin shaidanu da ya ke ba shi labari na abinda ya shafi gaibu na abinda suke satowa na Magana, kuma sun kasance suna cudanya gaskiya da karya, hardai inda ya ce: “Daga cikin wadannan akwai wanda shaidani zai zo mishi da abinci, da kayan marmari da kayan zaki da wanin haka, irin abinda ba’a saminshi a wannan wurin. Akwai kuma daga cikinsu wanda aljani yake tashi da shi zuwa Makkah ko Baitul makadis ko wasu wuraran”. Nan maganar Ibnu Taimiya ta kare. Wani lokacin kuma bada labarin na su yana kasancewa ne tahanyar anfani da taurari, wato lura da halayen falaki akan abubuwan dake faruwa a kasa, kamar lokacin tasowar iska, da zuwan ruwan sama da canzawar farashin kayan masarufi, da wanin haka na al’amuran da wai riya cewa suna saninsu ne ta hanyar taurari ta hanyar da suke gudana da kuma inda suke haduwa da kuma inda suke rabuwa, sai kuma ka ji suna cewa; duk wanda ya yi aure a lokacin tauraro kaza da kaza to abu kaza da kaza zai same shi, wanda kuma ya yi tafiya a tauraro kaza da kaza to abu kaza zai same shi, kuma dukkanin wanda aka Haifa a tauraro kaza da kaza to ciwo kaza ko abu kaza zai same shi, kamar yadda suke bayyanar da haka a wasu mujallu masa manufa akan irin wadan nan jagwalgwalo akan abinda ya shafi buruji da irin abubuwan da suke tafiya akansu. Wasu daga cikin jahilai da masu raunin Imani suna tafiya wurin wadannan masu harkar taurari sai ya tambaye su dangane da yadda rayuwarsu ta fuskanta, da kuma sauran irin abinda ke gudana akan haka na aurene ko wanin haka, to dukkanin wanda ya yi da’awar sanin ilimin gaibi ko kuma ya gasgata wanda ya yi da’awar sanin ilimin gaibin to hakika shi mushirikine kuma kafiri, domin yana da’awar tarayya da Allah a cikin abinda ya kebanci Allah shi kadai, su fa taurari abubuwane da Allah ya halicce su kuma ya hore musu, ba su da wani abu na al’amari kokadan, basa nuni akan fargaba ko rashi lafiya ko mutuwa ko kuma rayuwa, kawai abin sani dukkanin wadannan ayyukan shaidanune wadanda suke satar maganar mala’iku. ***** ***** ***** Fasali Na Biyu:Sihiri Da Bokanci Da Kuma Duba Dukkanin wadannan al’amura ayyukane na shaidau da aka haramta, suna ruguzawa mutum Imani ko kuma su rage masa imani, domin ba’a yin su sai da abubuwa na shirka da Allah.1. Sihiri: Wani abune da yake a boye, kuma ba kasafe ake gane sababinsa ba, an kirashi da sunan sihirine domin anayinshi ne da boyayyun abubuwa wadanne dakyar ido yake ganinsu, sune kuma kamar layu tofi da wasu surakatai da magunguna da hayaki. Sannan shi asiri yana da hakika, domin daga cikinshi akwai wanda yake tasiri a zukata wani kuma a jiki sai ya sanya rashin lafiya ko ma ya yi kisa wani kuma y araba tsakanin miji da mata, tasirin nasa ya na kasancewa da kaddarar Ubangiji, -aikine na shaidan- kuma mafi yawa ba’a kaiwa ga aikata shi sai an hada da shirka da neman kusanci ga shaidanu na abinda suke so, da kuma amfani da abinda suke so din na shirka da Allah, saboda wannan ne shari’a ta hada shi da shirka inda Annabi ﷺ ya ce: “Ku nisanci abubuwa guda bakwai masu halakarwa”, sai sahabbai suka ce mene ne su? Sai ya cer : Shirka da Allah da kuma asiri”. Bukhari da Muslim ne suka ruwaito hadisin. Sihiri yana shiga shirka ta bangarori biyu:Bangare Na Farko: Yadda ake amfani da shaidanu acikinshi da kuma yadda ake dogaro da su, sannan kuma ga yadda ake neman kusancin su na abinda suke so, domin su tashi tsaye su yi hidima ga mai yin asirin, kuma shi sihiri yana cikin abinda shaidanu suke koyarwa, Allah madaukakin sarki yana cewa:﴿وَاتَّبَعُوا مَا تَتْلُو الشَّيَاطِينُ عَلَى مُلْكِ سُلَيْمَانَ وَمَا كَفَرَ سُلَيْمَانُ وَلَكِنَّ الشَّيَاطِينَ كَفَرُوا يُعَلِّمُونَ النَّاسَ السِّحْرَ وَمَا أُنْزِلَ عَلَى الْمَلَكَيْنِ بِبَابِلَ هَارُوتَ وَمَارُوتَ وَمَا يُعَلِّمَانِ مِنْ أَحَدٍ حَتَّى يَقُولَا إِنَّمَا نَحْنُ فِتْنَةٌ فَلَا تَكْفُرْ فَيَتَعَلَّمُونَ مِنْهُمَا مَا يُفَرِّقُونَ بِهِ بَيْنَ الْمَرْءِ وَزَوْجِهِ وَمَا هُمْ بِضَارِّينَ بِهِ مِنْ أَحَدٍ إِلَّا بِإِذْنِ اللَّهِ وَيَتَعَلَّمُونَ مَا يَضُرُّهُمْ وَلَا يَنْفَعُهُمْ وَلَقَدْ عَلِمُوا لَمَنِ اشْتَرَاهُ مَا لَهُ فِي الْآخِرَةِ مِنْ خَلَاقٍ وَلَبِئْسَ مَا شَرَوْا بِهِ أَنْفُسَهُمْ لَوْ كَانُوا يَعْلَمُونَ١٠٢﴾ Ma’ana:“Saidai shaidanu su ne suka kafirta, suna koyawa mutane asiri”. Suratul Bakarah, aya ta:102.Bangare Na Biyu: Abinda ke cikin shin a da’awar sanin ilimin gaibi, kuma da’awar sanin ilimin gaibi tarayyane da Allah madaukakin sarki, wannan ko tsattsar kafircine da kuma bata, Allah yana cewa:(وَلَقَدْ عَلِمُوا لَمَنِ اشْتَرَاهُ مَا لَهُ فِي الْآخِرَةِ مِنْ خَلَاقٍ )Ma’ana:“Kuma hakika sun sani ga dukkan wanda ya zabe shi (asirin) ba shi da wani rabo a lahira”. Suratul Bakarah, aya ta:102. Ma’ana ba shi da wani kaso, tunda ko ya kasance hakane to babu wata shakka akan cewar sihiri kafirci ne kuma shirkane yana warware akidar musulmi, kuma yana zama wajibi a kashe duk wanda yake aikata shi, kamar yadda da yawa cikin manyamanyan Sahabbai suka kashe, hakika kuma mutane sun yi sanyi kan abinda ya shafi masihirci da kuma sihirin, harma sukan lissafa shi wannan wani fannine na fannoni da ake alfahari da shi har ma ake baba kyaututtuka domin zaburar da masu aikata hakan, ka ga ana hada kulab kulab da tarurruka da musabaka ta masihirta, ka ga dubundubatar mutane da ‘yankallo duk sun halarta, lalle wannan yana nuna jahiltar wannan addini na musulunci da kuma ko’in-kula da abinda ya shafi akidah da kuma daukar mataki akan masu wada da ita.2. Bokanci Da Kuma Duba: su ne kuma masu da’awar sanin gaibu da abubuwan da suke na gaibi, kamar labarikan abunda zai faru nan gaba a kasa, da abunda ake saran zai faru, kuma inane wurin abin nan da ba’a gani ba, suna yin wannan ne ta hanyar anfani da shaidanu wadanda suke sato Magana daga sama, Allah madaukakin sarki yana ce wa:﴿هَلْ أُنَبِّئُكُمْ عَلَى مَنْ تَنَزَّلُ الشَّيَاطِينُ٢٢١ تَنَزَّلُ عَلَى كُلِّ أَفَّاكٍ أَثِيمٍ٢٢٢ يُلْقُونَ السَّمْعَ وَأَكْثَرُهُمْ كَاذِبُونَ٢٢٣﴾Ma’ana:“Shin in ba ku labarin wadanda shedanu suke sauka a wurin su?. Suna sauka ne akan dukkan tintirin makaryace kuma mai laifi. Suna jefa Magana mafiyawansu karya suke yi”. Suratus Shu’ara’i, aya ta: 221-223. Domin shi shaidani yana sato kalma guda daga cikin maganganun mala’iku, sai ya jefa wannan maganar a kunnuwan bokaye, sai shi boka ya kirkiri karaya guda dari sai ya hada da wannan Kalmar da shedan ya jefa masa, sai mutane su dinga gasgata shi ta sanadiyyar wannan Kalmar da ya ji ta daga sama. Allah shi kadai ne ya kebantu da sanin gaibi, duk kuma wanda da’awar ta rayya da shi a wani abu guda cikin wadannan abubuwa ta hanyar bokanci ne ko ma ta wata hanyar ko ya gasgata wanda ya yi da’awar hakan to hakika ya sanyawa Allah tarayya a abinda yake ya kebanci Allah ne shi kadai. Shi bokanci baya taba rabuwa da shirka, domin neman kusanci ne da shedanu da abinda su shedanun suke so, wannan ko shirkace a Rububiyyah ta yadda da’awar tarayya da Allah ne a iliminsa, kuma shirkace a Uluhiyyah ta hanyar neman kusanci ga wanin Allah da wani abu da ake bautawa Allah da shi. An karbo daga Abuhurairata t daga Annabi ﷺ: “Dukkan wanda ya je wurin boka ya kuma gasgatashi a binda ya fada, to hakika ya kafirta da abinda aka saukarwa (Annabi) Muhammad ﷺ”. Trimizi da Abudawuda ne suka ruwaito. Yana daga cikin abinda ya zama wajibi a fadakar akansa kuma a fadaku da shi: Cewar lalle masihirta da bokaye da masu duba, suna matukar wasa da tauhidin mutane, ta yadda suke bayyana kamar masu magani, sais u umarci maralafiya da ya yi yanka ga wanin Allah, kamar ya yanka rago mai siffa kaza da kaza, ko ya yanka kaza, ko kuma su rubuta musu wadansu kuraman bakake (Dalsami) wadanda suke na shirka ne da wasu surakatai na shedanu wai don neman tsari da cewa ai hirzi ne, sais u rayata a wuyansu ko su ajiye a akwatinan su ko kuma su sanya adakunansu. Wani kuma yana bayyana ne da sunan mai bada labarin gaibu, da bada labarin wasu abubuwan da ba’a san inda suke ba, ta yadda jahilai za su zo musu suna tambayarsu dangane da wasu abubuwansu da suka bata, sai su ba su labarinsu, ko kuma ma su kawo musu wadannan abubuwa ta hanyar ma’aikatansa cikin shaidanu. Wasu kuma suna bayyana ne da sunan waliyyai, wanda yake da wadansu abubuwa da suka sabawa al’ada da karamomi, kamar shiga wuta kuma ba za ta yi masa komai ba, ko yanka wuka a jikinsa (Kufegere), ko kuma ya sanya kansa karkashin tayar mota kuma babu wani abu da zai faru, ko dai makamantan haka cikin ayyukan masu dabo, wacce a hakikaninta sihiri ne daga cikin ayyukan shaidanu, ya ke kasancewa a hannun waddanan nan domin su fitini al’umma, ko kuma kawai wadansu al’amurane na masu rufa ido, kwatakwata ma ba su da wata hakika, kawai wadansu suddabaru ne da suke yin su a gaban masu kallonsu kamar ayyukan masihirtan fir’auna da suka yi da igiyoyi da kuma sanduna. Shehul Islma Ibnu Taimiyah yana cewa a mukabalar da suka yi masahirtan Badahi’iyyah wadanda suke bin darikar Rufa’iyyah, sai babban shehun badahi’iyya din ya ce bayan ya daga muryarsa: Mu muna da wadansu halaye, iri kaza da kaza, ya yi da’awar abubuwa na daban kamar wuta da waninta da kuma yadda sauka kebanta da wutar, kuma su suna cancantar su sallamawar wutar halin da suke ciki domin ita karan kanta wutar. Sai Shehul Islam Ibnu Taimiyah ya ce: Sai nace kuma na daga muryata cikin fushi: “Ni a yanzunnan ina kalubalantar dukkan wani mai bin darikar Rufa’iyyah a gabashin duniya yake ko a yammacinta, duk wani abu da suka yi a wuta to ni ma zan yi irin abinda suka yi dukkan wanda ya kone to an yi Nasara a kansa, a wanilokacin kuma ya ce: To tsinuwar Allah ta tabbata a kansa, amma hakan bayan an wanke jikin mu da Khal da kuma ruwan zafi, - to sai sarakuna da sauran mutane suka tambayeni akan wannan sharadi sai na ce: domin suna da wadansu dabaru wurin shiga wuta, suna yin wadansu abubuwa kamar manshafawa da kwadi da kuma Narinj da kuma dutsan dalk, sai mutane suka fashe da ihu, sai (shi shehun darikar) kawai ya fara bayyanar da ikonsa, sai ya ce: Ni da kai mu je mu lulluba a wata bariya bayan an shafe jikin mu da farar kasa, sai na ce: tashi mu je (in ji Ibnu Taimiya) sai naita maimaita masa akan ya tashi mu ke mu yi hakan, sai ya meke hannu zai cire rigarsa, sai na ce: A’a, har sai ka wanke jikinka da ruwan zafi da kuma Khal, sai kawai ya rikice akan irin al’adarsu sai ya ce: Dukkan wanda ya kasance yanakaunar sarki to ya kawo itatuwa, ko kuma cewa ya yi: ya kawo dauri dauri na itatuwa, sai na ce (in ji Ibnu Taimiyah) wannan wata doguwar Maganace da kuma raba kan mutane, ba wai shine abin nufi ba, kawai a kunna kyandir in sanya yatsa n aka sanya yatsanka bayan an wanke, duk kuma wanda yatsan shi ya kone to tsinuwar Allah ta hau kanshi ko kuma an yi Nasara akan shi, to fa lokacin da na fadi haka sai ya rikice ya kaskanta’’. nan maganar ta kare, majmu’ul fatawah, juzu’i na 11, shafi na: 445-446. Babban abin nufi dai shine wadannan shedanun suna yiwa mutane karya ta hanyar irin wadannan boyayyun dabarun.**** **** **** Fasali Na Uku:Gabatar da hadayoyi da masu neman kusanci da masu alwashi suke yi a wuraran ziyara da kabarbura da kuma girmamasu. Hakika Ma’aikin Allah ﷺ ya toshe dukkan wata hanya da take kaiwa zuwa ga shirka, kuma ya tsoratar makurar tsoratarwa, daga cikin haka ya yi bayanai kan abinda ya shafi kabarbura, hakika ya sanya wadansu ka’idoji da za su hana a bauta musu, ko a tsananta soyayyar wadanda ke cikinsu, daga cikin haka akwai:1. Lalle Shi Ma’aikin Allah ﷺ ya tsoratar da Guluwwuwi (wuce-gona-da-iri) akan abinda ya shafi waliyyai da kuma salihan bayi, domin hakan yana kaiwa ga bauta musu, sai ya ce: “Kashedinku da wuce-gona-da-iri, domin abinda ya halakar da wadanda suka gabaceku shine wuce gona-da-iri”. Ahmad da Tirmizi suka ruwaito. Ya kuma ce: “Kada ku kambamani kamar yadda Nasara suka kambama dan (Nana) Maryam, abin sani kawai Ni bawa ne, saboda haka kuce: Bawan Allah kuma Manzan Allah”. Bukhari da Ahmad suka ruwaito.2. Kuma Ma’aikin Allah ﷺ ya tsoratar da yin gini akan kabarbara, kamar yadda Abulhayyaj Al’asadi ya ce: Aliyu dan Abudalib t ya ce: Shin ba na aika kaba akan abinda Manzan Allah ﷺ ya aika ni ba, kada ka bar wani mutunmutumi sai ka share shi, kuma kada ka bar wani kabari da aka daga sai ka daidaita shi”. Muslim ne ya ruwaito shi. Ma’aikin Allah ﷺ ya hana sanyawa kabari siminti da kuma yin gini akan shi, an karbo daga Jabir t ya ce: Ma’aikin Allah ﷺ ya hana sanyawa kabari siminti, kuma ya hana a zauna akansa, kuma ya hana ayi gini akan sa”. Muslim ne ya ruwaito.3. Kuma Ma’aikin Allah ﷺ ya tsoratar da yin sallah a inda kaburbura suke, an karbo daga Aisha Allah ya kara mata yarda, ta ce: “Lokacin da rashin lafiya ya tsananta ga Ma’aikin Allah ﷺ sai ya fara rufe fuskarsa da gefan mayafinsa, idan ya yi sauki sai ya bude fuskar ta sa, sai ya ce yana wannan halin: Tsinuwar Allah ta tabbata akan Yahudawa da Nasara, sun dauki kaburburan Annabawa masallatai”. Yana tsoratarwa akan aikin da suka yi, da badin haka ba to da an daga kabarinsa saidai an yi gudun kada a dauke shi masallaci (wato wurin yin sallah)”. Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi. Kuma Ma’aikin Allah ﷺ ya ce: “Ku saurara! Lalle wadanda suka zo kafinku sun kasance suna daukar kaburburan Annabawansu masallatai, ku saurara! Kada ku riki kaburbura masallatai, domin lalle ni ina hanaku hakan”. Muslim ne ya ruwaito shi. Abinda ake nufi da daukar kaburbura masallatai shi ne yin sallah a wuraran ko da ba’a gina masallaci ba, domin dukkan wurin da aka yi nufin yin sallah to an dauke shi masallaci, kamar yadda ma’aikin Allah ﷺ ya ce: “An sanya min kasa masallaci kuma abin yin tsarki”. Bukhari da Muslim ne suka ruwaito, idan ko har aka gina masallaci akai to abin ya tsananta. Tabbas mutane sun sabawa wadannan hane-hane, suka aikata abinda Annabi ﷺ ya tsoratar, ta sanadiyyar haka suka afkawa shirka wacce take babba, suka gina masallatai akan kaburbura da kubba da kuma makamantan haka, suka sanya kaburburan wuraran ziyara da ake aikata dukkan nau’ukan manyan shirka, kamar yi wa kaburburan yanka da kuma kiran wadanda ke ciki da neman agajinsu da yi musu alwashi da wanin haka. Babban malamin nan Ibnu Kayyim –Allah ya yi masa rahama- yake cewa: Dukkan wanda ya hada tsakanin karantarwar Ma’aikin Allah ﷺ akan abinda ya shafi kaburbura, da kuma abinda ya yi umarnin a yi awurin da kuma abinda ya hana ayi a wurin, da kuma abinda Sahabbansa shi ﷺ suka kasance akai, sannan kuma ya ga irin abinda mafi yawan mutane suke akai ayau (wannan fa alokacin sa kenan), to zai ga abubuwa masu cin karo da juna masu warware juna ta yadda babu yadda za’a yi su hadu har abada. Hakika Ma’aikin Allah ﷺ ya hana yin sallah ana kallon kabari, wadannan kuwa suna sallah ne a inda kabarin yake, ya hana kuma a dauke su (su kabarburan) masallatai, wadannan kuma masallatai suke ginawa akan kaburburan suke kiransu mashahad, wadanda suke kore masallatan Allah, kuma ya hana akunna futulu a kaburbura, wadannan mutanan fa suna tsayawane su dukufa wurin kunna futulu a wadannan wurare, kuma Ma’aikin Allah ﷺ ya hana ariki kaburbura wuraren idi, wadannan fa sun riki wuraran idi da kuma yanke-yanke, suna fa taruwane a wuraran kamar yadda suke taruwa a wurin idi ko ma ya fi haka. Kuma Ma’aikin Allah ﷺ ya yi umarnin a daidaita kaburbura, kamar yadda yake a hadisi ingantacce riwayar Muslim daga Abuhayyaj Al’asadi, ya ce: Aliyu dan Abudalib t ya ce da ni: Shin bana turaka ba (na aikakaba) akan abinda Ma’aikin Allah ﷺ ya aika ni ba? akan karkabar wani hoto sai ka share fuskarsa,kuma kada kabar wani kabari da aka daga shi sai ka daidaita shi”. Muslim ne ya ruwaito. Kuma dai a cikin Sahihi Muslim din an karbo daga Sumamata da Shufay, ya ce: Mun kasance tare da Fudalata dan Ubaid akasar Rom, sai wani abokin mu ya rasu, sai Fudalata ya bada umarnin a daidaita kabarinsa, sannan sai ya ce: Na ji Ma’aikin Allah ﷺ yana umarnin da a daidaita su (kaburbura)”. Muslim ne ya ruwaito. Wadannan kuwa suna matukar sabawa wadannan hadisai guda biyu, ka ga suna daga kaburbura daga kamar dakuna, suna sanya kubba kubba, har dai inda yake cewa: Kallaci irin wannan banbanci mai girma tsakanin abinda Ma’aikin ﷺ Allah ya shar’anta da kuma abinda ya nufata na hanawa da ya yi na abinda ya gabata akan abinda ya shafi kaburbura, da irin abinda wadannan suka shar’anta (wa kawunansu) kuma suka nuface shi, babu shakka lalle irin barnar da take cikin wannan babu wani mahaluki da zai iya kididdigeta. Sannan sai ya shiga ya fara lissafo irin barnar da take ciki, hardai inda ya ce: kuma yana daga ciki, lalle abinda Ma’aikin Allah ﷺ ya shar’anta alokacin ziyarar kaburbura kawai shi ne tunatar da lahira, da kuma kyautawa wanda aka ziyarta ta hanyar yi masa addu’a da kuma roka masa rahama da roka masa gafara da roka masa yafiyar Allah. Ke nan sai wanda ya yi ziyara ya kasance ya kyautatawa kansa ya kuma kyautatawa mamaci, to sai wadannan mushirikan suka juya al’amarin suka jirkita addini, suka sanya babban abin nufi a ziyarar shi ne yin shirka da mamacin, da kuma rokon shi mamacin, da rokon bukatunsu da sauraron saukar albarka daga wurinshi, da neman taimakonsa akan makiyansu, da dai makamantan haka, sai suka kasance wadanda suka munana wa kawunansu kuma suka munana wa mamacin, inda da abinda ya kasance saidai da haramta masa albarka na abinda Allah madaukakin sarki ya shar’anta na addu’a da nema masa rahama da roka masa gafara”. Nana maganar ta kare. Da wannan ne zai bayyana a fili lalle irin gabatar da bakance da abubuwan neman kusanci a wuraran ziyara babbar shirka ce, kuma abinda ya haifar da hakan shi ne sabawa karantarwar Annabi ﷺ, alokacin da yake ya kamata kaburburan su kasance, na cewa kada ayi gini akai, kuma kada a zamar da wurin wurin sallah, domin fa tunda aka sanya mata kubba-kubba kuma aka saya masallatai a gefansu da kuma wuraran ziyara to fa jahilai za su yi tsammanin wadanda aka binne a ciki suna amfanarwa ko kuma suna cutarwa, kuma za su yi zaton su suna agazawa wanda ya nemi agajinsu, sai su yi zato suna biyan bukatun wadanda suka fake a wurinsu, sai su dinga kai yi musu alwashi da kuma kai musu abubuwan neman kusanta ga Allah, harfa wadannan kaburbura suka kasance gumakane da ake bautawa koma bayan Allah, kuma hakika Annabi ﷺ ya ce: “Ya Allah kada ka sanya kabari na gunki sai a bauta masa”. Malik da Ahmad suka ruwaito. Bakomai ya sa Ma’aikin Allah ﷺ ya yi wannan addu’ar ba saidai don wani abu zai faru irin wannan a kabarin da ba na shi ba ﷺ, kuma hakan ya faru a garuruwa masu yawa na Musulmai, amma kabarinsa hakika Allah ya kareshi da albarkar addu’arsa ﷺ. Dudda cewar akan sami wani lokacin da wadansu abubuwa suke faruwa a kabarin nasa ﷺ wadanda suka saba daga wurin wasu jahilai ko masu tatsuniya, saidai ba su da ikon kaiwa ga kabarin na sar, domin kabarinsa yana cikin gidansa ba wai yana cikin masallacin sa ba ne, kuma an kewaye shi da Katanga, kamar yadda babban malamin nan Ibnul Kayyim yake cewa a Nuniyyarsa:Sai (Allah) Ubangijin talikai ya amsa addu’arsa, sai ya kewashe da katangu uku’.***** ***** ***** Fasali Na Hudu:Girmama mutummutumi da kuma kafe shi domin tunawa da shi.Mutummutumi: Sura ce ta mutum ko dabba ko ma waninsu da yake da rai da ake yi da kasa ko siminti ko zinare…’. Kafewa kuma: alamace da duwatsu da mushirikai suka kasance suna yanke-yanke domin tunawa da wani shugaba ko wani da suke girmamawa. Hakika Ma’aikin Allah ﷺ ya tsoratar akan suranta abubuwa masu rai, musammamma suranta wadanda ake girmamawa acikin mutane, kamar malamai da sarakuna da masu ibada da kwamandoji da shuwagabanni, daidai ne wannan hoton ya kasance ta hanyar zanawane a alluna ko a takarda ko bango ko ma a tufafi ne, ko kuma ta hanyar dauka ne da kyamara a wannan lokacin, ko kuma ta hanyar sassakawa ne da ginawa akan tsarin mutummutumi, kuma Ma’aikin Allah ﷺ ya hana a manna hotuna a jikin bango da makamantansu, ko kuma kafe mutummutumi ko kuma kafewa domin tunawa da su, domin dukkanin wadannan wasu hanyoyi ne da suke kaiwa ga shirka, domin fa farkon shirka da ta faru a doron kasa ta kasance ne ta hanyar hoto da kuma kafe su, hakan kuwa ya kasance ne a zamanin Annabi Nuhu u, an sami wasu mutane wadanda suke salihan bayi ne, lokacin da ajali ya riske su mutanansu sun yi bakin cikin mutuwarsu, sai shedan ya riya musu akan su kafe mutummutumin su a wuraran zamansu inda suka kasance suna zama, kuma su kira su da sunayan su, sai suka aikata amma ba su bauta musu ba, har lokacin da wadannan da suka yi wannan aikin suka rasu ilimi ya bace kawai sai aka bauta musu, a lokacin da Allah ya aiko Annabinsa Nuhu u yana hana shirka wacce ta faru ta sanadiyyar wadancan hotunan da aka kakkafe sai mutanan suka ki karbar maganar Annabi Nuhu u din, suka cije akan bautawa wadannan hotuna da aka kakkafe wadanda suka koma gumaka:﴿وَقَالُوا لَا تَذَرُنَّ آلِهَتَكُمْ وَلَا تَذَرُنَّ وَدًّا وَلَا سُوَاعًا وَلَا يَغُوثَ وَيَعُوقَ وَنَسْرًا٢٣﴾Ma’ana: “Kuma suka ce; Kada ku kuskura ku bar allolinku, kuma kada ku kuskura ku bar Waddu kuma kada ku bar Suwa’a kuma kada ku bar Yagusa da kuma Nasra”. Suratu Nuh, aya ta: 23. Wadannan sunayan mutanan da aka suranta gangar jikinsu ne kamar ka ce a tsaye suke, domin tunawa da su da kuma girmama su. Yanzu kalli yadda karshen al’amarin ya kasance, ta sanadiyyar sanya wadannan mutummutumi domin tunawa ta yadda aka yi shirka da Allah kuma aka yi kiyayya da manzanninsa, abinda ya yi sanadiyyar halakar da su da ambaliya da kuma azabar da Allah ya tanada musu da kuma kin da mutane suke yi musu, abinda yake nuni akan hatsarin dake cikin hoto da kuma kafe hotunan, saboda wannan ne Annabi ﷺ ya la’anci masu hoto, kuma ya bada labarin cewa su sukafi kowa matsananciyar azaba a ranar alkiyama, kuma ya yi umarni da a share hotuna, kuma ya bada labarin cewa mala’iku ba sa shiga dakin da yake da hoto, dukkan wannan saboda irin yadda barnar da take cikin hoto da kuma irin mummunan hatsarin da zai sami al’umma ta sanadiyyar hoto a tauhidi, domin fa farkon shirka da ta faru a bayan kasa ta kasance ne ta sanadiyyar sanya hotuna, kuma daidai ne wannan sanyawar ta kasance hotuna ne ko kuma mutummutumi a wuraran zama ne ko kuma a dandali ko a wuraran shakatawa ne, dukkanin wannan haramunne a shar’ance domin hanyace ta kaiwa ga shirka da lalacewar akidar Musulmai, idan har kafirai sun kasance suna aikata irin wannan aiki a yau domin su ba su da wata akida da suke karewa, to ai bai halatta ga Musulmai su yi kamanceceniya da su ba, su kuma yi tarayya da su ba a wannan aiki domin kare akidarsu wacce take ita ce tushen karfinsu da kuma kwanciyar hankalinsu. Fasali Na Biyar:Izgili da addini da kuma wulakantar da alfarmarsa.Izgili da wannan addini ridda ne daga barin musulunci, kuma fita ne daga musulunci baki daya, Allah madaukakin sarki na cewa:﴿وَلَئِنْ سَأَلْتَهُمْ لَيَقُولُنَّ إِنَّمَا كُنَّا نَخُوضُ وَنَلْعَبُ قُلْ أَبِاللَّهِ وَآيَاتِهِ وَرَسُولِهِ كُنْتُمْ تَسْتَهْزِئُونَ٦٥ لَا تَعْتَذِرُوا قَدْ كَفَرْتُمْ بَعْدَ إِيمَانِكُمْ إِنْ نَعْفُ عَنْ طَائِفَةٍ مِنْكُمْ نُعَذِّبْ طَائِفَةً بِأَنَّهُمْ كَانُوا مُجْرِمِينَ٦٦﴾Ma’ana:“Ka ce: Yanzu da Allah da ayoyinsa da kuma Manzansa kuka kasance kuna izgili.? Kada ku bada hanzari tabbas kun kafirta bayan imaninku”. Suratut Taubah, aya ta: 65-66.Wannan ayar: Tana nuni akan izgili da Allah kafircine, kuma lalle izgili da Ma’aikin Allah kafurcine kuma lalle izgili da ayoyin Allah kafirci ne, to duk wanda ya yi izgili da daya daga cikin wadannan al’amura to shi mai izgiline da dukkansu, kuma abinda ya faru daga wadannan munafukan lalle su sun yi izgili da wannan Mazon na Allah ﷺ da kuma sahabbansa sai wannan ayar ta sauka, saboda haka izgili da wadannan abubuwa damfare yake da juna, to dukkanin wadanda suke sako-sako da kadaita Allah madaukakin sarki kuma suke girmama kiran waninsa na abinda ya shafi matattu, kuma idan aka umarce su da tauhidi aka kuma hana su shirka sai su dauki abin ba a bakin komai ba, kamar yadda Allah madaukakin sarki ya ce: ﴿وَإِذَا رَأَوْكَ إِنْ يَتَّخِذُونَكَ إِلَّا هُزُوًا أَهَذَا الَّذِي بَعَثَ اللَّهُ رَسُولًا٤١ إِنْ كَادَ لَيُضِلُّنَا عَنْ آلِهَتِنَا لَوْلَا أَنْ صَبَرْنَا عَلَيْهَا وَسَوْفَ يَعْلَمُونَ حِينَ يَرَوْنَ الْعَذَابَ مَنْ أَضَلُّ سَبِيلًا٤٢﴾Ma’ana:“Kuma idan suka ganka ba sa daukarka sai wanda za’a yi wa izgili (sai su ce) yanzu wannan Allah zai turo Manzo?. Kadan ya rage da ya batar da mu, mun bar ababan bautarmu da badin mun yi hakuri akan su ba”. Suratul Furkan, aya ta: 41-42. Saboda haka sai suka yi wa Manzan Allah ﷺ izgili a lokacin da ya hanasu shirka, kuma mushirikai ba su gushe ba suna muzanta Annabawa ba suna siffanta Annabawan da wawanci da kuma bata da hauka, idan Annabawan sun kirasu zuwa ga tauhidi, saboda irin abindake zukatansu na girmama shirka, wanndako zaka sami wanda yake da kamanceceniya da su, idan ya ga wanda yake kira zuwa ga tauhidi sai ya yi izgili da hakan, saboda irin abinda yake da shi na shirka, Allah madaukakin sarki yana cewa:﴿وَمِنَ النَّاسِ مَنْ يَتَّخِذُ مِنْ دُونِ اللَّهِ أَنْدَادًا يُحِبُّونَهُمْ كَحُبِّ اللَّهِ وَالَّذِينَ آمَنُوا أَشَدُّ حُبًّا لِلَّهِ وَلَوْ يَرَى الَّذِينَ ظَلَمُوا إِذْ يَرَوْنَ الْعَذَابَ أَنَّ الْقُوَّةَ لِلَّهِ جَمِيعًا وَأَنَّ اللَّهَ شَدِيدُ الْعَذَابِ١٦٥﴾Ma’ana:“Kuma akwai daga cikin mutane wadanda suke rikon wasu koma bayan Allah amatsayin kishiyoyi ga Allah, suna son su kamar yadda suke son Allah”. Suratul Bakara, aya ta:165. To dukkan wanda ya so wani halitta irin son da yakewa Allah to wannan mushirikene, kuma yana zama wajibi a banbance tsakanin so domin Allah da kuma so tare da Allah, to su fa wadannan da suka riki kaburbura gumaka zaka same su suna izgili da abinda yake na kadaita Allah ne da kuma bauta masa, suna kuma girmama abinda suka rika koma-bayan Allah a matsayin masu cetonsu, zaka ga dayansu yana rantsuwa mummunar rantsuwa akan karya, kuma ba zai iya bukar kirji ya rantse da shehunsa ba akan karya, dayawa kungiyoyi dabandaban zaka ga wani daga cikinsu yana ganin neman agaji da shehu kodai agaban kabarin shehun koma ba’a gaban kabarin ba ya fi mishi amfani da ya roki Allah a masallaci alokacin sahur. Kuma zaka ganshi yana izgili da wanda ba ya bin darikarsa kawai shi tauhidi yake bi, dayawan su fa suna rushe masallataine suna rayar da makabartu, to yanzu wannan ba wasa bane da Allah da ayoyinsa da kuma Manzonsa, sannan kuma da girmama shirka, wannanko yana aukuwa da yawa awurin masu bautar kabari a wannan lokaci.Izgili Ya Kasu Nau’i Biyu:Na Farko: izgili a bayyane, kamar wanda aya ta sauka akanshi, shi ne kuwa fadinsu; Mu fa ba mu taba ganin irin malamam mu haka ba masu yawan ci, kuma masu yawan karya kuma ga yawan tsoro idan aka hadu da abokan gaba. Ko makamancin haka cikin maganganun masu izgili, kamar kuma yadda wasu suke cewa: wannan addinin na ku shi ne addini na biyar, wasu kuma su ce: addininku kurma ne, wasu kuma su ce; idan sun ga masu umarni da kyakkyawan aiki masu kuma hana barna: Kai ga masu addininan (ga Ustazai nan), kawaidai don tozartar da su, da makamantan haka wadanda ba za su iya kirguwaba sai da bakar wahala (kamar: saki wandon ka tsalleke ruwa, ko ka tsallake wuta, ko ya sa wandon kaninsa), abinda yake da matukar hatsari akan maganar wadanda ayar ta sauka akan su.Nau’i Na Biyu: Jurwaye me kama da wanka, wannanko kogine da bashi da gaba, kamar kifta idanu, da fitar da harshe, da tura lebe, da taba wani da hannu alokacin karanta littafin Allah ko kuma Sunnar Ma’aikin Allah ﷺ, haka namma alokacin umarni da kyakyyawa da kuma hani da mummuna, irin wannan ne wasu suke cewa; Ai shi musulunci bai yi ba ga ‘yankarni na ashirin saidai ‘yanshekarun tsakiya, saidai shi ya makara ko ya dawo, kuma akwai cin zarafi ko dabbanci a abinda ya shafi haddi da hukuncin gobe-ka-kuma, da kuma cewa an zalinci mace hakkokinta ta yadda aka halasta saki da auran mata hudu, da yadda suke cewa; Dokokin kasa su suka fi dacewa da mutane sama da dokokin musulunci, ka ji suna kiran wadanda suke kira zuwa ga tauhidi suna kuma tsoratarwa kan bautar kaburbura; mai kaifin kishin addini, ko kuma yana son ya raba kan Musulmi, ko kuma ai wannan bawahabiye ne ko ‘yan mazahaba ta biyarne, dadai makamantan haka wadanda suke dukkaninsu batanci ne ga wannan addini na musulunci da kuma masu bin karantarwarsa, kuma izgiline da ingantacciyar akidah, ba da dabara bane mumini ya bi Allah ba kuma ba da karfi bane kafiri ya kaucewa Allah saidai da abinda Allah yaga dama ne, yana fa daga cikin hakan izgilin nasu da dukkan wanda ya yi ruko da Sunnah guda daga cikin sunnonin Ma’aikin Allah ﷺ, sai ka ji suna cewa: Ai addini ba’a gashi yake ba, wai suna nufin aibanta gemu dadai abinda ya yi kama da irin wadannan munanan maganganu.**** ***** ***** Fasali Na Shida:Hukunci da abinda Allah ba shi ya saukar ba. Yana daga cikin tabbatuwar Imani da Allah madaukakin sarki da kuma bauta masa Kankan dakai ga hukunce-hukuncensa, da kuma yarda da shari’arsa da kuma komawa ga littafinsa da kuma sunnar Ma’aikinsa ﷺ a lokacin da aka sami sabani a maganganu ko a tauhidi ko kuma arikice-rikicen kisa ko rauni ko kuma dukiya da kuma sauran hakkoki, to Allah madaukakin sarki shine mai hukunci kuma daga gareshi za’a nemi hukunci. Yana zama wajibi akan mahukunta da su yi hukunci da abinda Allah ya saukar, kuma yana zama wajibi ga wadanda ake shugabanta da su kai kararrakin su ga abinda Allah ya saukar a littafinsa da kuma sunnar Manzansar, Allah madaukakin sarki yana cewa:﴿إِنَّ اللَّهَ يَأْمُرُكُمْ أَنْ تُؤَدُّوا الْأَمَانَاتِ إِلَى أَهْلِهَا وَإِذَا حَكَمْتُمْ بَيْنَ النَّاسِ أَنْ تَحْكُمُوا بِالْعَدْلِ إِنَّ اللَّهَ نِعِمَّا يَعِظُكُمْ بِهِ إِنَّ اللَّهَ كَانَ سَمِيعًا بَصِيرًا٥٨﴾Ma’ana:“Lalle Allah yana umartarku da ku mayar da amanoni zuwa ga masu ita, kuma idan za ku yi hukunci a tsakanin mutane to ku yi adalci”. Suratun Nisa’i, aya ta: 58. Ya kuma fada ta bangaren wadanda ake shugabanta.﴿يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا أَطِيعُوا اللَّهَ وَأَطِيعُوا الرَّسُولَ وَأُولِي الْأَمْرِ مِنْكُمْ فَإِنْ تَنَازَعْتُمْ فِي شَيْءٍ فَرُدُّوهُ إِلَى اللَّهِ وَالرَّسُولِ إِنْ كُنْتُمْ تُؤْمِنُونَ بِاللَّهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ ذَلِكَ خَيْرٌ وَأَحْسَنُ تَأْوِيلًا٥٩﴾Ma’ana:“Ya ku wadanda suka yi imani! ku bi Allah kuma ku bi Ma’aikin Allah da kuma shugabanninku, to idan kuka yi jayayya akan wani abu to ku mayar (da hukunci) shi zuwa ga Allah da kuma Ma’aikin Allah in har kun kasance kuna yin Imani da Allah da kuma ranar lahira, yin haka shi ne mafi alheri kuma mafi kyawun fassara”. Suratun Nisa’i, aya ta: 59. Sannan sai Allah madaukakin sarki ya bayyana imani bai taba haduwa da kai kara zuwa ga abinda ba Allah ne ya saukar da shi ba, sai Allah madaukakin sarki ya ce:﴿أَلَمْ تَرَ إِلَى الَّذِينَ يَزْعُمُونَ أَنَّهُمْ آمَنُوا بِمَا أُنْزِلَ إِلَيْكَ وَمَا أُنْزِلَ مِنْ قَبْلِكَ يُرِيدُونَ أَنْ يَتَحَاكَمُوا إِلَى الطَّاغُوتِ وَقَدْ أُمِرُوا أَنْ يَكْفُرُوا بِهِ وَيُرِيدُ الشَّيْطَانُ أَنْ يُضِلَّهُمْ ضَلَالًا بَعِيدًا٦٠﴾Ma’ana: “Shin ba ka ga wadannan da suke riya cewa lalle su sun yi Imani da abinda aka saukar maka da kuma abinda aka saukar kafin kai suna son su kai hukunce-hukuncensu zuwa ga dagutu kuma hakika an umarce su da su kafirce masa, kuma shedan yana son ya batar da su batarwa mai nisa”. Suratun Nisa’i, aya ta:60 har zuwa inda Allah madaukakin sarki yake cewa:﴿فَلَا وَرَبِّكَ لَا يُؤْمِنُونَ حَتَّى يُحَكِّمُوكَ فِيمَا شَجَرَ بَيْنَهُمْ ثُمَّ لَا يَجِدُوا فِي أَنْفُسِهِمْ حَرَجًا مِمَّا قَضَيْتَ وَيُسَلِّمُوا تَسْلِيمًا٦٥﴾Ma’ana:“To tabbas ba sai na rantse da Ubangijinkaba! Ba za su taba yin imaniba har sai sun saka mai hukunci a dukkan abinda ya gudana tsakanin su sannan kuma ba su sami wani kaikayi ba azukatansu cikin dukkanin abinda ka hukunta, su kuma sallama hakikanin sallamawa”. Suratun Nisa’i, aya ta: 65. Sai Allah mai girma da daukaka ya kore, korewa wacce aka karfafeta da rantsuwa ya kore Imani ga dukkanin wanda bai kai kara wurin Manzan Allah ﷺ ba, kuma ya yarda da hukuncin, kuma ya karbi hukuncin, kamar kuma yadda ya yi hukuncin kafircin shuwagabanni wadanda ba sa hukunci da abinda Allah ya saukar, ya kuma yi hukuncin cewa su azzalumaine kuma su fasikai ne, Allah madaukakin sarki yana cewa:﴿إِنَّا أَنْزَلْنَا التَّوْرَاةَ فِيهَا هُدًى وَنُورٌ يَحْكُمُ بِهَا النَّبِيُّونَ الَّذِينَ أَسْلَمُوا لِلَّذِينَ هَادُوا وَالرَّبَّانِيُّونَ وَالْأَحْبَارُ بِمَا اسْتُحْفِظُوا مِنْ كِتَابِ اللَّهِ وَكَانُوا عَلَيْهِ شُهَدَاءَ فَلَا تَخْشَوُا النَّاسَ وَاخْشَوْنِ وَلَا تَشْتَرُوا بِآيَاتِي ثَمَنًا قَلِيلًا وَمَنْ لَمْ يَحْكُمْ بِمَا أَنْزَلَ اللَّهُ فَأُولَئِكَ هُمُ الْكَافِرُونَ٤٤﴾Ma’ana:“Dukkan wanda bai yi hukunci da abinda Allah ya saukar ba to wadannan su ne kafirai”. Suratul Ma’idah, aya ta:44.﴿ وَمَنْ لَمْ يَحْكُمْ بِمَا أَنْزَلَ اللَّهُ فَأُولَئِكَ هُمُ الظَّالِمُونَ٤٥﴾Ma’ana:“Dukkanin wanda bai yi hukunci da abinda Allah ya saukarba to wadannan su ne azzalimai”. Suratul Ma’aidah, aya ta: 45.﴿ وَمَنْ لَمْ يَحْكُمْ بِمَا أَنْزَلَ اللَّهُ فَأُولَئِكَ هُمُ الْفَاسِقُونَ٤٧﴾Ma’ana:“Dukkan wanda bai yi hukunci da abinda Allah ya saukar ba to wadannan su ne fasikai”. Suratul Ma’idah, aya ta:47. Ba makawa sai an yi hukunci da abinda Allah ya saukar, kuma sai an kai karar hukunce-hukunce zuwa ga reshi cikin dukkan jayayya a maganganu na ijtihadi a tsakanin malamai, ba abinda za’a karba sai abinda littafin Allah da Sunnar Ma’aikin Allah ﷺ suka tabbatar, ba tare da makalkalewa mazahaba ba, ko kuma karkata ga wani malami kadai ba, da ma abinda ya shafi kararraki da rikice-rikice a hakkoki ba wai sai abinda mutum shi kadai ba, kamar yadda yake a wasu kasashe da suke jingina kansu ga musulunci, domin shi musulunci bakidaya ake yinsa ba’a yinsa rabi, Allah madaukakin sarki yana cewa:﴿يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا ادْخُلُوا فِي السِّلْمِ كَافَّةً وَلَا تَتَّبِعُوا خُطُوَاتِ الشَّيْطَانِ إِنَّهُ لَكُمْ عَدُوٌّ مُبِينٌ٢٠٨﴾Ma’ana:“Ya ku wadanda suka yi Imani! Ku shiga musulunci bakidaya”. Suratul Bakarah, aya ta: 208, da kuma fadin Allah madaukakin sarki:﴿ أَفَتُؤْمِنُونَ بِبَعْضِ الْكِتَابِ وَتَكْفُرُونَ بِبَعْضٍ ٨٥﴾Ma’ana:“Yanzu zaku dinga yin Imani da wani sashi na littafi kuma ku dinga kafircewa wani sashi”?. Suratul Bakarah, aya ta:85 Haka nan kuma yana zama wajibi ga dukkanin masu bin mazahabobi da su mayar da maganganun shugabanninn mazahabobinsu ga Alkur’ani mai girma da kuma karantarwar Annabi ﷺ, to dukkanin abinda ya yi daidai da su sai su rike shi amma wanda ya saba sai su ajiye shi ba tare da mazahabanci ba ko makalkalewa wani malami ba, musammam a abinda ya shafi al’amuran akidah, domin dukkanin limaman mazahabobin nan sun yi wasiyyah da hakan, kuma wannan shine mazahabinsu bakidayansu, to kuma dukkan wanda ya saba hakan to bai kasance me binsu ba, ko da ko ya jingina kansa ga resu, to shikan yana cikin wadanda Allah madaukakin sarki ya fada dangane da su:﴿اتَّخَذُوا أَحْبَارَهُمْ وَرُهْبَانَهُمْ أَرْبَابًا مِنْ دُونِ اللَّهِ وَالْمَسِيحَ ابْنَ مَرْيَمَ وَمَا أُمِرُوا إِلَّا لِيَعْبُدُوا إِلَهًا وَاحِدًا لَا إِلَهَ إِلَّا هُوَ سُبْحَانَهُ عَمَّا يُشْرِكُونَ٣١﴾Ma’ana:“sun riki manyan malamansu da masu bautar cikinsu ababan bauta koma bayan Allah, (kuma sun riki) Masihu (Annabi Isa u) dan Maryam (abin bauta)”. Suratut Taubah, aya ta:31. Wannan ayar bawai ta takaitu ga Nasara ba ne kadai, a’a ta shafi dukkan wanda ya aikata aiki irin na su. Duk wanda ya saba abinda Allah ya yi umarni da shi ya kuma saba abinda Manzanshi ﷺ ya yi umarni da shi ta yadda ya yi hukunci a tsakanin mutane da abinda ba shi Allah ya saukarba, ko kuma shi ya nemi hakan kawai domin son zuciyarsa da abinda shi yake so to wannan ya cire suturar musulunci da Imani da ke wuyansa, ko da ya riya cewa ai shi muminine, domin Allah madaukakin sarki ya yi inkari ga dukkan wanda ya riya hakan kuma ya karyata su a riyawar da suka yi, alokacin da ya tattara maganar da yace ((Suna riyawa)), na kore imaninsu, domin (suna riyawa) saudayawa ana fadanshi ne ga wanda yake da’awar wani abu wanda yake shi makaryaci ne a wannan abun, domin ya sabawa abinda ta kunsa kuma aikinsa yana kore hakan, abinda zai tabbatar da hakan shi ne fadin Allah madaukakin sarki:﴿ وَقَدْ أُمِرُوا أَنْ يَكْفُرُوا بِهِ٦٠﴾Ma’ana:“Kuma tuni an umarcesu da su kafirce masa”. Suratun Nisa’i, aya ta:60. Domin kafircewa dagutu rukunine daga cikin rukunan tauhidi kamar yadda ya zo a ayar Suratul Bakarah (wato fadin Allah madaukakin sarki:﴿لَا إِكْرَاهَ فِي الدِّينِ قَدْ تَبَيَّنَ الرُّشْدُ مِنَ الْغَيِّ فَمَنْ يَكْفُرْ بِالطَّاغُوتِ وَيُؤْمِنْ بِاللَّهِ فَقَدِ اسْتَمْسَكَ بِالْعُرْوَةِ الْوُثْقَى لَا انْفِصَامَ لَهَا وَاللَّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٌ٢٥٦﴾Ma’ana:“Dukkanin wanda ya kafircewa dagutu kuma ya yi Imani da Allah to hakika ya yi riko da igiya mai karfi”. Suratul Bakarah, aya ta: 256. Domin kuwa lalle kaiwa dagutu hukunci ai Imani da shi ne). Kore imani dangane da wanda bai yi hukunci da abinda Allah ya saukarba, yana nuna cewa ashe hukunci da shari’ar Allah imanine kuma akidace kuma bautawa Allah ne, wannan ya zama kowanne musulmi ya bautawa Allah da shi, ba wai za’a yi hukunci da shari’ar Allah bane don cewa hukunci da ita shi ya fi yi wa mutane kyau kuma shi ya fi tabbatar da tsaro ba, domin wasu sun fi maida hankali akan wannan bangaren, sai su bar bangaren farko, kuma Allah madaukakin sarki hakika ya aibanta wadanda suke hukunci da shari’ar Allah domin fa’idar kansa ba wai domin bauta ga Allah madaukakin sarki ba, Allah mai girma da daukaka yana cewa:﴿وَإِذَا دُعُوا إِلَى اللَّهِ وَرَسُولِهِ لِيَحْكُمَ بَيْنَهُمْ إِذَا فَرِيقٌ مِنْهُمْ مُعْرِضُونَ٤٨ وَإِنْ يَكُنْ لَهُمُ الْحَقُّ يَأْتُوا إِلَيْهِ مُذْعِنِينَ٤٩﴾Ma’ana:“Kuma idan aka kirayesu zuwa ga Allah da Manzonsa domin ya yi hukunci a tsakaninsu kawai sai wasu tawaga daga cikinsu su juya baya, idan kuwa ya kasance su suke da gaskiya sai su zo wurinsa a guje”. Suratun Nur, aya ta: 48-49. Su basa himmatuwa sai akan abinda suke so, abin kuwa da ya sabawa son zuciyarsu sai su kawar da kawunansu, domin su basa bautawa Allah da kai kararrakinsu wurin Manzon Allah ﷺ.Hukuncin wanda ya yi hukunci da abinda ba shi Allah ya saukar ba.Allah madaukakin sarki yana cewa: ﴿ وَمَنْ لَمْ يَحْكُمْ بِمَا أَنْزَلَ اللَّهُ فَأُولَئِكَ هُمُ الْكَافِرُونَ٤٤﴾Ma’ana:“Dukkan wanda bai yi hukunci da abinda Allah ya saukar ba to wadannan su ne kafirai”. Suratul Ma’idah, aya ta:44. A wannan aya mai girma lalle yin hukunci da abinda ba shi Allah madaukakin sarki ya saukarba kafirci ne, wannan kafircin kuma a wani lokaci yana zama kafirci babba wanda yake fitarwa daga musulunci, a wani lokacin kuma yana kasancewa kafircine karami wanda ba ya fitarwa daga musulunci, wannanko yana kasancewa gwargwadon halin wanda ya yi hukuncin, idan ya kudurce cewa hukunci da abinda Allah ya saukar ba wajibibane, wannan wani zabine aka ba shi, ko kuma ya wulakanta hukuncin Allah, ya kudurce cewa abinda ba shi ban a dokoki da aka kaga su suka fi, kuma shi hukuncin Allah ba zai yi daidai da wadandake wannan zamanin ba, ko kuma ya yi nufin farantawa kafirai da munafukai ta hanyar yin hukunci da abinda ba shi Allah ya saukarba to wannan kafircine wanda yake babba. Idan kuwa ya kudurce wajibcin hukunci da abinda Allah ya saukar ya kuma sanshi a wannan abunda ya faru sai kuma ya kauce masa tare da tabbatarwar da ya yi cewa shi wanda ya cancanci ukubane to wannan melefine, ana kiransa kafiri kuma kafirci karami, idan kuma ya jahilci hukuncin Allah a wannan abinda ya farun tare da yin iyakar kokarin wurin sanin hukuncin Allah din sai kuma ya kuskure masa, to wannan mekuskure ne, yana da ladan ijitihadin da ya yi kuma kuskuransa an yafe masa shi, wannan fa a hukunci a wani abu da ya faru kadai, amma hukunci a bubuwa dadama to wannan yakan sha-ban-ban. Shehul Islam Ibnu Taimiyah ya cewa: To hakika shi mai hukunci idan ya kasance mai riko da addinine saidai ya yi hukunci da abinda ba shi Allah ya saukar ba to ya kasance cikin ‘yanwuta, idan kuma ya kasance ya sani saidai ya yi hukunci da sabanin gaskiyar da ya sani to ya kasance cikin ‘yanwuta, idan kuma ya yi hukunci ba da adalciba ba kuma da ilimiba to ai shi yafi cancantar zama cikin ‘yanwuta, to wannan idan ya yi hukuncine awata matsala guda ga wani mutum, amma idan ya yi hukuncine kuma gamamman hukunci a addinin Musulmai, sai ya sanya gaskiya karya ya kuma maida karya gaskiya, ya maida Sunnah bidi’a ya kuma maida bidi’a Sunnah, ya maida abu mai kyau marakyau ya kuma maida marakyau mai kyau, ya hana abinda Allah da Manzonsa suka suka yi umarni, ya kuma yi umarnin abinda Allah da Manzonsa suka hana to wannan wani nau’ine kuma na badan da Allah ne Ubangijin talikai zai yi hukunci, kuma abin bautar Manzanni mamallakin ranar sakamako wanda yake gareshi kadai dukkan godiya take a duniya da kuma lahira,﴿وَلَا تَدْعُ مَعَ اللَّهِ إِلَهًا آخَرَ لَا إِلَهَ إِلَّا هُوَ كُلُّ شَيْءٍ هَالِكٌ إِلَّا وَجْهَهُ لَهُ الْحُكْمُ وَإِلَيْهِ تُرْجَعُونَ٨٨﴾Ma’ana: ((Shi kadai yake da hukunci kuma gareshi ake mayar da ku)). Suratul Kasas, aya ta:88,﴿هُوَ الَّذِي أَرْسَلَ رَسُولَهُ بِالْهُدَى وَدِينِ الْحَقِّ لِيُظْهِرَهُ عَلَى الدِّينِ كُلِّهِ وَكَفَى بِاللَّهِ شَهِيدًا٢٨﴾Ma’ana:((Shi ne Allahwanda ya aiko Manzansa da shiriya da kuma addinin da yake na gaskiya domin ya bayyanar da shi akan addini bakidayansa, kuma Allah ya isa ya mai shaida)). Suratul Fath, aya ta: 28.Ya kuma ce: Babu wata shakka lalle dukkan wanda bai kudurce wajibcin hukunci da abinda Allah ya saukarba akan Manzansa ﷺ to shi kafirine, kuma dukkanin wanda ya halasta yin hukunci a tsakanin mutane da abinda shi yake ganinsa adalci ba tare da bin abinda Allah ya saukarba to shi kafiri ne, domin fa, babu wata al’umma face tana umarni da yin hukunci da adalci, kuma adalcin yakan kasance atsarin nasu abinda manasu suka gani shine adalci, kai!, da yawa daga cikin wadanda suke jingina kansu da musulunci suna yin hukuncine da al’adunsu wacce Allah bai saukar da itaba (kamar gargajiyar wadanda suka gabacesu) sun kasance shuwagabanni ne da ake yiwa biyayya, kuma suke ganin wannan shine abinda ya kamata ayi hukunci da shi ba wai littafin Allah da Sunnar Annabinsa ﷺ ba, wannanko shi ne kafirci. Domin da yawa daga cikin mutane sun musulunta saidai ba sa hukunci saida al’adunsu wacce shuwagabanninsu suke bada umarni. To su wadannan idan suka san cewa bai halatta a garesu yin hukunci face saida abinda Allah ya saukar kuma ba su rungumi hakan ba, kawaidai su sun halatta yin hukunci da sabanin abinda Allah ya saukar to su kafiraine”. Nan maganar ta kare. Shehun Malami Muhammad dan Ibrahim ya ce: Amma wanda aka ce akansa: Kafircin da baikai kafirci ba, idan ya kai kara zuwa ga wanin Allah tare da kudurcewarsa cewa shi mailaifine, kuma lalle hukuncin Allah shine gaskiya, to wannan shine wanda irin hakan yakan auku gareshi sau guda da makamantan haka. Amman wanda ya sanya dokin kasa ta wurin tsara al’amura da kuma kankanda kai gareta to wannan kafirci ne, koda sunce kuwa mun yi kuskure hukuncin Allah shine mafi adalci, to wannan kafircine wanda yake fitarwa daga musulunci”. Sai malam Allah ya jikanshi da gafara ya rabe tsakanin wani hukunci guda wanda bai maimaituwa da kuma gamamman hukunci wanda yake shi ake komawa cikin dukkanin hukunce hukunce ko galibin hukunce-hukunce, ya kuma tabbatar da cewa wannan kafircin yana fitarwa daga muslunci kaitsaye, kuma abinda ya kawo haka lalle dukkan wanda ya ajiye shar’ar musulunci gefe guda ya kuma sanya dokokin kasa makwafinsu to daliline akan cewa lalle yana ganin dokokin kasa su suka fi kuma suka dacewa akan shari’ar musulunci, wannanko ba kokwanto cewa kafircine kuma babba wanda yake fitarwa daga musulunci kuma yake warware tauhidi.**** **** **** Fasali Na Bakwai: Da’awar cancantar shar’antawa ko halastawa ko haramtawa. Shar’anta hukunce hukunce da bayi zasu tafi akai a wurin ibadarsu da kuma ma’amalolinsu da sauran al’amuransu wadanda suke hukunci akan rikicin dake tsakaninsu kuma suke kashe wutar rikici to wannan hakkin Allah ne madaukakin sarki wanda yake shine Ubangijin mutane kuma mahaliccin halitta﴿ أَلَا لَهُ الْخَلْقُ وَالْأَمْرُ تَبَارَكَ اللَّهُ رَبُّ الْعَالَمِينَ٥٤﴾ma’ana:“Ku saurara dukkanin halitta ta sa ce da kuma al’amurra, albarkatun Allah wanda yake shine Ubangijin talikai sun girmama”. Suratul A’araf, aya ta:54. Shi ne kuma wanda yasan abinda ya fi dacewa da bayinsa sai ya shar’anta musu shi, saboda hukuncin cewa shine mahaliccinsu yake shar’anta musu, kuma saboda hukuncin su bayinsa ne suke karbar hukunce-hukuncensa, kuma fa’idar hakan tana komawa garesu, Allah madaukakin sarki yana cewa:﴿يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا أَطِيعُوا اللَّهَ وَأَطِيعُوا الرَّسُولَ وَأُولِي الْأَمْرِ مِنْكُمْ فَإِنْ تَنَازَعْتُمْ فِي شَيْءٍ فَرُدُّوهُ إِلَى اللَّهِ وَالرَّسُولِ إِنْ كُنْتُمْ تُؤْمِنُونَ بِاللَّهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ ذَلِكَ خَيْرٌ وَأَحْسَنُ تَأْوِيلًا٥٩﴾Ma’ana:“To idan kuma kuka yi jayayya akan wani abu to ku mayar da (hukuncinsa) ga Allah da Manzonshi in har kun kasance kuna yin Imani da Allah da kuma ranar karshe, yin hakan shine mafi alheri kuma mafikyawun makoma”. Suratun Nisa’i, aya ta: 59. Da kuma fadinsa mai girma da daukaka:﴿وَمَا اخْتَلَفْتُمْ فِيهِ مِنْ شَيْءٍ فَحُكْمُهُ إِلَى اللَّهِ ذَلِكُمُ اللَّهُ رَبِّي عَلَيْهِ تَوَكَّلْتُ وَإِلَيْهِ أُنِيبُ١٠﴾Ma’ana:“Kuma dukkan abinda kuka yi sabani a kansa to hukuncinsa na ga Allah, wannac dinku shine Allah wanda yake Ubangijina”. Suratus Shurah, aya ta:10. Kuma Allah mai girma da daukaka bai taba yard aba bayinsa su dauki wani mai shar’anta musu koma bayansa, sai Allah madaukakin sarki ya ce:﴿أَمْ لَهُمْ شُرَكَاءُ شَرَعُوا لَهُمْ مِنَ الدِّينِ مَا لَمْ يَأْذَنْ بِهِ اللَّهُ وَلَوْلَا كَلِمَةُ الْفَصْلِ لَقُضِيَ بَيْنَهُمْ وَإِنَّ الظَّالِمِينَ لَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ٢١﴾Ma’ana:“Koko sunada abokan tarayya suka shar’anta musu abinda yake addinin wanda Allah bai yi izini da shi ba”. Suratus Shurah, aya ta: 21. To dukkan wanda ya karbi shar’antawar wani koma bayan shar’antawar Allah to hakika ya yi tarayya da Allah madaukakin sarki, kuma dukkanin abinda Allah da Manzonsa basu shar’antashi ba na ibadu to bidi’ane, ita kuma bidi’a dukkaninta bata ce, Ma’aikin Allah ﷺ ya ce: “Dukkan wanda ya farar da wani abu abinda babu shi to an mayar masa”. Bukhari da Muslim suka ruwaito. A wata ruwayar kuma: “Dukkan wanda ya aikata wani aiki da ba mu muka umarce shi ba to an mayar masa”. Bukhari da Muslim suka ruwaito. Kuma dukkanin abinda Allah da Manzansa basu shar’anta shi ban a abinda ya shafi shugabanci da hukunci tsakanin mutane to sunansa hukuncin dagutu kuma hukuncin maguzanci;﴿أَفَحُكْمَ الْجَاهِلِيَّةِ يَبْغُونَ وَمَنْ أَحْسَنُ مِنَ اللَّهِ حُكْمًا لِقَوْمٍ يُوقِنُونَ٥٠﴾Ma’ana:“To yanzu hukuncin maguzanci suke bukata? Wa ya fi Allah kyawun hukunci ga mutanan da suke da yakini”. Suratul Ma’idah, aya: 50. Hakanan kuma halastawa da haramtawa hakki ne na Allah madaukakin sarki, bai halatta ga wani ya yi tarayya da shi a ciki, Allah madaukakin sarki ya ce:﴿وَلَا تَأْكُلُوا مِمَّا لَمْ يُذْكَرِ اسْمُ اللَّهِ عَلَيْهِ وَإِنَّهُ لَفِسْقٌ وَإِنَّ الشَّيَاطِينَ لَيُوحُونَ إِلَى أَوْلِيَائِهِمْ لِيُجَادِلُوكُمْ وَإِنْ أَطَعْتُمُوهُمْ إِنَّكُمْ لَمُشْرِكُونَ١٢١﴾Ma’ana:“Kuma kada ku ci daga abinda ba’a anbaci sunan Allah ba a kansa to lalle shi fasikancine, kuma lalle shaidanu hakika suna yiwa ‘yan’uwansu wahayi domin su yi jayayya da ku, kuma har idan kuka bisu to lalle ku hakika mushirikaine”. Suratul An’ama, aya ta:121. Sai Allah mai girma da daukaka ya sanya biyayya ga shaidanu da ‘yan’uwan shaidanu a halatta abinda Allah ya haramta shirka ne da shi mai girma da daukaka, kuma haka yake dukkan wanda ya bi malamai ko shuwagabanni wurin haramta abinda Allah ya halasta ko halasta abinda Allah ya haramtashi to hakika ya rikesu ababan bauta koma bayan Allah, domin fadar Allah madaukakin sarki: ﴿اتَّخَذُوا أَحْبَارَهُمْ وَرُهْبَانَهُمْ أَرْبَابًا مِنْ دُونِ اللَّهِ وَالْمَسِيحَ ابْنَ مَرْيَمَ وَمَا أُمِرُوا إِلَّا لِيَعْبُدُوا إِلَهًا وَاحِدًا لَا إِلَهَ إِلَّا هُوَ سُبْحَانَهُ عَمَّا يُشْرِكُونَ٣١﴾Ma’ana:“Sun riki malamansu da masu bauta a cikinsu wasu ababan bauta koma bayan Allah (sunkuma riki) Masihu dan Maryama, kuma ba’a umarcesu ba sai don su bautawa abin bauta guda daya, babu wani abin bauta sai shi, tsarki ya tabbata ga reshi daga barin abinda suke yi masa shirka”. Suratut Taubah, aya ta: 31. Hadisi ya zo daga Tirmizi da waninsa lalle Ma’aikin Allah ﷺ ya karanta wannan ayar ga Adiyu dan Hatim Adda’it sai ya ce: “Ya Ma’aikin Allah ba mu kasance muna bauta musuba, sai ya ce: Ashe basu kasance suna halasta abinda Allah ya haramta shi ba, sai kuma ku halastaba, kuma haramta abinda Allah ya halasta sai ku ma ku haramta ba?, sai ya ce: Eh, sai Annabi ﷺ ya ce: Wannan itace bauta musun”. Tirmizi ya ruwaito. Sai yi musu biyayya cikin halastawa da haramtawa koma bayan Allah ta kasance bauta musu kuma shirka, kuma wannan shirkace babba da take kore tauhidi, wanda shine kuma Kalmar shahada ta ((لا إله إلا الله)) take nufi, domin yana daga cikin abinda take nufi cewa lalle halastawa da kuma haramtawa hakkine na Allah madaukakin sarki shi kadai, to idan haka ya kasance ga wanda ya yi wa malamai da masu ibadah biyayya a halastawa ko haramtawa wanda yake sabawa shari’ar Allah tare da cewa su suka fi kusa ida ilimi da kuma addini, wani lokacimma kuskuran na su yana kasancewa ne ta fuskar ijtihadi wanda basu dace da gaskiyaba a ciknsa kuma suna da lada akai, to ya zaka kwatanta da wanda yake bin hukunce-hukuncen dokokin kasa wanda mutane suka kaga, wacce take kirkirace ta kafurai wadanda ba ruwansu da addini suke kawo wadannan dokoki kasashen Musulmai kuma suke hukunci da su a tsakaninsu, to bada dabara bane musulmi ya bi Allah, kuma ba da karfi bane kafiri ya kafircewa Allah saidai da abinda Allah ya kaddara. Lalle wanda wannan ya riki wannan to hakika ya riki kafirai ababan bauta koma bayan Allah, suna shar’anta musu hukunce-hukunce, suna kuma halasta musu haram, suna hukunce-hukunce tsakanin bayin Allah.***** ***** ***** Fasali Na Takwas:Shiga kungiyoyin Ilhadi da kuma kungiyoyi na jahiliyyah.1. Shiga kungiyoyi na Ilhadi (cewar babu Allah) kamar kwaminisanci da ‘yanbaruwammu da addini da jarihujja da sauransu na kungiyoyin kafirci to wannan ridda ne daga barin addinin musulunci, to idan wanda ya kasance a cikin wadannan kungiyoyi yana cewa shi musulmi ne to wannan yana daga cikin munafuncin da yake babba, domin su Musulmai suna jingina kansu ga musulunci ne a bayyane, kuma su suna tare da kafirai ne a boye, kamar yadda Allah madaukakin sarki ya ce:﴿وَإِذَا لَقُوا الَّذِينَ آمَنُوا قَالُوا آمَنَّا وَإِذَا خَلَوْا إِلَى شَيَاطِينِهِمْ قَالُوا إِنَّا مَعَكُمْ إِنَّمَا نَحْنُ مُسْتَهْزِئُونَ١٤﴾Ma’ana:“Kuma idan suka hadu da wadanda suka yi Imani sai su ce; mun yi Imani, idan kuma suka koma zuwa ga shaidanunsu sai suce; Lalle mu muna tare da ku, ai kawai mu muna musu izgili ne”. Suratul Bakarah, aya ta:14. Kuma Allah mai girma da daukaka ya ce:﴿الَّذِينَ يَتَرَبَّصُونَ بِكُمْ فَإِنْ كَانَ لَكُمْ فَتْحٌ مِنَ اللَّهِ قَالُوا أَلَمْ نَكُنْ مَعَكُمْ وَإِنْ كَانَ لِلْكَافِرِينَ نَصِيبٌ قَالُوا أَلَمْ نَسْتَحْوِذْ عَلَيْكُمْ وَنَمْنَعْكُمْ مِنَ الْمُؤْمِنِينَ فَاللَّهُ يَحْكُمُ بَيْنَكُمْ يَوْمَ الْقِيَامَةِ وَلَنْ يَجْعَلَ اللَّهُ لِلْكَافِرِينَ عَلَى الْمُؤْمِنِينَ سَبِيلًا١٤١﴾Ma’ana:“Sune wadanda suke dakonku, to idan wani budi daga Allah ya sameku sai su ce: Ashe ba mu kasance tare da ku ba?. Idan kuma ya kasance kafiraine suka sami wani kaso sai su ce (musu); Ashe ba mu yi muku bayaniba kuma muka dinga hanaku daga muminai”. Suratun Nisa’i, aya ta:141. To wadannan munafukai masu yaudara: Kowanne mutum daga cikinsu yana da fuska biyu, fuska guda yana fuskantar muminai da ita, fuska guda kuma yana komawa da ita ga ‘yan’uwan mulhidai (kafirai), kuma yana da harsuna biyu, daya daga cikinsu yana yi wa Musulmai bayanine da zahirinsa, dayan kuma yana bayyana abinda ke zuciyarsa;﴿وَإِذَا لَقُوا الَّذِينَ آمَنُوا قَالُوا آمَنَّا وَإِذَا خَلَوْا إِلَى شَيَاطِينِهِمْ قَالُوا إِنَّا مَعَكُمْ إِنَّمَا نَحْنُ مُسْتَهْزِئُونَ١٤﴾Ma’ana:“Kuma idan suka hadu da wadanda suka yi Imani sai su ce; mun yi Imani, idan kuma suka koma zuwa ga shaidanunsu sai suce; Lalle mu muna tare da ku, ai kawai mu muna musu izgili ne”. Suratul Bakarah, aya ta:14. Hakika sun kaucewa littafin Allah da Sunnar Annabinsar suna masu izgili da masu binsu da kuma wulakantar da su, suka ki su yarda da hukuncin wahayai biyu (Kur’ani da Hadisi), kawai dan alfahari da abinda ke wurinsu na ilimin da tarashi bashi da wani amfani saidai sharri da girman kai, saidai ka gansu a kullum izgili suke yi da masu ruko da karantarwar musulunci;﴿اللَّهُ يَسْتَهْزِئُ بِهِمْ وَيَمُدُّهُمْ فِي طُغْيَانِهِمْ يَعْمَهُونَ١٥﴾Ma’ana:“Allah ne yake musu izgili kuma yake kara nitsar da su cikin batansu suna fagamniya”. Suratul Bkarah, aya ta:15. Hakika Allah ya yi umarnine da haduwa da mutanan da suke muminai,﴿يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اتَّقُوا اللَّهَ وَكُونُوا مَعَ الصَّادِقِينَ١١٩﴾Ma’ana:“Ya ku wadanda suka yi Imani ku ji tsoron Allah kuma ku kasance tare da masu gaskiya”. Suratut Taubah, aya ta:119. Wadannan kungiyoyi na ilhadi (barna) kungiyoyine masu matukar barna, domin an gina sune akan barna, shi dai kwaminisanci: yana inkarin cewar akwai Allah madaukakin sarki, kuma yana yakar dukkanin shari’o’in da suka zo daga sama, wanda duk ya yarda da hankalinsa da ya rayu ba tare da akidah ingantacciya ba, kuma yake musun abubuwan da suke afili na yakini to ya kasance wanda ya yi watsi da hankalinsa. Ilmaniyyah: kuma bata yadda da wani addiniba, kawai tana dogarane akan me suka gani, ba wanda yake ce musu yi kaza, kuma babu inda suka sa gaba a wannan rayuwa saidai rayuwar dabbobi kawai?.Jarihujja: Kwai himmarsu tara dukiya ta kowacce fuska, babu maganar halas ko haram, babu tausayawa babu kuma rangwantawa ga talakawa marasashi, babban tushen arzikinsu shi ne riba wacce take yakine da Allah yakine kuma da Manzon Allah ﷺ, wacce take kuma itace take ruguje kasa da daidaikun mutane, masu tsotsar jinin al’ummar da suke talakawa, to wane mai hankali ne –balle ace wanda ke da Imani- zai so ya rayu a irin wadannan kungiyoyi ba tare da wani hankaliba ba kuma tare da addini ko manufa ingantacciya ba a rayuwarsa da yake da wata manufa da yake so ya kai ba da kuma yake so ya habbaka saboda ita. Kawai dai wadannan kungiyoyi sun yaki kasashen Musulmai alokacin da mafi yawansu suka rasa addini ingantacce, akai ta tafiya akan bata, kuma aka rayu akan me naga ana yi?.2. Shiga kungiyoyin jahiliyyah da “yan jama’ata kawai’ da bangaranci to shi ma wani kafircin ne daban, kuma riddace daga barin musulunci, domin musulunci yana kore bangaranci da duk wani tarsashin maguzanci, Allah madaukakin sarki yana cewa:﴿يَا أَيُّهَا النَّاسُ إِنَّا خَلَقْنَاكُمْ مِنْ ذَكَرٍ وَأُنْثَى وَجَعَلْنَاكُمْ شُعُوبًا وَقَبَائِلَ لِتَعَارَفُوا إِنَّ أَكْرَمَكُمْ عِنْدَ اللَّهِ أَتْقَاكُمْ إِنَّ اللَّهَ عَلِيمٌ خَبِيرٌ١٣﴾Ma’ana:“Ya ku mutane! Lalle mu mun halicceku daga namiji da mace kuma muka sanyaku dangidangi kuma kabilu kabilu domin kusan juna, lalle mafi darajarku a wurin Allah shine wanda ya fi ku tsoron (Allah)”. Suratul Hujurat, aya ta:13. Kuma Annabi ryana cewa: “Ba shi daga cikimmu duk wanda ya yi kira zuwa ga bangaranci, kuma ba shi daga cikimmu duk wanda ya yi yaki akan bangaranci, haka kuma bashi daga cikimmu duk wanda ya yi fushi akan bangaranci”. Muslim da Abudawud suka ruwaito. Kuma ﷺ ya ce: “Lalle hakika Allah ya tafiyar muku da guggubin jahiliyyah (maguzanci) da kuma alfahari da iyaye, abin sani kawai mumini mai tsoron Allah ko fajiri shakiyyi, su mutane ‘ya’yan Adamu ne, shi kuma Adamu an halicce shi ne daga wuta, babu wata falala ga balarabe akan wandaba balarabeba sai da tsoron Allah”. Abudawud da Tirmizi suka ruwaito. Wadannan kungiyoyi sun rarraba kan musulmi, kuma hakika Allah ya yi umarni da hadakai da taimakon juna akan bin Allah da tsoronsa, kuma ya hana rabuwarkai da sabani, Allah madaukakin sarki yana cewa:﴿وَاعْتَصِمُوا بِحَبْلِ اللَّهِ جَمِيعًا وَلَا تَفَرَّقُوا وَاذْكُرُوا نِعْمَتَ اللَّهِ عَلَيْكُمْ إِذْ كُنْتُمْ أَعْدَاءً فَأَلَّفَ بَيْنَ قُلُوبِكُمْ فَأَصْبَحْتُمْ بِنِعْمَتِهِ إِخْوَانًا وَكُنْتُمْ عَلَى شَفَا حُفْرَةٍ مِنَ النَّارِ فَأَنْقَذَكُمْ مِنْهَا كَذَلِكَ يُبَيِّنُ اللَّهُ لَكُمْ آيَاتِهِ لَعَلَّكُمْ تَهْتَدُونَ١٠٣﴾Ma’ana:“Ku yi riko da igiyar Allah baki daya kada ku rarraba, ku tuna ni’imar Allah da yi muku lokacin da kuka kasance makiyan juna sai ya hada zukatanku sai kuma wayi gari da ni’imarsa ‘yan’uwa”. Suratu Ali Imran, aya ta:103. Lalle Allah yana bukatarmu da mu kasance kungiya guda (tsintsiya madaurinki daya) sune kuma rundunar Allah wadanda suka rabauta, to saidai duniyar musulunci ta wayi garine bayan turawa sun yake su ta bangaran siyasa da wayewa suna bin wadannan bangarancin na; jinimmu, ko kabilanci ko kasanci, kuma aka yi Imani da hakan kai kace wata mas’alace ta ilimi tabbatacciya ko kuma wani abune tabbatacce da ba za’a iya guje masa ba. Sai ‘yan kasashen suka wayi gari suna fankama, fankama da ban mamaki wurin rayar da wadannan bangarancin wacce musulunci tuni ya kashe ta da wadatuwa da ita da kuma rayar da alamominta da alfahari da loakcin da ya gabatu akan musulunci, to shine abinda musulunci yake kiranshi da jahiliyyah (maguzanci), kuma hakika Allah ya yi ni’imarsa ga al’ummar Musulmai ta yadda ya fitar da su daga wannan jahiliyyah ya kuma kwadaitar da su akan su gode akan wannan ni’imar. Adabi’ance shine mumini kada ya ambaci wata al’ada ake tunawa da ita, ko ya yi kusa sai dai da kyama da cije baki, da motsawar tsigar jiki, to wai wanda ya yi zaman kurkuku wanda ake azabtarwa wanda kuma aka sakeshi zai yi bikin tuna ranakun da yake a daure da ake azabtar da shi ake wulakantar da shi ai saidai jijiyoyinsa suna makyarkyata. Shin maralafiyan da ya warke bayan doguwar mugunyar cuta mai tsanani wacce ya yi tunanin bankwana da duniya zai zo yana bikin ranar wannan cutar ai sai hankalinsa ya tashi launinshi ya kada. Abinda yake shi ne a sani wadannan kungiyoyin wata irin azaba ce Allah madaukakin sarki ya aikota ga dukkan wanda ya kaudakai daga bin shari’arsa, yake kullawa addinin Allah makirci, kamar yadda Allah madaukakin sarki yake cewa:﴿قُلْ هُوَ الْقَادِرُ عَلَى أَنْ يَبْعَثَ عَلَيْكُمْ عَذَابًا مِنْ فَوْقِكُمْ أَوْ مِنْ تَحْتِ أَرْجُلِكُمْ أَوْ يَلْبِسَكُمْ شِيَعًا وَيُذِيقَ بَعْضَكُمْ بَأْسَ بَعْضٍ ٦٥﴾Ma’ana:“Ka ce: Shi mai ikone akan ya tayar muku da azaba daga samanku ko kuma daga kasan kafafuwanku ko kuma ya sanyaku kungiyoyi kuma sai dandana azabar sashinku ga sashi”. Suratul An’am, aya ta:65., kuma Ma’aikin Allah ﷺ yana cewa: “Kuma dukkanin wadanda shugabanninsu ba su hukunci da littafin Allah ba to sai Allah ya sanya azabar su a tsakaninsu”. Ibnu Majah ya ruwaito shi. Lalle makalkalewa wadannan kungiyoyi yana haifar da kin karbar gaskiya wacce take tare da wasu, kamar yadda hakan shine halin Yahudawa, Allah madukakin sarki yana cewa dangane da su:﴿وَإِذَا قِيلَ لَهُمْ آمِنُوا بِمَا أَنْزَلَ اللَّهُ قَالُوا نُؤْمِنُ بِمَا أُنْزِلَ عَلَيْنَا وَيَكْفُرُونَ بِمَا وَرَاءَهُ وَهُوَ الْحَقُّ مُصَدِّقًا لِمَا مَعَهُمْ ٩١﴾Ma’ana:“Kuma idan akace da su; Ku yi Imani da abinda Allah ya saukar, sai su ce; Mu za mu yi imanine da abinda aka saukar mana, sai su dinga kafircewa abinda ba shi ba wanda yake shine gaskiya mai gasgata abindake tare da su”. Suratul Bakarah, aya ta: 91. Kuma kamar haka yake halin maguzawa wadanda suka ki karbar gaskiyar da Manzon Allah ﷺ ya zo musu da ita, kawai don makalkalewa abinda iyayansu suke a kai;﴿وَإِذَا قِيلَ لَهُمُ اتَّبِعُوا مَا أَنْزَلَ اللَّهُ قَالُوا بَلْ نَتَّبِعُ مَا أَلْفَيْنَا عَلَيْهِ آبَاءَنَا أَوَلَوْ كَانَ آبَاؤُهُمْ لَا يَعْقِلُونَ شَيْئًا وَلَا يَهْتَدُونَ١٧٠﴾Ma’ana:“Kuma idan kace da su; Ku bi abinda Allah ya saukar, sai su ce; A’a, Za mu bi abinda muka samu iyayammu akai”. Suratul Bakarah, aya ta:170. Masu irin wadannan kungiyoyin abinda suke nufi shi ne su sanya wadannan kungiyoyin makwafin musulunci wanda Allah ya yi ni’imarsa da shi akan mutane baki daya. Fasali Na Tara:Mahanga ta ci gaba a rayuwa. Akwai mahanga biyu a rayuwa; mahanga ya za’a rayu da kuma mahanga ingantacciya, kuma kowacce mahanga daga cikin wadannan mahangan suna da tasirinsu:(1) Mahanga ta ya za’a rayu-(Ma’anarta):Shi ne tunanin mutum ya kasance ya takaitune akan abubuwan jindadi na nan duniya, kuma aikinsa ya kasance akan wannan tsarin, tunaninsa ba zai wuce wannan ba, ballantana ya ga me wannan din zai haifar, ba ma zai yi aiki domin hakan ba, ba kuma zai himmatu da hakan ba, shi bai san Allah ya sanya wannan rayuwa ta duniya ta kasance shukace ga rayuwar lahira ba, sai Allah ya sanya duniya wurine na aiki, ya kuma sanya lahira wurine na sakamako, to dukkan wanda ya yi amfani da duniyarsa ta hanyar aiki maikyau to wannan ya rabauta duniya da lahira, duk kuma wanda ya tozartar da rayuwarsa ta duniya to ya wulakantar da lahirarsa; ﴿ خَسِرَ الدُّنْيَا وَالْآخِرَةَ ذَلِكَ هُوَ الْخُسْرَانُ الْمُبِينُ١١﴾Ma’ana:“Ya yi asarar duniya da lahira, yin haka kuwa shine bayyananniyar asara”. Suratul Hajj, aya ta:11. To Allah madaukakin sarki bai halicci wannan duniya domin wasa ba, a’a ya halicceta ne domin wata hikima mai girman gaske, Allah madaukakin sarki na cewa:﴿الَّذِي خَلَقَ الْمَوْتَ وَالْحَيَاةَ لِيَبْلُوَكُمْ أَيُّكُمْ أَحْسَنُ عَمَلًا وَهُوَ الْعَزِيزُ الْغَفُورُ٢﴾Ma’ana:“Shi ne wanda ya halicci mutuwa da rayuwa domin ya jarrabaku wa ye a cikinku ya fi kyakkyawan aiki”. Suratul Mulk, aya ta:2., kuma Allah madaukakin sarki ya ce:﴿إِنَّا جَعَلْنَا مَا عَلَى الْأَرْضِ زِينَةً لَهَا لِنَبْلُوَهُمْ أَيُّهُمْ أَحْسَنُ عَمَلًا٧﴾Ma’ana:“Lalle mu munsa dukkanin abindake bayan kasa ya zama adone gareta, domin mu jarrabaku waye daga cikin ya fi kyawun aiki”?. Suratul Kahf, aya ta:7. Allah madaukakin sarki ya samar da kayan jin dadi a wannan rayuwar ta yanzu yanzu, ya kuma samar da kayan ado na zahiri kamar dukiya da ‘ya’ya da matsayi ga iko da sauran kayan jindadin da ba wanda ya sansu sai Allah madaukakin sarki shi kadai. Akwai daga cikin mutane akwai wandanda – kuma su suka fi yawa- suka takaita hangensu akan abinda ya shafi zahirin duniyar da kuma abubuwan da suke fitina ne na duniyar, ya jiyar da kansa dadinta bai lura da sirrin nata ba, kawai sai ya shagaltu da nemanta da kuma tarata da wadaka da ita, bai yi aiki akan abinda zai zo bayanta ba, kai ya yi musun cewa ma akwai wata rayuwa ta daban bayan rayuwar duniya, kamar yadda Allah madaukakin sarki yace:﴿وَقَالُوا إِنْ هِيَ إِلَّا حَيَاتُنَا الدُّنْيَا وَمَا نَحْنُ بِمَبْعُوثِينَ٢٩﴾Ma’ana:“Kuma suka ce: Ita wannan bakomai bace illa kawai rayuwar duniya mu kuma ba wadanda za’a taba tashimmu bane”. Suratul An’am, aya ta:29. Hakika Allah madaukakin sarki ya yi alkawari narkon azaba ga dukkanin wanda wannan itace mahangarsa a rayuwa, Allah madaukakin sarki yana cewa:﴿إِنَّ الَّذِينَ لَا يَرْجُونَ لِقَاءَنَا وَرَضُوا بِالْحَيَاةِ الدُّنْيَا وَاطْمَأَنُّوا بِهَا وَالَّذِينَ هُمْ عَنْ آيَاتِنَا غَافِلُونَ٧ أُولَئِكَ مَأْوَاهُمُ النَّارُ بِمَا كَانُوا يَكْسِبُونَ٨﴾Ma’ana:“Lalle dukkanin wadanda ba sa kaunar haduwa da mu kuma suka yarda da rayuwar duniya kuma suka natsu da ita, kuma wadanda suke dangane da ayoyimmu suna gafalallu.* Wadannan makomarsu itace wuta saboda abinda suka kasance suna aikatawa”. Suratu Yunus, aya ta:7-8. Kuma Allah madaukakin sarki ya ce: ﴿مَنْ كَانَ يُرِيدُ الْحَيَاةَ الدُّنْيَا وَزِينَتَهَا نُوَفِّ إِلَيْهِمْ أَعْمَالَهُمْ فِيهَا وَهُمْ فِيهَا لَا يُبْخَسُونَ١٥ أُولَئِكَ الَّذِينَ لَيْسَ لَهُمْ فِي الْآخِرَةِ إِلَّا النَّارُ وَحَبِطَ مَا صَنَعُوا فِيهَا وَبَاطِلٌ مَا كَانُوا يَعْمَلُونَ١٦﴾Ma’ana:“Duk wanda ya kasance yana son rayuwar duniya da kuma adonta to za mu cika musu (ladan) ayyukansu a cikinta, su kuma a cikinta ba za’a taba ragemusuba. Wadannan ba su da komai a lahira saidai wuta, kuma duk abinda suka yi a cikinta (ita duniyar) ya baci, kuma bataccene duk abinda suka kasance suna aikatawa”. Suratu Hud, aya ta: 15-16. Wannan alkawari na narkon azaba ya shafi masu irin wannan tunanin, shin suna cikin wadanda suke yin aiki domin lahira amma suke neman duniya da shi, kamar munafukai wadanda suke nuna ayyukansu koko ma sun kasance cikin kafirai wadanda basa yi Imani da cewar za’a tashi haka kuma basa yin Imani da hisabi kamar maguzawan jahiliyyah (Ahlul jahiliyyah) da kungiyoyi masu rushe al’umma kamar ‘yan jari-hujja da kwaminisanci da wadanda ba ruwansu da addini da wadanda basu yarda da Allah ba (masu Ilhadi), wadannan basu san kimar rayuwaba kuma yadda suke kallon rayuwar duniya bai huce irin kallon da dabbobi suke mat aba, kai! Ai sun ma fi dabbobi bacewa, domin su sun yi watsi da tunaninsu suka tafiyar da ikonsu suka kuma wulakantar da lokutansu cikin abida ba zai saurar musuba su kuma ba za su saura dominshi ba, kuma basu yi aiki domin makomarsu ba wacce take sauraransu kuma babu wata makawa sai sun koma. Dabbobi ba su da makoma da suke sauraranta, kuma basu da hankula da suke tunani da su sabanin wadannan, saboda haka Allah madaukakin sarki yake cewa dangane da su:﴿أَمْ تَحْسَبُ أَنَّ أَكْثَرَهُمْ يَسْمَعُونَ أَوْ يَعْقِلُونَ إِنْ هُمْ إِلَّا كَالْأَنْعَامِ بَلْ هُمْ أَضَلُّ سَبِيلًا٤٤﴾Ma’ana:“Koko kana tsammanin cewa lalle mafi yawansu suna sauraro ko suna hankalta, ba komai suke ba sai kamar dabbobi, a’a su sun fi (dabbobi) bacewa”. Suratul Furkan, aya ta:44. Hakika Allah ya siffanta masu irin wannan hangen da rashin ilimi, Allah madaukakin sarki yana cewa:﴿وَعْدَ اللَّهِ لَا يُخْلِفُ اللَّهُ وَعْدَهُ وَلَكِنَّ أَكْثَرَ النَّاسِ لَا يَعْلَمُونَ٦ يَعْلَمُونَ ظَاهِرًا مِنَ الْحَيَاةِ الدُّنْيَا وَهُمْ عَنِ الْآخِرَةِ هُمْ غَافِلُونَ٧﴾Ma’ana:“Saidai mafi yawan mutane ba su sani ba. Suna sanin zahiri na rayuwar duniya, kuma su dangane da lahira to su gafalallu ne”. Suratu Rum, aya ta:6-7. To su koda sun kasance suna da kwarewa ta kirkire kirkire da kuma kerekere to su jahilaine ba sa cancantar a siffanta su da ilimi, domin iliminsu bai wuce zahirin rayuwar duniyaba, wannanko ilimine da yake tauyayye, masu shi ba sa cancantar a siffantasu da wannan siffa mai daraja, sai ace; malamai, ai ana fadin wannan ne (malamai) ga wadanda suka san Allah kuma suke tsoronsa, kamar yadda Allah madaukakin sarki yake cewa:﴿وَمِنَ النَّاسِ وَالدَّوَابِّ وَالْأَنْعَامِ مُخْتَلِفٌ أَلْوَانُهُ كَذَلِكَ إِنَّمَا يَخْشَى اللَّهَ مِنْ عِبَادِهِ الْعُلَمَاءُ إِنَّ اللَّهَ عَزِيزٌ غَفُورٌ٢٨﴾Ma’ana:“Abin sani kawai wadaida suke jin tsoron Allah sune malamai”. Suratu Fatir, aya ta:28. Yana daga cikin hange na rayuwar duniya kadai irin irin abinda Allah madaukakin sarki ya ambata a kissar Karuna, da irin abinda Allah ya bashi na taskokin arziki:﴿فَخَرَجَ عَلَى قَوْمِهِ فِي زِينَتِهِ قَالَ الَّذِينَ يُرِيدُونَ الْحَيَاةَ الدُّنْيَا يَا لَيْتَ لَنَا مِثْلَ مَا أُوتِيَ قَارُونُ إِنَّهُ لَذُو حَظٍّ عَظِيمٍ٧٩﴾Ma’ana:“To, sai ya fita ga mutanansa a cikin adonsa, sai wadanda suke son rayuwar duniya suka ce; Inama ace muna da irin abinda aka baiwa Karuna, lalle shi hakika yana da rabo maigirma”. Suratul Kasas, aya ta:79. Sai suka yi burin irin abinda yake da shi, suka so kuma suka siffantashi da rabo mai girma, wannan a yadda suke hangen samu. Wannan kuwa haka yake a yau akasashen da suke na kafirai, da kuma irin abinda suke da shi na ci gaban kere-kere da tattalin arziki, domin masu raunin Imani daga cikin Musulmai suna musu kallo na birgewa, ba tare da sun ga irin abinda suke da shi na kafirci ba da kuma abinda yake jiransu na mummunar makoma, sai irin wannan makahon hangen ya sa su dinga girmama kafirai da karrama su azukatansu, da kuma kamanceceniya da su a dabi’unsu da kuma munanan al’adunsu, ba su yi koyi da sub a wurin kokari ba da kuma tattalin karfi da abubuwa masu amfani na kirkire-kirkire da kuma kere-kere.(b) Hange Na Biyu: Da Za’a Yiwa Rayuwa (Hange mekyau).Itace kuwa mutum ya yi tunanin abindake cikin wannan rayuwa na dukiyane ko karfi to tsanine da za’a yi amfani da shi domin samun lahira, ita duniya a hakikanin yadda take ba’a zarginta don karankanta, kawaidai za’a yi yabo ne ko zargi ga aikin da bawa ya yi a cikinta, saboda haka ita wata gadace wacce ake ketarawa domin isa lahira, acikinta kuma ake samun guzurin aljanna, mafi kyawun rayuwa da ‘yan aljanna suke samu to fa ya samune saboda abinda suka shuka a duniya, ita duniya gidane na jihadi da sallah da azumi da ciyarwa domin daukaka addinin Allah, kuma wurine da ake rige-rige zuwa ga aikata ayyuka na alheri, Allah madaukakin sarki yana cewa ‘yan aljannah:﴿كُلُوا وَاشْرَبُوا هَنِيئًا بِمَا أَسْلَفْتُمْ فِي الْأَيَّامِ الْخَالِيَةِ٢٤﴾Ma’ana: “Ku ci kuma ku sha cikin kwanciyar hankali saboda abinda kuka gabatar a kwanukan da suka gabata”. Suratul Hakkah, aya ta: 24. Wato duniya. **** **** **** Fasali Na Goma:Layu da kuma tofi.1. Tofetofe, jam’ine na “tofi”, wani abune da ake daurawa ayayyaku, kamar; zazzabi, bugun aljan, da wanin haka na nau’ukan ayayyaku, kuma suna kiranta da ‘Tsari’, kuma shi tofi nau’i biyu ne:Nau’i Na Farko: Wanda yake ya kasance kwata-kwata babu shirka a cikinsa, kamar a karantawa mara lafiya wani abu na Alkur’ani, ko kuma a nema masa tsari da sunayan Allah da kuma siffofinsa, to wannan halasne, domin tabbas Ma’aikin Allah ﷺ ya yi tofi kuma ya yi umarni da a yi kuma ya halatta ta. An karbo daga Awf dan Malik, ya ce: “Mun kasance muna yin tofi azamanin jahiliyyah, sai mukace ya Ma’aikin Allah; ya ka gani akan hakan? Sa ya ce; “Ku karantamin addu’o’in na ku, babu laifi ga dukkanin tofin da babu shirka acikinsa”. Muslim sa Abudawuda suka ruwaito. Sayudi yace: Hakika malamai sun yi ijma’i, akanhalaccin tofi alokacin da sharudda uku suka cika: Ya kasance da zancan Allah ne ko sunayansa da siffofinsa. Kuma ya kasance da harshen larabci, kuma abinda ake gane ma’anarsa. Kuma ya kudurce cewa shi tofin bashi da wani tasiri a karan kansa, saida kaddarawar Allah. Yadda kuma ake yi shi ne; Ya karanta kuma ya tofawa mara lafiyan, ko ya karanta a ruwa sai mara lafiyan ya sha, kamar yadda ya zo a hadisin Sabitu dan Kais, lalle Ma’aikin Allah ﷺ ya debi kasa daga But’han, sai ya sanyata a akushi, sannan sai ya yi tofi akai sai ya zuba masa”. Abudawuda ne ya ruwaito.Nau’i Na Biyu: Wanda yake da shirka, shi ne tofin da ake neman temako ga waninin Allah, kamar kiran wanin Allah da neman agajin wanin Allah da kuma neman tsarin wanin Allah, kamar yin tofi da sunayan aljanu ko sunayan mala’iku (ko As’habul Kahf) ko Annabawa da salhan bayi, to wannan kiran wanin Allah ne kuma wannan shirkace babba, ko kuma ya kasance bada harshen larabciba ko kuma da abinda ba’a san ma’anarshi ba, domin ana gudun kada kafirci ya shiga ko shirka kuma ba’a sani ba, wannan nau’i na tofi an hana shi.Layu:Itakuma jam’ice ta laya, itace kuwa: Abinda ake ratayawa a wuyan yara domin kauda kabbun-baka, wani lokacinmma manya suna ratayawa maza da mata, tana da nau’i biyu:Nau’i Na Farko: wacce ta kasance da Kur’ani, kamar a rubuta ayoyin Alkur’ani ko kuma wasu daga cikin sunayan Allah da siffofinsa sai a rataya domin neman waraka da ita, to wannan nau’i malamai sun karawa juna sani akan sanya shi maganganu biyu ne:Magana Ta Farko: Ya halatta, wannanko shine maganar Abdullahi dan Amru dan As, kuma wannan shine zahirin abinda aka ruwaito daga nana Aisha, da shi ne kuma Abu Ja’far bakir ya yi fatawa da Ahmad dan Hanbali a wata riwaya daga gareshi, sai suka dauki hadisin da y azo ya hana sanya layu akan layun da acikinsu akwai shirka.Magana Ta Biyu: Hana hakan, wannan kuma shine maganar Abdullahi dan Mas’ud da Dan Abbas, wannan kuma shine zahirin maganar Huzaifah da Ukubah da Amir da Dan Ukaim, itace kuma fatawar jama’a masu yawa daga cikin Tabi’ai daga cikin akwai almajiran Abdullahi dan Mas’ud, da kuma Ahmad a wata ruwayar da kaso maiyawa na almajiransa suka zaba, kuma da wannanne ‘yan baya suka tabbata, suka kafa hujja kuma da abinda Abdullahi dan Mas’ud t ya ruwaito, ya ce: Na ji Ma’aikin Allah ﷺ yana cewa; “Lalle tofi da layu da tiwala shirka ne”. Abudawud ya ruwaito shi. Tiwala wani abune da suke sanya shi suke kuma riya cewar yana karawa mace soyayya a wurin mijinta haka kuma miji a wurin matarsa.Wannan (Magana ta biyun) kuwa ita ce ingantacciya, ta fuskoki uku;(1) Yadda hana sanya laya ya zama gamamman hani ne, kuma babu wani abu da ya kebanci wannan gamewar.(2) Toshe kafa, domin idan aka bude sanyata to zai kai ga sanya wacce bata halattaba.(3) Cewar idan ya rataya wani abu na Alkur’ani, to ko ba makawa sai wanda ya rataya din ya wulakantar da shi ta hanyar shiga wurin bayan-gida da shi da ma yin tsarki da shi, da makamantan haka.Nau’i Na Biyu Na Laya: wacce ake ratayawa abu wacce take ba Alkur’ani ba ne, kamar kwabo ko kasha ko wuri ko takalmi ko kuma kusa ko kuma sunayan shaidanu da aljanu da dalsami, to wannan haramunne yanke kuma yana daga cikin shirka, domin ratayuwane ga wanin Allah madaukakin sarki da sunayansa da kuma siffofinsa da ayoyinsa, ya zo a hadisi: “Duk wanda ya rataya wani abu to za’a dorashi ga wannan abun”. Tirmizi da Ahmad suka ruwaito. Wato Allah zai mayar da tawakkalinsa ga wannan abun da ya rataya, duk wanda ya dogara ga Allah ya koma ga Allah, ya kuma fawwala al’amuransa ga Allah to Allah ya isar masa, kuma duk abinda ya yi mishi nisa to zai zo masa kusa, kuma dukkan abinda ya tsananta a gareshi to zai yi masa sauki, wanda kuma ya dogara ga wanin Allah cikin halittun Allah da layu da wasu tsubbatai da kabarurruka to Allah zai mayar da tawakkalinsa ga wannan abun da ba zai iya magance masa komai ba, ba shi da mallakar cuta kuma ba shi da mallakar amfani, sai ya yi asarar akidarsa kuma alakarshi da Ubangijinsa ta yanke, kuma Allah ya tabar da shi. Abinda ya ke wajibi akan dukkan musulmi shine ya kiyaye akidarsa daga dukkan abinda zai bata masa ita, koma ya lalata masa ita, kada ya sha magungunan da basu halatta ba, kuma kada ya je wurin masu tatsuniyoyi da masu rufa ido domin neman magani a wurinsu, domin su za su sawa zuciyarsa da akidarsa cutane, kuma dukkan wanda ya dogara ga Allah to Allah ya isar masa. Wasu daga cikin mutane suna rataya wadannan abubuwanne akaran kansa, ba wai don yana fama da rashin lafiya ba, a’a kawaidai yana fama da rashin lafiyar rudewane shine kuma; tsoron kambun-baka da hassada, ko ya rataya a motarsa ko a dabbarsa ko a kofar gidansa koma a shagonsa, duk wadannan abubuwa yana nuna raunin Imani kuma shine babban rashin lafiyar da yake damunsu, wanda ya zama wajibi a magance shi ta hanyar sanin tauhidi da kuma kyakkyawar akidah. **** ***** ***** Fasali Na Goma sha daya:Rantsuwa da wanin Allah da kuma tawassuli da neman taimako ga wani mahaluki da ba Allah ba.(1) Rantsuwa Da Wanin Allah:Rantsuwa: Itace karfafa hukunci da ambaton wanda ake girmamawa akebance. Girmamawa kuwa hakkin Allah ne madaukakin sarki, saboda haka bai halatta a rantse da wanin Allah, hakika malamai sun yi ijima’i kana ita rantsuwa ba ta kasancewa saidai da Allah ko da sunayansa da siffofinsa, kuma bakinsu ya zo daya akan hana rantsuwa da wanin Allah. Rantsuwa da wanin Allah shirka ne, saboda abinda Abdullahi dan Umar ya ruwaito –Allah ya kara musu yarda- lalle Ma’aikin Allah ﷺ ya ce: “Duk wanda ya rantse da wanin Allah to hakika ya kafirta ko kuma ya yi shirka”. Bukhari da Muslim suka ruwaito. Wannan ko shirkace karama, saidai idan wanda aka rantse da shi wanda ake girmamawane a wurin wanda ya yi rantsuwar har ta kai ga bauta masa, to wannan shirkace babba, wannanko shine halin da ake ciki a yau wurin masu bautar kabari, domin su suna tsoron wadanda suke girmamawa cikin wadanda aka binne sama da yadda suke tsoron Allah ko suke girmama Allah, tayadda idan aka nemi wani daga cikinsu da ya rantse da waliyyin da yake girmamawa ba zai taba rantsewa da shi ba saidai idan yana da gaskiya, amma kuwa inda za’a nemeshi ya rantse da Allah tuni zai rantse da shi kodako karya yake yi. Rantsuwa girmamawace ga wanda aka rantse da shi, kuma ba ta tabbata ga kowa sai ga Allah, kuma yana zama wajibi girmama rantsuwa da Allah, kada mutum ya yawaita rantsuwa, Allah madaukakin sarki yana cewa:﴿وَلَا تُطِعْ كُلَّ حَلَّافٍ مَهِينٍ١٠﴾Ma’ana: “Kuma kada ka bi dukkan mai yawan rantsuwa wulakantacce”. Suratul Kalam, aya ta:10, kuma Allah madaukakin sarki yana cewa:﴿ وَاحْفَظُوا أَيْمَانَكُمْ ٨٩﴾Ma’ana:“Kuma ku kiyaye rantse-rantsenku”. Suratul Ma’idah, aya ta:89. Wato kada ku rantse sai lokacin bukatar rantsuwar kuma akan gaskiya da kyautatawa, domin yawaita rantsuwa ko kuma karya a rantsuwar suna nunine akan wasa da Allah da rashin girmama shi, wannanko yana kore cikar tauhidi, ya zo a hadisi lalle Ma’aikin Allah ﷺ ya ce: “Mutane uku Allah ba zai yi Magana da su ba, kuma ba zai tsarkake su ba, kuma suna da azaba mai radadi”. Bukhari da Muslim suka ruwaito shi, ya kuma zo a cikinsa: “Da mutumin da ya sansa Allah hajarsa, ba ya saya sai ya rantse da shi (Allah) ba kuma ya sayarwa sai ya rantse da shi”. Tabarani ne ya ruwaito shi. Hakika tsananin alkawarin narkon azaba ya tabbata akan yawan rantsuwa abinda yake nuni akan cewa hakan haramun ne, domin girmama sunan Allah madaukakin sarki da kuma girmamashi shi Allah madaukakin sarki, haka nan kuma yana haramta rantsewa da Allah akan karya, rantsuwar da take jefa me ita cikin laifi sannan kuma ta jefashi a wuta, hakika Allah madaukakin sarki ya siffanta munafukai da cewar su suna rantsewa akan karya kuma suna sane. Adunkule na bayanan da suka ganata:1. Haramcin rantsuwa da wanin Allah madaukakin sarki, kamar rantsewa da amana ko da Ka’abah ko kuma da Annabi domin girmansa, kuma duk wannan shirka ne.2. Haramcin rantsewa da Allah akan karya da gangan, kuma wannan rantsuwar tana halakarwa.3. Haramcin yawan rantsewa da Allah ko ya kasance yana da gaskiya, idan babu bukatar hakan, domin hakan wasane da Allah mai girma da daukaka.4. Halascin rantsewa da Allah akan gaskiya idan bukatar hakan ta taso.(b) Tawassali: Kama Kafa Da Halittar Allah Zuwa Ga Allah (madaukakin sarki):Tawassali: shine neman kusanci zuwaga wani abu da son kaiwa ga reshi, ita kuma ‘Wasilah’ kusanci kenan. Allah madaukakin sarki yana cewa: ﴿ وَابْتَغُوا إِلَيْهِ الْوَسِيلَةَ َ٣٥﴾Ma’ana:“Ku nemi kusanci zuwa ga reshi”. Suratul Ma’idah, aya ta:35. Wato kusanci ga reshi maigirma da daukaka ta hanyar yi masa biyayya da kuma bin abinda ya yarda da shi.Tawassali (Kamunkafa) ya kasu kashi biyu:Kashi Na Farko: Shar’an taccan tawassali, shi kuma yana da nau’uka:Nau’i Na Farko: Neman kusanci ga Allah madaukakin sarki da sunayansa da kuma siffofinsa, kamar yadda Allah madaukakin sarki ya yi umarni da hakan a fadarsa:﴿وَلِلَّهِ الْأَسْمَاءُ الْحُسْنَى فَادْعُوهُ بِهَا وَذَرُوا الَّذِينَ يُلْحِدُونَ فِي أَسْمَائِهِ سَيُجْزَوْنَ مَا كَانُوا يَعْمَلُونَ١٨٠﴾Ma’ana:“Kuma Allah yana da sunaye kyawawa ku rokeshi da su, kuma ku kyale wadannan da suke karkatar da sunayansa, da sannu za’a sakanka musu da abinda suka kasance suna aikatawa”. Suratul A’araf, aya ta:180.Nau’i Na Biyu: Neman kusanci ga Allah madaukakin sarki da yin Imani da kuma kyawawan ayyuka wacce wanda yake neman kusanci ya aikata, kamar yadda Allah madaukakin sarki ya fada dangane da masu Imani:﴿رَبَّنَا إِنَّنَا سَمِعْنَا مُنَادِيًا يُنَادِي لِلْإِيمَانِ أَنْ آمِنُوا بِرَبِّكُمْ فَآمَنَّا رَبَّنَا فَاغْفِرْ لَنَا ذُنُوبَنَا وَكَفِّرْ عَنَّا سَيِّئَاتِنَا وَتَوَفَّنَا مَعَ الْأَبْرَارِ١٩٣﴾Ma’ana: “(Ya) Ubangijimmu! Lalle mu mun ji me kira yana kira ga Imani akan ku yi Imani da Ubangijinku kuma mun yi Imani, (Ya) Ubangijimmu to ka gafarta mana zunubammu kuma ka kankare mana munanan ayyukammu kuma ka dauki rayuwarmu tare da mutanan kwarai”. Suratu Ali Imrana, aya ta:193. Kuma kamar yadda yake a hadisin mutanan uku da dutse ya fado ya rufe musu kofar kogwansu, ba su sami damar fita ba, sai suka nemi kusanci ga Allah da kyawawan ayyukansu, sai Allah ya yaye musu bakin cikin da suke ciki sai kawai suka fito suna ta tafiyarsu. Nau’i Na Uku: Neman kusanci ga Allah madaukakin sarki ta hanyar Tauhidi (kadaitashi da bauta) kamar yadda Annabi Yunusa u ya yi:﴿ فَنَادَى فِي الظُّلُمَاتِ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا أَنْتَ سُبْحَانَكَ إِنِّي كُنْتُ مِنَ الظَّالِمِينَ٨٧﴾Ma’ana:“Sai ya yi kira a cikin duffai cewa; Babu abinda bautawa da cancanta sai kai, tsarki ya tabbata a gareka”. Suratul Anbiya’i, aya ta:87.Nau’i Na Hudu: Neman kusanci ga Allah ta hanyar bayyanar da rauni da kuma damuwa da bukata ga Allah madaukakin sarki, kamar yadda Annabi Ayyuba uya yi:﴿ أَنِّي مَسَّنِيَ الضُّرُّ وَأَنْتَ أَرْحَمُ الرَّاحِمِينَ٨٣﴾Ma’ana:“Lalle ni cuta ta samini kuma kaine mafi jinkan masu jinkai”. Suratul Anbiya’i, aya ta:83.Nau’i Na Baiyar: Neman kusanci ga Allah ta hanyar addu’ar salihan bayi wadanda ke raye, kuma wannan kamar yadda Sahabbai idan sun shiga fari sais u nema daga Annabi ﷺ da ya roka musu Allah, bayan ya koma ga Allah kuma sai su nemi baffansa Abbas t sai ya yi musu addu’ar.Nau’i Na Shida: Neman kusanci ga Allah ta hanyar furuci da zunubi, kamar:﴿قَالَ رَبِّ إِنِّي ظَلَمْتُ نَفْسِي فَاغْفِرْ لِي فَغَفَرَ لَهُ إِنَّهُ هُوَ الْغَفُورُ الرَّحِيمُ١٦﴾Ma’ana:“Yace; (Ya) Ubangiji lalle ni na zalinci kaina to ka gafarta mini”. Suratul Kasaa, aya ta:16.Kashi Na Biyu: Neman kusancin da bai shar’anta ba. Wannan ko shine neman kusanci ga Allah ta hanyar neman addu’a da ceto daga wadan sun mutu, da kuma tawassuli da matsayin Annabi ﷺ da tawassuli da zatin wadanda Allah ya halitta ko da darajarsu, bayani akan haka ga shi:1. Neman addu’a daga matattu bai halatta ba. Domin shi mamaci baida ikon yin addu’a, kamar yadda yake da ikon alokacin da yake raye, kuma neman ceto daga matattu bai halattaba, domin Umar dan Khaddab da Mu’awiyah dan Abu Sufyan da duk wadanda suke tare da su cikin Sahabbai da wadanda suka bi su da kyautatawa lokacin da fari (rashin ruwa) ya tsananta sun nemi addu’ane da kuma kamun kafa da ceto daga wadanda suke raye, kamar Abbas, da Yazidu dan Aswad, ba su nemi kamun kafa ba da ceto da addu’ar neman ruwan sama daga Annabi ﷺ ba, ba su yi a gaban kabarinsaba ba su yi kuma a gaban waninsaba, sun koma wurin wani ne kamar Abbas da Yazidu, kuma Umar t ya ce: “Ya Allah Ubangiji mun kasance muna neman kusanci zuwa gareka da (addu’ar) Annabinka sai ka shayar da mu, to lelle mu muna neman kusanci zuwa ga reka da (addu’ar) baffan Annabimmu (Ya) Allah ka shayar da mu”. Sai suka sanya wannan zama madadin wancan, alokacin da ya wahala da su nemi kusanci da shi da hanya shar’antacciya wacce suka kasance suna aikatawa. Hakika ya kasance abu ne me yiwuwa su je kabarinsa su nemi kusanci da shi inda hakan ya halatta, to yadda suka bar hakan ya nuna rashin yin tawassuli da wadanda suka rasu, ba’a neman addu’arsu kuma ba’a neman cetonsu, inda ace neman addu’arsa da kuma neman ceto da shi a lokacin yana raye da kuma bayan ya rasu duk dayane da ba su ki zuwa wurinsa ba, suka je wurin wand aba shi ba wanda kuma bai kaishi daraja ba.2. Tawassuli da matsayin Annabi rko da matsayin wani wanda ba shi ba to bai halattaba. Hadisin da yake cewa: “Idan za ku roki Allah to ku roke shi da matsayina, domin matsayi na a wurin Allah mai girma ne”. Kagaggen hadisine, baya cikin wani littafi daga cikin littattafan al’ummar musulmi da suke dogaro da su, kuma babu wani malami daga cikin malaman hadisi da ya ambace shi, to ko tunda dalili akan haka bai inganta ba to bai halatta a yi hakan ba, domin ita ibada ba ta tabbata saida dalili ingantacce kuma fayyatacce.3. Tawassuli (Kamun kafa) da zatin halittun bai halatta ba. Domin idan (Ba) ta kasance ta rantsuwace to ya zama rantsema Allah da wani, idan kuwa rantsewa halitta da halitta bai halattaba kuma hakamma shirkane kamar yadda yake a hadisin, ko kake ganin rantsewa Allah mahalicci (wanda ya daukaka) da halitta, idan kuwa (Ba) ta kasance ta sababiyyace, to Allah madaukakin sarki bai sanya roko da halittarsa shi ne sababin karbar addu’a ba, kuma bai shar’anta hakan ga bayinsa ba.4. Tawassuli (Kamun kafa) da matsayin wanda aka ahilitta bai halastaba, saboda abubuwa biyu:Na farko: Lalle shi Allah madaukakin sarki, babu hakkin wani da ya wajaba akansa, shi ne dai mai girma da daukaka yake falalarsa ga wani cikin halittarsa, kamar yadda Shi mai girma da daukaka yake cewa:﴿ وَكَانَ حَقًّا عَلَيْنَا نَصْرُ الْمُؤْمِنِينَ٤٧﴾Ma’ana:“Kuma ya kasane hakkine (da muka) dorawa kammu taimakon muminai”. Suratur Rum, aya ta:47. To kasancewar wanda ya yi biyayya ga Allah yana cancantar sakamako to hakan cancantar falalace da kuma ni’ima, ba wai cancanta ba ce makwafi abinda ya yi, kamar yadda halitta yake cancanta daga wurin halitta.Na biyu: Lalle shi wannan hakki wanda Allah madaukakin sarki ya yi falalarsa ga bawansa hakkine wanda yake kebantacce gareshi kadai, ba wani da yake da alaka da shi, to idan wanda ba shi yake da shi ba ya yi kamun kafa da shi to ya kasance wanda ya yi kamun kafa da wani abu can da ba shi da alaka da shi, wannan ko ba zai amfana mai komai ba. Amma hadisin da yake cewa: “Ina rokonka da hakkin masu tambaya”. To hadisine da bai tabbata ba, domin a isnadin hadisin akwai Adiyyatul Awfi, kuma da’ifine bakin malamai ya hadun akan da’ifancinshi, kamar yadda wasu daga cikin malaman hadisi suka fada. To ko abinda ya kasance haka ai ba’a faka hujja da shi a irin wannan babbar mas’ala da ta shafi al’amuran akidah, sannan kuma babu wani bayani a cikinsa na kamun kafa da matsayin wani mutum da aka ambata, kawai abinda ke ciki kamun kafa da hakkin (matsayin) masu roko bakidaya, kuma hakkin masu roko (da Allah ya dorawa kansa) shi ne ya amsa musu kamar yadda Allah ya yi alkawarin hakan, wanda yake hakkine da ya dorawa kansa babu wani mutum da ya dora masa, kenan ya zama kamun kafane da alkawarinsa na gaskiya ba da wani hakki bane na wanda aka halitta.(c) Hukuncin Neman Taimako da Neman agaji daga wanda aka halitta.Neman Taimako: Shi ne neman taimakawa da sa hannu a wani al’amari.Neman Agaji: Shi ne neman agazawa da gusar da tsanani. Neman Taimako da Neman agaji daga wanda aka halitta yana da nau’uka biyu:Nau’i Na Farko:Neman taimako da neman agaji daga wanda aka halitta a abinda zai iya yi, to wannan ya halatta, Allah madaukakin sarki yana cewa:﴿ وَتَعَاوَنُوا عَلَى الْبِرِّ وَالتَّقْوَىِ٢﴾Ma’ana:“Kuma ku yi taimakekeniya akan bin Allah da kuma jintsoron (Sa)”. Suratul Ma’idah, aya ta:2, kuma Allah madaukakin sarki yana cewa:﴿ فَاسْتَغَاثَهُ الَّذِي مِنْ شِيعَتِهِ عَلَى الَّذِي مِنْ عَدُوِّهٌِ١٥﴾Ma’ana:To sai wanda yake cikin jama’arsa ya nemi agajinsa (agajin Annabi Musa u) akan makiyinsa”. Suratul Kasas, aya ta: 15.Nau’i Na Biyu:Neman taimako da neman agaji daga wanda aka halitta a abinda ba mai iya yi sai Allah, kamar neman taimakon wadanda suka mutu, da kuma neman agajin wadanda ke raye da kuma neman taimakonsu a abinda babu mai iko akai sai Allah, kamar warkar da marasa lafiya, da yayewar bakinciki da gusar da cuta, to wannan nau’i bai halattaba, kuma shi shirkace babba, hakika ya kasance a zamanin Annabi ﷺ wani munafiki yana cutar da muminai, sai wasu sukace: Ku tashi mu je mu nemi agajin Ma’aikin Allah ﷺ daga wannan munafuki, sai Annabi ﷺ ya ce: “Ba’a neman agajina ana nemana agajin Allah ne”. Dabarani ne ya ruwaito shi. Annabi ﷺ ya hana a yi anfani da wannan lafazin akansa, dudda abin ya kasance Annabi ﷺ zai iya magance shi a rayuwarsa amma domin baima tahidi kariya da kuma toshe dukkan hanyoyin shirka, da kuma ladabi da kankanda kai ga Ubangijinsa, da kuma tsoratar da al’umma kaucewa hanyoyin shirka na zantuttuka da kuma ayyuka, to idan wannan ya kasance a abinda Annabi ﷺ yake da iko akaine a rayuwarsa, to yaya za’a ne agajinsa bayan bayan rasuwarsa, kuma adinga neman wadansu abubuwa daga wurinsa wand aba mai iko akansu sai Allah, to idan wannan bai halatta ayi wa Ma’aikin Allah ﷺ ba to kenan a hana yi wa wani shi yafi cancanta.**** ***** **** BABI NA UKU:Akan abinda yake zama wajibi akudurce shi dangane da Ma’aikin Allah ﷺ da kuma iyalan gidanshi.To a wanna babin akwai fasali kamar haka:Fasali Na Farko: Akan wajibcin son Manzon Allah ﷺ da kuma girmamashi, da hani akan wuce iyaka da kambamawa a yabonsa, da kuma bayanin matsayinsa.Fasali Na Biyu: Wajibcin yi masa biyayya da kuma koyi da shi.Fasali Na Uku:Shar’antuwar yi masa salatir.Fasali Na Hudu:Akan falalar Iyalansa da kuma abinda ya wajaba garesu ba jafa’i ba kuma wuce iyaka.Fasali Na Biyar:Akan falalar sahabbai da kuma abinda yake zama wajibi a ayi Imani da shi dan gane da su, da kuma bayanin mazahabin Ahlussunna wal jama’ah akan abinda ya wakana atsakanin su.Fasali Na Shida:Akan hana aibanta sahabbai da kuma malaman musulunci. **** ***** **** Fasali Na Farko:Akan wajibcin son Manzon Allah ﷺ da kuma girmamashi, da hani akan wuce iyaka da kambamawa a yabonsa, da kuma bayanin matsayinsa.1. Wajibcin sonsa da kuma girmamashi:Yana zama wajibi akan kowanne bawa tun farko ya so Allah mai girma da daukaka, wannan ko shine mafi girman nau’ukan ibadah, Allah madaukakin sarki yana cewa;﴿ وَالَّذِينَ آمَنُوا أَشَدُّ حُبًّا لِلَّهِ ِ١٦٥﴾Ma’ana:“Wadanda suka yi Imani suna matukar son Allah”. Suratul Bakarah, aya ta:165. Domin shi shine Ubangiji wanda ke yin falala ga bayinsa na dukkan ni’imomi ta zahiri da ta boye, sannan bayan son Allah madaukakin sarki son Manzon Allah (Annabi) Muhammad ﷺ domin shi shine wanda ya yi kira ga son Allah ya yi bayanin son Allah din kuma ya isar da shara’arsa kuma ya yi bayanin hukunce hukuncensa, to dukkan abinda ya samu ga muminai na alheri a nan duniya da kuma lahira to ta hannun Ma’aikin Allah ﷺ ne, babu wani wanda zai shiga aljanna sai ta hanyar bin Manzan Allah ﷺ da kuma bin koyarwarsa, ya zo a hadisi: “Abubuwa uku duk wanda suka kasance a tare da shi to ya sami dandanon Imani; Ya kasance Allah da Manzonsa su ya fi so daga wadanda ba su ba. Kuma ya so mutum ba ya sonsa sai domin Allah. Kuma ya ji tsoron komawa kafirci bayan Allah ya tserar da shi kamar yadda yake tsoron kada a jefa shi wuta”. Bukhari da Muslim ne suka ruwaito. Son Ma’aikin Allah ﷺ tana bin son Allah madaukakin sarkine kuma tana lizimtarta, kuma tana binta a daraja, kuma bayanai sun zo da kebance son Ma’aikin Allah ﷺ da kuma wajibcin gabatar da soyayyarsa akan dukkan wani da ake so in ba Allah madaukakin sarki ba, Ma’aikin Allah ﷺ yane ce wa:“Dayanku imaninsa bai yi ba har sai na kasance nine mafi soyiwa a gareshi da dansa da kuma mahaifinsa da mutane bakiyada”. Bukhari da Muslim suka ruwaito. Ya ma zo cewa ya zama wajibi akan kowanne mumini ya kasance Ma’aikin Allah ﷺ shi ne mafi soyiwa a gareshi akan karankansa, kamar yadda yake a hadisi: “Lalle Umar dan Khaddab t ya ce: Ya Ma’aikin Allah, wallahi kai na fi so sama da komai in ba kai na ba. Sai Ma’aikin Allah ﷺ ya ce: “Na rantse da wanda rayuwata ke a hannunsa har sai na kasance mafi soyuwa akaran kanka”. To daga nan sai Umar ya ce: To lalle kai a yanzu ka fi soyuwa a gareni sama da kaina. Sai Ma’aikin Allah ﷺ ya ce: Ayanzu kan ya Umar”. To a wannan akwai cewa lalle son Ma’aikin Allah ﷺ wajibine kuma shi ake gabatarwa akan son komai in ba Allah madaukakin sarki ba, domin son Ma’aikin Allah yana bin son Allah ne kuma yana tabbatar da son Allah ne, domin so ne akab bin Allah kuma saboda Allah, yana karuwa saboda karuwar son Allah a zuciyar mumini kuma tana raguwa da raguwarsa, kuma dukkan wanda ya kasance yana son Allah to lalle kan zai so akan bin Allah kuma saboda Allah, sonsa shi Ma’aikin Allah taka hukunta girmamashi da kuma da mutuntashi da kuma bin sa da kuma gabatar da maganarsa akan maganar kowanne halitta da kuma girmama karantarwarsa. Babban Malami Ibnu Kayyim –Allah ya yi masa rahama- yana cewa: Dukkan wani so da kuma wani girmamawa da ake yiwa mutum to yana halsatane idan ya zamo yana bin son Allah ne da kuma girmama Allah, kamar son Ma’aikin Allah ﷺ da kuma girmamashi domin wannan yana cikin cikar girmama wanda ya aiko shi da kuma girmamashi, domin al’ummarsa suna sonsa domin son da Allah yake masa kuma suna girmamashi kuma kambamashi saboda kambamawar da Allah ya yi masa, to wannan so yana daga cikin abinda yake tabbatar da son Allah. Abin nufi, lalle shi Ma’aikin Allah ﷺ Allah ya sanya masa abinda yake na kwarjini da kuma so, wanda wani mutum bai so wani mutum ba kuma ba’a sa masa kwarjininsa ba kuma ba’a girmamashi ba kamar Ma’aikin Allah ﷺ a zukatan Sahabbansa Allah ya kara musu yarda, Amru dan As yana cewa bayan ya musulunta: “Ban taba samun mutumin da na ki shi ba kamar shi, amma alokacin da na musulunta ban taba samun mutumin da na so shi ba kamar shi, kuma ban ga wani mai daraja a ido ba kamar shi, ya ce; In; Da za’a tambayeni in wasafta muku shi da ba zan iya ba, domin ban taba kura masa ido ba, saboda girmama shi”. Bukhari ya ruwaito shi. Kuma Urwah da Mas’ud ya ce wa Kuraishawa: “Ya ku mutanena! Ina rantse muku da Allah na je wuri Kisrah (sarkin farisa) da Kaisar (sarkin Rum) da sauran sarakuna, amma ban taba ganin sarkin da mutanansa suke girmamashi ba kamar yadda Sahabba (Annabi) Muhammad suke girmam (Annabi) Muhammad ﷺ, ina rantse muku da Allah ba sa taba kura masa ido saboda girmamawa, kuma bai taba yin kaki ba ya tofar saidai kakin ya fada tafin hannun wani daga cikinsu, ya shafe fuskarsa da girjinsa da shi, kuma idan ya yi alwala sukan kusa danne junansu akan ruwan alwalarsa”. Bukhari da Muslim suka ruwaito.2. Hana Guluwwi da Kambamawa: A yabon Ma’aikin Allahr.Guluwwi: Shi ne wuce iyakar da aka iyakance, Allah madaukakin sarki yana cewa:﴿يَا أَهْلَ الْكِتَابِ لَا تَغْلُوا فِي دِينِكُمْ ﴾Ma’ana:“Kada ku wuce iyaka a addninku”. Suratun Nisa’i, aya ta:171.Kambamawa: Wuce iyaka awurin yabon mutum ko kuma yi masa karya, abinda ake nufi da guluwwi a hakkin Annabi ﷺ shi ne wuce iyakar da Allah ya iyakance masa, kamar a dauke shi daga matsayin bauta da manzanci a sanya masa wasu abubuwa da suka kebanci Ubangiji kamar a dinga kiranshi a dinga neman agajinsa koma bayan Allah kana a dinga rantsewa da shi. Abinda ake nufi da kambamawa ga abinda ya shafi Ma’aikin Allah ﷺ kuwa shi ne a kara a yabonshi, kuma hakika Ma’aikin Allah ﷺ ya hana hakan, a inda yace:“Kada Ku kambani kamar yadda Nasara suka kambama (Annabi Isah) dan Maryam, abin sani kawai Ni bawane kuma Manzone, saboda haka ku ce: Bawan Allah kuma Manzonshi”. Bukhari ya ruwaito shi, ma’ana: kada ku yabeni da abubuwan da suke na barna, kuma kada ku wuce iyaka a yabona kamar yadda Nasara suka wuce iyaka a sha’anin Annabi Isah u, har suka yi masa da’awar hakkin Allah na bauta, saboda haka ku siffanta ni da abinda Ubangina ya siffantani, ku ce: Bawan Allah kuma Manzon Allah. Alokacin da wasu daga cikin Sahabbansa suka ce da shi: Kai ne shugabammu, sai yace: Shugaba shine Allah madaukakin sarki. Alokacin da kuma sukace; Kai ne mafificimmu kuma babbammu a matsayi, sai yace: Kudai fadi maganganunku, ko sashin maganganunku, kada ku bari shaidan ya ja ku”. Abudawud ne ya ruwaitoshi. Wasu mutane sun ce da shi; Ya Ma’aikin Allah, Ya mafificimmu kuma dan mafificimmu, kuma shugabammu dan shugabammu, sai ya ce:“Ya ku mutane! Ku san mekuke cewa, kada shedan ya ja ku, Ni Muhammad bawan Allah kuma Manzon Allah, ba na son ku daga ni sama da matsayina wanda Allah ya sanya min”. Ahmad ne ya ruwaito shi. Ma’aikin Allah ﷺ ya kyamaci da su yabe shi da wadannan lafuzza: Kai ne shugabammu- Kai ne zababbammu- kai ne mafificimmu kai ne mafi darajarmu, tare da cewa shine mafificin halittar Allah baki daya kuma wanda ya fisu matsayi kaf din su, saidai ya hanasu hakanne saboda nisantar da su guluwwi da kuma kambamawa akan abinda ya shafi hakkinsa da kuma bada kariya ga tauhidi, kuma ya dorasu akan su siffantashi da siffofi biyu wadanda suke sune mafi girman daraja ga bawa, kuma babu wuce iyaka sannan kuma ba su da hatsari a tauhidi, sune kuwa; Bawan Allah, kuma Manzan Allah ﷺ, kuma shi bai son su daga shi sama da inda Allah madaukakin sarki ya ajiyeshi na matsayin da ya yardarm masa, kuma hakika wasu dayawa cikin mutane sun sabawa wannan hani na Ma’aikin Allah ﷺ, suka kasance suna suna kiransa kuma suna neman agajinsa, suna rantsewa da shi, suna nema daga wurinsa irin abinda ba’a nema sai gurin Allah kadai, kamar yadda suke yi a wuraran maulidi da kasidu da wakoki basa banbance tsakanin hakkin Allah da hakkin Manzan Allah ﷺ, Ibnu Kayyim yana cewa a littafinsa Nuniyyah:للهِ حَـــــــــــــــقٌّ لاَ يَكُونُ لِغَيْــــــــــرِهِ وَلِعَبْدِهِ حَقٌّ هُمَا حَقَّانِلاَ تَجْعَلُواْ اَلْحَقَّيْنِ حَقًّا وَاحِدًا مِنْ غَيْرِ تَمْيِيزٍ وَلاَ قُرْبَانِMa’ana: Allah yana da hakkin da baya kasancewa ga waninsa, kuma bawansa yana da hakki, yanzu sun zama hakkoki biyu kenan. Kada ku maida hakkoki biyu su koma hakki daya ba tare da kun wareba, kuma kuna neman kusancin Allah.3. Bayanin Matsayinsar. Babu wani laifi don an yi bayanin matsayinsa ta hanyar yabonsa ﷺ da abinda Allah madaukakin sarki ya yabeshi ya kuma ambaci matsayinsa wacce Allah ya fifita shi da ita da kuma kudurce hakan, domin shi ﷺ yanada matsayi mai girma wanda Allah ya ba shi, shi fa bawan Allah ne kuma Ma’aikin Allah kuma zababban Allah ne a halittunsa baki daya, kuma shi ne mafificin halittar Allah bakidaya kuma kai-tsaye, shi Ma’aikin Allah ne zuwa ga mutane bakiyada, kuma zuwa ga aljanu da mutane, kuma shine mafificin Manzanni kuma cika makin Annabwa, babu wani Annabi a bayansa, hakika Allah ya yalwata masa zuciyarsa, kuma ya daga ambatonsa, ya kuma sanya wulakanta da kaskanci akan duk wanda ya saba umarninsa, shi yake da matsayi abin yabo, wanda Allah madaukakin sarki ya ambace shi:﴿ عَسَى أَنْ يَبْعَثَكَ رَبُّكَ مَقَامًا مَحْمُودًا٧٩﴾Ma’ana:“Kuma ya kusa da Ubangikinka zai tayar da kai a wani matsayi abin yabo”. Suratul Isra’i, aya ta: 79. Wato matsayin da Allah zai tayar da shi domin ceton mutane ranar tashin alkiyama, domin Ubangijinsu ya hutar da su daga tsananin wannan tsayuwar, kuma wannan matsayi ne da aka kebeshi da shi ﷺ shi kadai banda sauran Annabawa, shi ne fa wanda ya fi dukkanin halitta jin tsoron Allah, hakika an hana daga murya a inda yake ﷺ kuma aka yi yabo ga dukkanin wadanda suke rage muryarsu a inda yake ﷺ, Allah madaukakin sarki yana cewa:﴿يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَرْفَعُوا أَصْوَاتَكُمْ فَوْقَ صَوْتِ النَّبِيِّ وَلَا تَجْهَرُوا لَهُ بِالْقَوْلِ كَجَهْرِ بَعْضِكُمْ لِبَعْضٍ أَنْ تَحْبَطَ أَعْمَالُكُمْ وَأَنْتُمْ لَا تَشْعُرُونَ٢ إِنَّ الَّذِينَ يَغُضُّونَ أَصْوَاتَهُمْ عِنْدَ رَسُولِ اللَّهِ أُولَئِكَ الَّذِينَ امْتَحَنَ اللَّهُ قُلُوبَهُمْ لِلتَّقْوَى لَهُمْ مَغْفِرَةٌ وَأَجْرٌ عَظِيمٌ٣ إِنَّ الَّذِينَ يُنَادُونَكَ مِنْ وَرَاءِ الْحُجُرَاتِ أَكْثَرُهُمْ لَا يَعْقِلُونَ٤ وَلَوْ أَنَّهُمْ صَبَرُوا حَتَّى تَخْرُجَ إِلَيْهِمْ لَكَانَ خَيْرًا لَهُمْ وَاللَّهُ غَفُورٌ رَحِيمٌ٥﴾Ma’ana: “Ya ku dukkanin wadanda suka yi Imani kada ku daga muryarku sama da muryar Annabi kuma kada ku bayyana masa Magana kamar yadda sashinku ke bayyanarwa ga sashi domin kada ayyukanku su baci alhalin baku sani ba. Lalle dukkanin wadanda suke kasa da muryarsu a inda Manzon Allah yake to wadannan Allah ya jarraba zukatansu da takawa, sunada gafara tamusamman kuma sunada lada mai girma. Lalle wadanda suke kiranka ta bayan dakuna to mafi yawansu basu da hankali. Da ace sudin sun yi hakuri hark a fito zuwa garesu to da hakan ya fi alheri a garesu, kuma Allah mai yawan gafarane kuma mai yawan jinkai”. Suratul Hujurat, ayat ta:2-5. Imam Ibnu Kasir – Allah ya yi masa gafara - yake cewa; A wadannan ayoyi Allah madaukakin sarki ya ladabtar da bayinsa muminai ta yadda za su dinga mu’amala da Ma’aikin Allah ﷺ ta hanyar girmamawa da mutuntawa ganin girma da ganin mutunci ta kada su daga muryarsu a gaban Ma’aikin Allah ﷺ sama da muryarsa, kuma Allah madaukakin sarki ya hana a kirayi Manzon Allah da sunansa kamar yadda ake kiran sauran mutane ace wai; Ya Muhammad’. Saidai kawai za’a kirashine da manzanci ko da annabta, sai ace; Ya Ma’aikin Allah, Ya Annabin Allah, Allah madaukakin sarki yana cewa:﴿لَا تَجْعَلُوا دُعَاءَ الرَّسُولِ بَيْنَكُمْ كَدُعَاءِ بَعْضِكُمْ بَعْضًا قَدْ يَعْلَمُ اللَّهُ الَّذِينَ يَتَسَلَّلُونَ مِنْكُمْ لِوَاذًا فَلْيَحْذَرِ الَّذِينَ يُخَالِفُونَ عَنْ أَمْرِهِ أَنْ تُصِيبَهُمْ فِتْنَةٌ أَوْ يُصِيبَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ٦٣﴾Ma’ana:“Kada ku sanya kiran Manzo a tsakaninku kamar kiran sashinku ga sashi”. Suratun Nur, aya ta:63. Kamar yadda Allah madaukakin sarki yake kiransa da; Ya kai wannan Annabi, Ya kai wannan Manzo, hakika Allah da mala’ikunsa sun yi masa salati, ya kuma umarci bayinsa da yin salati da kuma sallamewa a gareshi, sai Allah Madaukakin sarki:﴿إِنَّ اللَّهَ وَمَلَائِكَتَهُ يُصَلُّونَ عَلَى النَّبِيِّ يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا صَلُّوا عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا تَسْلِيمًا٥٦﴾Ma’ana:“Lalle Allah da mala’ikunsa suna yin salati ga Annabi, Ya ku wadanda suka yi Imani ku yi salati a gareshi kuma ku yi sallami sallamewa”. Suratul Ahzab, aya ta:56. Saidai ba’a kebance wani lokaci ko wani yanayi na musamman domin yabonsa saida dalili ingantacce daga littafin Allah ko Sunnar Ma’aikin Allah ﷺ, amma abinda masu maulidi suke yin a kebance rana wacce wai suke cewa itace ranar da aka haifeshi domin yabonshi to wannan mummunar bidi’ace. Kuma yana daga cikin girmamashi ﷺ girmama karantarwar shi (Sunnar Sa) da kuma kudurce wajibcin aiki da ita, kuma lalle ita tana matsayi na biyune bayan Alkur’ani mai girma, wurin wajibcin girmamawa da kuma aiki, domin itama wahayi ce daga wurin Allah mai girma da daukaka, kamar yadda Allah madukakin sarki ya ce:﴿وَمَا يَنْطِقُ عَنِ الْهَوَى٣ إِنْ هُوَ إِلَّا وَحْيٌ يُوحَى٤﴾Ma’ana: “Kuma ba ya furuci akan san zuciya. Shidin (maganar da ya yi) ba wani abubane saidai wahayi da ake yi masa wahayinsa”. Suratun Najmi, aya ta: 3-4. Bai halatta yin kokwanto a sunnar Ma’aikin Allah ﷺ ko daukarta ba’abakin komai ba, ko kuma tsoma baki akan ingantawa da dha’ifantar da hanyoyin da isinadanta ko kuma bayanin ma’anoninta sai akan ilimi da kwarewa, hakika a wannan lokacin da ake ciki ya yawaita yadda jahilai suka daga wuya akan sunnar Ma’aikin Allah ﷺ musammamma wasu daga cikin samari masu tasowa wadanda suke har yanzu a matakin farko suke na karatu, amma suka kasance suna ingantawa suna dha’ifantawa na abinda ya shafi hadisai, suna jarraha maruwaita hadisi ba tare da wani ilimi ba saidai kawai karanta littafi, wannan abune mai matukar hadari akansu da kuma al’umma baki daya, to ya zama wajibi akan su da su ji tsoron Allah su tsaya inda aka iya kance musu.**** **** **** Fasali Na Biyu:Wajibcin yi masa biyayya da kuma koyi da shi. Yi wa Annabi ﷺ biyayyata abune da yake wajibi, ta hanyar yin abinda ya yi umarni da kuma barin abinda ya hana, wannan ko yana cikin abinda shaida da cewa Shi Ma’aikin Allah ne ta kunsa, hakika Allah ya yi umarni da yi masa biyayya a yoyi masu yawa, wani lokacimma a hada da iwa Allah biyayya, kamar yadda yake a fadin Allah madaukakin sarki:﴿يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا أَطِيعُوا اللَّهَ وَأَطِيعُوا الرَّسُولَ ٥﴾Ma’ana:“Ya ku wadanda suka yi Imani ku bi Allah kuma ku bi Ma’aiki”. Suratun Nisa’i, aya ta: 59. Da ire-iren wadannan ayoyin, wani lokacin yana umarni da bin Ma’aikin Allah ﷺ ne kadai, kamar yadda yake a fadinsa:﴿مَنْ يُطِعِ الرَّسُولَ فَقَدْ أَطَاعَ اللَّهَ٨٠﴾Ma’ana:“Duk wanda ya bi Ma’aiki to hakika ya bi Allah”. Suratun Nisa’i, aya ta:80. Da kuma fadinsa:﴿ وَأَطِيعُوا الرَّسُولَ لَعَلَّكُمْ تُرْحَمُونَ٥٦﴾Ma’ana: “Kumaku bi Ma’aiki domin ayi muku rahama”. Suratun Nur, aya ta:56.Wani lokacin kuma yana yin alkawarin narkon azabane ga dukkan wanda ya sabawa Ma’aikin sa ﷺ, kamar yadda yake cewa:﴿ فَلْيَحْذَرِ الَّذِينَ يُخَالِفُونَ عَنْ أَمْرِهِ أَنْ تُصِيبَهُمْ فِتْنَةٌ أَوْ يُصِيبَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ٦٣﴾Ma’ana:“To wadanda suke sabawa umarninsa su kiyaye domin kada wata fitina ta samesu ko kuma wata azaba mairadadi ta sa me su”. Suratun Nur, aya ta:63. Wato fitina ta samesu a zukatansu na kafirci ko munafinci ko kuma ma bidi’a ko kuma wata azaba mai radadi anan duniya ta hanyar kisa ko haddi ko kullewa ko ma dai wanin hakan, na abinda ya shafi wata ukuba tuna nan duniya. Hakika Allah madaukakin sarki ya sanya yi wa Ma’aikin Allah ﷺ biyayye hanyace ta samun soyayyar Allah ga bawa da kuma gafarta zunubai, Allah madaukakin sarki yana cewa:﴿قُلْ إِنْ كُنْتُمْ تُحِبُّونَ اللَّهَ فَاتَّبِعُونِي يُحْبِبْكُمُ اللَّهُ وَيَغْفِرْ لَكُمْ ذُنُوبَكُمْ وَاللَّهُ غَفُورٌ رَحِيمٌ٣١﴾Ma’ana:“Ka ce; har in kun kasance kuna son Allah, to ku bi ni sai Allah ya so ku kuma ya gafarta muku zunubanku”. Suratu Ali Imran, aya ta:31. Kuma ya sanya yi wa Ma’aikin Allah ﷺ biyayya shi ne shiriya, kuma ya sanya saba masa shi ne bata, Allah madaukakin sarki yana cewa:﴿ وَإِنْ تُطِيعُوهُ تَهْتَدُواُ٥٤﴾Ma’ana:“Kuma idan har kun bi shi to kun shiryu”. Suratun Nur, aya ta:54. Kuma Allah madaukakin sarki yana cewa:﴿فَإِنْ لَمْ يَسْتَجِيبُوا لَكَ فَاعْلَمْ أَنَّمَا يَتَّبِعُونَ أَهْوَاءَهُمْ وَمَنْ أَضَلُّ مِمَّنِ اتَّبَعَ هَوَاهُ بِغَيْرِ هُدًى مِنَ اللَّهِ إِنَّ اللَّهَ لَا يَهْدِي الْقَوْمَ الظَّالِمِينَ٥٠﴾Ma’ana:“Kuma har idan ba su amsa maka ba, to ka sani kawai suna bin son zuciyarsu ne, kuma babu wanda ya kai mai bin son zuciyarsa bata, ba tare da wata shiriya ba daga wurin Allah, lalle Allah ba ya shiryar da mutanan da suke azzaluma”. Suratul Kasas, aya ta: 50. Kuma Allah mai cikakken tsarki ya bada labarin cewa lalle akwai cikakken abin koyi kyakkyawa ga al’ummarsa daga gareshi, sai ya ce:﴿لَقَدْ كَانَ لَكُمْ فِي رَسُولِ اللَّهِ أُسْوَةٌ حَسَنَةٌ لِمَنْ كَانَ يَرْجُو اللَّهَ وَالْيَوْمَ الْآخِرَ وَذَكَرَ اللَّهَ كَثِيرًا٢١﴾Ma’ana:“Hakika ya kasance a gareku dangane da Ma’aikin Allah abin koyi mai kyau ga dukkan wanda ya kasance yana kaunar Allah da ranar lahira kuma ya ambaci Allah da yawa”. Suratul Ahzab, aya ta: 21. Ibnu Kasir ya ce: Wannan ayar mai daraja ita ce asalin da yake babba wurin koyi da Ma’aikin Allah ﷺ a maganganunsa da ayyukansa da kuma halayansa, Allah mai girma da daukaka ya umarci mutane da yin koyi da Annabi ﷺ a ranar yakin taron-dangi, akan hakurinsa da jajircewarsa da kuma dakonsa kana da kokarinsa da kuma sauraron yayewar damuwa daga wurin Ubangijinsa mai girma da daukaka, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi har zuwa ranar sakamako. Hakika Allah ya maimaita biyayya ga Ma’aikin Allah ﷺ da kuma binsa a wurare kusan arba’in a cikin Alkur’ani, kuma mutane suna da matukar bukatar sanin abinda Ma’aikin Allah ﷺ ya zo da shi da kuma bin sa sama da bukatar abin ci da abin sha, idan kuma abinda ake neman bai samu ba to shikenan an mutu tun anan duniya, idan aka rasa biyayya da bin Ma’aikin Allah ﷺ to kan azaba ta auku da dawwamammiyar wahala, hakika Ma’aikin Allah ﷺ ya yi umarnin da a yi koyi da shi awurin aiwatar da ibadu, kuma a aiwatar da su a yadda ya kasance yana aiwatarwa, sai Ma’aikin Allah ﷺ ya ce: “Ku yi sallah kamar yadda kuka ganni ina sallah”. Bukhari ne ya ruwaito shi. Ya kuma ce: “Ku karbi ayyukan hajjin ku daga gare ni”. Muslim ne ya ruwaito shi. Ya kuma ce: “Duk wanda ya aikata wani aiki da ba mu muka umarce shi ba to an mayar masa”. Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi. Kuma ya ce: “Duk wanda ya kawar da kai daga Sunnah ta to ba shi tare da ni”. Bukhari ya ruwaito. Dadai wadansu bayanai masu yawa da suke umarni da yin ko yi da shi, suke kuma hana saba masa.**** **** **** Fasali Na Uku: Shar’antuwar yi masa salati ﷺ. Yana daga cikin hakkinsa rwanda Allah madaukakin sarki ya shar’anta akan al’ummarsa su dinga yi masa salati, hakika Allah madaukakin sarki ya ce:﴿إِنَّ اللَّهَ وَمَلَائِكَتَهُ يُصَلُّونَ عَلَى النَّبِيِّ يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا صَلُّوا عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا تَسْلِيمًا٥٦﴾Ma’ana:“Lalle Allah da mala’iuknsa suna yin salati ga Annabi. Ya ku wadanda suka yi imani ku yi salati a gare shi, kuma amince amincewa”. Suratul Ahzab, aya ta:56. Kuma abin nufi da salatin Allah madaukakin sarki shi ne: Yabonshi a gaban mala’iku. Salatin mala’iku kuma: Addu’a. Salatin ‘yan’dam kuma neman gafara. Kuma hakika Allah madaukakin sarki ya bada labari a wannan ayar akan matsayin bawansa kuma Annabinsa a wurinsa a cikin manyan mala’iku, da cewar yana yabon shi ne agaban mala’iku na kusa, kuma lalle mala’iku na yi masa salati, sannan kuma sai Allah madaukakin sarki ya umarci haluttun kasa da su yi masa salati da da kuma sallamewa, domin ya hada yabon wadanda suke sama da wadanda suke kasa. Kuma ma’anar “Su amince amince wa”. Wato sun gaishe shi gaisuwa da musulunci, to idan mai salati ya yi salati ga Annabi ﷺ sai ya hada salati da sallamewa, ba zai takaita akan dayansu ba, ba zai ce ba: Allah ya yi dadin tsira a gare shi, ya tsaya iya nan ba, kuma ba zai ce; amincin ya tabbata a gare shi’, ya tsaya nan kadai ba, domin Allah ya yi umarni da a hadu baki-daya. Kuma an shar’anta yin salati ga Manzon Allah ﷺ a wasu wurare na musamman, ko ma dai ya zama wajibi ko mustahabbi mai karfi. Ibnu Kayyinm (Allah ya yi masa rahama) ya ambata a cikin littafinsa ‘Jila’ul Afham’ ya ambaci wurare arba’in da daya, ya kuma farane da wuri na farko, shi ne kuma mafi muhimmanci da kuma karfi wato karshen Tahiya, kuma hakika musulmai bakidayan su sun yi ijima’i akan shar’antuwarta, sun karawa juna sani akan wajibcinta a wannan wurin. Sannan kuma ya ambata daga cikin wuraran karshen Alkanut, da kuma Hudubobi kamar hudubar juma’a da ta sallar Idi da kuma sallar rokwan ruwa, da kuma bayan ka maimaita abinda mai kiran sallah yake fada da kuma lokacin addu’a da kuma lokacin shiga masallaci da lokacin fita daga masallacin, da kuma lokacin ambatonsa shi Ma’aikin Allah ﷺ. Sannan kuma ya ambaci fa’idojin da ake samu daga yi wa Ma’aikin Allah ﷺ salati, kuma ya ambaci fa’idoji arba’in. Daga ciki akwai riko da umarnin Allah madaukakin sarki da ya ce a yi hakan, kuma daga ciki samun salati goma daga wurin Allah madaukakin sarki ga dukkan wanda ya yi salatin sau daya, kuma daga ciki akwai fatan karbar addu’ar da ka gabatar da salatin Annabi ﷺ kafin a yi ta. Kuma daga ciki yin salatin daliline na samun ceton Ma’aikin Allah ﷺ idan ya hada salatin da nemar wa Ma’aikin Allah ﷺ wasila, kuma yin salatin dalili ne da gafarta zunubai, kuma dai yin salati gare shi ﷺ dalili ne na Annabi ﷺ ya mayarwa ga wanda ya yi salatin, to tsira da amincin Allah su tabbata ga wannan Annabi mai karamci ﷺ. ***** ***** ***** Fasali Na Hudu: Akan falalar iyalansa da kuma abinda ya wajaba garesu ba jafa’i ba kuma wuce iyaka.Ahlulbaiti: su ne dangin Annabi ﷺ wadanda sadaka ta haramta a garesu, su ne kuma jama’ar gidan sayyidina Aliyu, da gidan Ja’afar da iyalan Akilu da kuma iyalan Abbas da kuma Banu Harith dan Abdulmuddalib da kuma matan Annabi ﷺ da ‘ya’yanshi mata, saboda fadinsa mai girma da daukaka: ﴿وَقَرْنَ فِي بُيُوتِكُنَّ وَلَا تَبَرَّجْنَ تَبَرُّجَ الْجَاهِلِيَّةِ الْأُولَى وَأَقِمْنَ الصَّلَاةَ وَآتِينَ الزَّكَاةَ وَأَطِعْنَ اللَّهَ وَرَسُولَهُ إِنَّمَا يُرِيدُ اللَّهُ لِيُذْهِبَ عَنْكُمُ الرِّجْسَ أَهْلَ الْبَيْتِ وَيُطَهِّرَكُمْ تَطْهِيرًا٣٣﴾Ma’ana:Abinkawai da Allah yake nufi (shine) domin ya tafiyar da kazanta daga gareku Ahlal baiti, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa”. Suratul Ahzab, aya ta: 33. Imam Ibnu Kasir, Allah ya yi masa rahama yake cewa: Sannan kuma abinda babu wani da yake la’akari da Alkur’ani da zai yi kokwantansa shi ne; lalle matan Annabi ﷺ fadarsa Allah mai girma da daukaka.﴿ إِنَّمَا يُرِيدُ اللَّهُ لِيُذْهِبَ عَنْكُمُ الرِّجْسَ أَهْلَ الْبَيْتِ وَيُطَهِّرَكُمْ تَطْهِيرًا٣٣﴾Domin siyakin zancan tare da su yake, saboda wannan ne bayan hakan Allah madaukakin sarki ya ce:﴿وَاذْكُرْنَ مَا يُتْلَى فِي بُيُوتِكُنَّ مِنْ آيَاتِ اللَّهِ وَالْحِكْمَةِ إِنَّ اللَّهَ كَانَ لَطِيفًا خَبِيرًا٣٤﴾Ma’ana:“Kuma ku tuna abinda ake karantawa a dakunan ku na ayoyin Allah da kuma hikima”. Suratul Ahzab, aya ta:34. Wato ku san abinda Allah madaukakin sarki yake saukar da shi ga Manzan shi ﷺ a dakunan kun a Littafin (Alkur’ani) da kuma Sunnah. Katadah da wasu malamai suka ce; Ku tuna wannan ni’ima wacce aka kebance ku da ita banda sauran mutane, da cewar kuma hakika wahayi yana sauka a dakunan ku banda sauran mutane. Kuma (Sayyida) Aisha Siddika ‘yan Siddiki Allah ya kara mata yarda ita ta fi su samun wannan ni’imar, kuma ta kebanta da wannan rahamar wacce take gamammiya, domin wahayi bait aba sauka ga Ma’aikin Allah ﷺ ba a shinfidar wata mata ba in ba ita ba, kamar yadda shi Ma’aikin Allah ﷺ ya nassanta hakan. Kuma wasu daga cikin malamai suka ce: Domin shi Ma’aikin Allah bait aba auran wata budurwaba in ba ita ba, kuma babu wani mutum da ya taba kwana a shinfidarta in ba shi ba ﷺ (wato yana nufin bata taba auran wanni ba in ba shi ba, saboda haka sai ya yi daidai da a wareta da wannan matsayin, kuma ta kebantu da wannan babbar darajar. Saidai matanshi sun kasance cikin Ahlulbaitinsa to danginsa su suka fi cancantar wannan sunana”. Nan maganar ta kare daga Tafsirin Ibnu Kasir. To su Ahlussunnah Wal Jama’a suna son iyalan gidan Ma’aikin Allah ﷺ, kuma suna jibintarsu suna kuma kiyaye wasiyyar Ma’aikin Allah ﷺ dangane da su, da ya yi a ranar Gudai Khum (sunan wuri ne) inda ya ce: “Ina tunasar da ku Allah dangane da iyalaina”. Muslim ne ya ruwaito shi. To su Ahlussunnah suna son su kuma suna karrama su, domin hakan yana daga cikin son Annabi ﷺ da kuma karrama shi, amma hakan saida sharadin sun kasance masu bin Sunnah tsayayyu akan addini, kamar yadda magabatan su suka kasance, kamar Abbas da ‘ya’yansa da sayyidina Aliyu da ‘ya’yansa, amma dukkan wanda ya sabawa Sunnah bai kuma tsayu akan karantarwar musulunci ba to wannan bai halatta a jibince shi ko da ya kasance cikin Ahlulbaiti. Ita fa matsayar Ahlussunnah Wal Jama’a akan iyalan gidan Manzon Allah ﷺ matsaya ce madaidaiciya da kuma bin daidai, suna kaunar wadanda suka rike addini suka kuma tsayu akan shi daga cikin su, kuma suna barranta daga wadanda suka sabawa Sunnah suka karkace wa addini, koda kuwa ya kasance cikin Ahlulbaiti ne, domin kasancewar sa cinkin Ahlulbaiti kuma dangin Ma’aikin Allah ﷺ ba ya anfanar da shi da wani abu har sai ya tsayu akan addinin Allah, domin hakika Abuhurairah t ya ce: Ma’aikin Allah ﷺ ya mike a cikin mu lokacin da aka saukar masa da:﴿وَأَنْذِرْ عَشِيرَتَكَ الْأَقْرَبِينَ٢١٤﴾Ma’ana: “Kuma ka gargadi danginka na kusa”. Suratus Shu’ara’i, aya ta:214. Sai ya ce: “Ya ku taron kuraishawa! –ko kuma wata kalma makamanciyar haka- ku tserar da kawunan ku daga wuta, bazan iya wadatar muku da wani abu ba a gaban Allah. Ya kai Abbas dan Abdulmuddalib bazan iya yi maka komai ba a gaban Allah. Ya ke Safiyyah gwaggwan Ma’aikin Allah ba zan iya yi wadatar miki da wani abu ba a gaban Allah. Ya ke Fatima ‘yar Muhammad ﷺ tambaye ni abinda ya shafi dukiyata duk abinda kike so, ba zan iya wadatar miki da wani abu ba a gaban Allah”. Bukhari ne ya ruwaito shi. Da kuma hadisin: “Duk wanda aikin shi ya ja shi baya to dangantakar shi ba za ta yi sauri a gareshi ba”. Muslim ne ya ruwaito shi. Kuma su Ahlussunnah Wal Jama’ah suna barranta daga aikin Rafilawa (‘Yan shi’ah) wadanda suke wuce iyaka dangane da wasu daga cikin Ahlulbaiti, har ma suke yi musu da’awar ba sa laifi (wato su ma’asumai ne). Kuma (su Ahlussunnah Wal Jama’ah) suna barranta da aikin Nawasib wadanda suke nuna kiyayya ga Ahlulbaiti wadanda suke tsayayyu, suke sukansu. Kuma su (Ahlussunnah Wal Jama’ah) suna barranta daga ayyukan ‘yan’bidi’ah da masu tatsunuyoyi wadanda suke kamun kafa da Ahlulbaiti, kuma suke rikarsu wasu abin bauta koma bayan Allah. To su Ahlussunnah, a wannan babin da waninsa suna kan tsari ne madaidaici kuma tafarki mikakke, wanda babu zakalkalewa a cikin sa babu kuma ko-in-kula, babu wulakantarwa sannan kuma babu wuce-iyaka akan abinda ya shafi hakkin Ahlulbaiti da wasunsu. Su Ahlulbaiti da suke tsayayyu suna musun ayi musu abinda ya wuce-iyaka kuma suna barranta da masu wuce-iyakar. Hakaki Amirul muminina Aliyu dan Abudalib t ya kona masu wuce-iyaka akan al’amarisa da wuta, kuma Abdullahi dan Abbas t ya yarda da kisan na su, saidai yana ganin a kashe su da takobi shi ne ya fi akan konesu din, kuma shi sayyidina Aliyu ya nemi Abdullahi dan Saba’i wanda yake shi ne shugaban masu wuce-iyakar domin ya kashe shi amma ya gudu ya buya, (wanda yake shi Abdullahi dan Saba’in shi ne ya kirkiri shi’anci). **** ***** ***** Fasali Na Biyar:Akan falalar sahabbai da kuma abinda yake zama wajibi a ayi Imani da shi dan gane da su, da kuma bayanin mazahabin Ahlussunna wal jama’ah akan abinda ya wakana atsakanin su.To me ake nufi da sahabbai? Kuma me ya zama wajibi a kudurce dangane da su?.Sahabbai jam’ine na sahabi. Shi ne kuma duk wanda ya hadu da Annabi ﷺ kuma ya yi Imani da shi ya mutu kuma akan imanin. Abinda yake zama wajibi a kudurce dangane da sahabbai shi ne cewa; Sune mafificiyar al’umma, kuma zamaninsu shi ne fiyayyan zamani, saboda sun riga kuma sun kebantu da kasancewa tare da Annabi ﷺ, da yin jihadi tare da shi, da kuma daukar nauyin shari’a daga gareshi da isar da ita ga wadanda suka zo bayan su, hakika Allah ya yabesu a cikin littafinsa Alkur’ani, Allah mai girma da daukaka ya ce:﴿وَالسَّابِقُونَ الْأَوَّلُونَ مِنَ الْمُهَاجِرِينَ وَالْأَنْصَارِ وَالَّذِينَ اتَّبَعُوهُمْ بِإِحْسَانٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمْ وَرَضُوا عَنْهُ وَأَعَدَّ لَهُمْ جَنَّاتٍ تَجْرِي تَحْتَهَا الْأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا أَبَدًا ذَلِكَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ١٠٠﴾Ma’ana:“Kuma da wadanda suka riga (wadanda suke) na farko daga cikin wadanda suka yi hijira da kuma mutanan madina, da wadanda suka bi su da kyautatawa Allah ya yarda su, kuma su ma sun yarda da shi, kuma ya yi musu tattalin gidaje na aljanna koramu suna gudana daga karkashinta, suna masu dawwama a cikinta har abada, wannan shi ne rabo mai girma”. Suratut Tauba, aya ta: 100.Da kuma fadin sa:﴿مُحَمَّدٌ رَسُولُ اللَّهِ وَالَّذِينَ مَعَهُ أَشِدَّاءُ عَلَى الْكُفَّارِ رُحَمَاءُ بَيْنَهُمْ تَرَاهُمْ رُكَّعًا سُجَّدًا يَبْتَغُونَ فَضْلًا مِنَ اللَّهِ وَرِضْوَانًا سِيمَاهُمْ فِي وُجُوهِهِمْ مِنْ أَثَرِ السُّجُودِ ذَلِكَ مَثَلُهُمْ فِي التَّوْرَاةِ وَمَثَلُهُمْ فِي الْإِنْجِيلِ كَزَرْعٍ أَخْرَجَ شَطْأَهُ فَآزَرَهُ فَاسْتَغْلَظَ فَاسْتَوَى عَلَى سُوقِهِ يُعْجِبُ الزُّرَّاعَ لِيَغِيظَ بِهِمُ الْكُفَّارَ وَعَدَ اللَّهُ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ مِنْهُمْ مَغْفِرَةً وَأَجْرًا عَظِيمًا٢٩﴾Ma’ana:“Muhammadu Ma’aikin Allah ne, kuma wadanda suke tare da shi masu tsanani ne akan kafirai kuma masu tausayin junan su ne, za ka gan su suna ruku’i suna sujjadah suna neman falala daga wurin Allah da kuma yarda. Alamarsu a fuskokinsu na gurbin sujjada, wannan shi ne siffas su a cikin Attaura, siffas su kuma a Injila kamar shuka ce ta fitar da saiwarta, kuma ta yi karfi ta kafu ta daidaitu akan tushanta, take burge manoma domin ya bakantawa kafirai rai. Allah ya yi alkawari ga dukkanin wadanda suka yi Imani da kuma ayyuka na kwarai daga cikinsu da kuma gafara da lada mai girma”. Suratul Fath, aya ta: 29. Kuma Allah madaukakin sarki ya ce:﴿لِلْفُقَرَاءِ الْمُهَاجِرِينَ الَّذِينَ أُخْرِجُوا مِنْ دِيَارِهِمْ وَأَمْوَالِهِمْ يَبْتَغُونَ فَضْلًا مِنَ اللَّهِ وَرِضْوَانًا وَيَنْصُرُونَ اللَّهَ وَرَسُولَهُ أُولَئِكَ هُمُ الصَّادِقُونَ٨ وَالَّذِينَ تَبَوَّءُوا الدَّارَ وَالْإِيمَانَ مِنْ قَبْلِهِمْ يُحِبُّونَ مَنْ هَاجَرَ إِلَيْهِمْ وَلَا يَجِدُونَ فِي صُدُورِهِمْ حَاجَةً مِمَّا أُوتُوا وَيُؤْثِرُونَ عَلَى أَنْفُسِهِمْ وَلَوْ كَانَ بِهِمْ خَصَاصَةٌ وَمَنْ يُوقَ شُحَّ نَفْسِهِ فَأُولَئِكَ هُمُ الْمُفْلِحُونَ٩﴾Ma’ana:“(Abayar) ga dukkanin fakirai masu hijira wadanda aka fitar da su daga gidajan su da dukiyoyinsu suna neman falala daga wurin Allah da kuma yarda, suna kuma taimako (addinin) Allah da kuma Manzan shi, wadannan sune wadanda suka yi gaskiya. Da kuma wadanda suka bayar da gida (mutanan madina da suka sauki wadanda suka yi hijira) da kuma Imani kafin su, suna son wanda ya yi hijira zuwa garesu ba sa jin wata damuwa a zukatan su akan abinda suka bayar, kuma suna fifita (masu hijira) akan su koda kuwa wannan abin sun kebance shi ne domin kan su, kuma duk wanda aka tsare shi daga yi wa kansa kwauro to wadannan sune wadanda suka rabauta”. Suratul Hashr, aya ta:8-9. To awadannan ayoyin hakika Allah mai girma da daukaka ya yi yabo ga Muhajirun (wadanda suka yo hijira) ya kuma ya bi Ansar (mutanan Madina), kuma ya wasafta su da wadanda suka riga aikata alheri, kuma ya bada labarin lalle shi ya yarda da su, kuma ya yi musu tattalin gidaje na aljanna, kuma ya siffanta su da cewa su masu tausayin junan su ne kuma masu tsanani akan kafirai, ya siffanta su da yawan ruku’i da sujjada da kuma kyawun zuciya. Kuma su ana gane su ne da biyayya ga Allah da kuma Imani, kuma Allah ya zabe su ne domin su kasance sahabbai ne na Annabin sa domin ya bakantawa makiyansa wato kafirai. Kamar kuma yadda ya siffanta wadanda suka yi hijira suka bar kasashen su da dukiyoyinsu domin Allah madaukakin sarki da taimakon addininsa da kuma neman falalarsa da yardarsa, kuma lalle su wadanda suka tabbatar da hakan ne. Ya kuma siffanta mutanan Madina da cewar sune masu masaukin wadanda suka yi hijira, suka kuma taimaka ga su da Imani na gaskiya, ya kuma siffanta su da son ‘yan’uwansu Muhajirai (wadanda suka yo hijira), da yadda suke fifita su ma akan kan su, da yadda suke hakura domin su da kuma yadda suka kubuta daga kwauro, to fa da wannan ne suka rabauta. Wannan shi kadan daga cikin falalarsu wacce take gamammiya, to kuma suna da falala wacce take takebanci wasu ne, da kuma matsayi wanda wani ya dara wani, Allah ya kara musu yarda, wannan ko gwargwadon yadda suka riga juna shiga musulunci da kuma jihadi da hijira. Mafi girman Sahabbai sune Halifofi hudu: wato Abubakar da Umar da Usman da Aliyu. sannan sai sauran da suka cika goma wadanda aka yi musu bishara da aljanna, sune kuma bayan wadannan hudun sai; Dalhatu da Zubairu da Abdurrahman dan Awf da kuma Abu’ubaidah dan Jarrah da kuma Sa’ad dan Abiwakkas sai kuma Sa’id dan Zaid. Muhajirai (wadanda suka yo hijira) sun dara mutanan Madina falala, sai wadanda suka je Badar sai kuma wadanda suka halarci sulhun Hudaibiyyah (Bai’atur Radhwan). Kuma wanda ya musulunta kafin bude Makkah ya kuma yi yaki ya dara wanda ya musulunta bayan bude Makkah. Mazahabar Ahlussunnah Wal Jama’ah dangane da abinda ya auku a tsakanin sahabbai na yaki da kuma fitintinu: Sababin Futuntunu: Yahudawa sun yi wa Musulunci da kuma Musulmai shiri, sai suka kulla makirci mummuna ta yadda suka bayyana musulunci domin karya tsagwaranta (wannan makirci kuwa) shi ne Abdullahi dan Saba’i daga cikin Yahudawan Yaman yake, sai wannan bayahude ya fara kulla wannan makirci da bala’i iri-iri akan halifa na uku daga cikin halifofi masu shiryarwa wato sayyidina Usman t, ya dinga kirkiro tuhume-tuhume akan sa, sai ko wadanda suke kusa da shi masu gajeran tunani masu raunin Imani masu son fitina suka waiga ya yaudare su, har aka shirya yadda za’a kashe Khalifa mai shiryarwa Usman t yana wanda aka zalunta. To fa bayan kashe shi ne fitina ta auku tsakanin Musulmai, fitina ta ruru saboda yadda bayahudannan da mabiyansa suke ta ziga har yaki ya auku tsakanin sahabbai akan ijitihadin da suka yi.Mai sharhin littafin Tahawiyyah yake cewa: Lalle asalin shi’anci ya faru ne ta hanyar wani munafiki kuma zindiki, abinda yake so kawai shi ne ya bata musulunci ya kuma muzanta Ma’aikin Allah ﷺ, kamar yadda malamai suka ambaci hakan, domin shi Abdullahi dan Saba’i alokacin da ya bayyana cewar shi musulmi ne abinda yake so shi ne ya bata addinin musuluncin da mummunan makircinsa, kamar yadda Bulus ya yi wa addini Nasara. Sai ya bayyana riko da musulunci, sannan kuma ya bayyana umarni da kyakkyawan aiki da kuma hani ga mummunan aiki, hardai ya dinga hada fitinar da ta kai ga kashe sayyidin Usman. Sannan lokacin da ya isa Kufa sai ya bayyana wuce iyaka dangane da sayyidin Aliyu da taimakonsa, domin cimma burin sa, har labarin hakan ya kai ga sayyidina Aliyu sai ya yi nufin kashe shi nan-da-nan sai ya gudu zuwa Kurkis, labarinsa sananne ne a wurin malaman tarihi. Shehul Islam Ibnu Taimiya –Allah ya yi masa rahama- ya ce: Alokacin da aka kashe (sayyidina) Usman zukata sun rarrabu bakin-ciki ya girmama, sharri iri-daban-daban ya bayyana kuma mutanan kwarai sun tozarta, kuma ya afka cikin fitinar wanda bai kamata ya shiga ba, wanda ko yake son tabbatar da alheri da kawo gyara ya kasa hakan. Sai suka yi wa Amirul muminina Aliyu dan Abitalibt, kuma shi ya fi kowa cancantar zama Khalifa a wannan lokaci kuma shi ne mafi darajar wadanda suka saura, saidai zukata sun kasance a rarrabe, kuma wutar rikici na ruruwa kalama bata hadu ba, kuma ba sami tsarin haduwar kai ba, saboda haka Khalifa (Aliyu Bin Abitalibt) da sauran mataimakansa na gari ba su sami damar aiwatar da duk abinda suke so na alheri ba, mutane da dama suka shiga cikin kungiyoyi da fitintinu har abinda ya kasance ya kasan ce. Kuma dai ya sake fada yana bayyana hanzarin wadanda suka yi yakin daga cikin sahabbai a yakin sayyidina Aliyu da Mu’awiya (Allah ya kara musu yarda): Shi Mu’awiya bai bar halifanci ba kuma bai yi mishi (bai yi wa sayyidina Aliyu) mubaya’a ba a lokacin da ya yaki sayyidina Aliyu, kuma bai yake shi a matsayin shi Khalifa ba ne, kuma bai yake shi a matsayin wanda ya cancanci halifancin ba, kuma suna tabbatar masa da wannan, kuma shi ma Mu’awiyan ya kasance yana tabbatar da hakan ga duk wanda ya tambaye shi akan haka, kuma Mu’awiya t da jama’arsa ba sa ganin ace sun farwa sayyidina Aliyu t da jama’arsa da yaki ba tare da komai ba. Saidai a lokacin da sayyidina Aliyu t ya ga jama’arsa ya zama wajibi akan su da su yi masa biyayya kuma su yi masa mubaya’ah ta yadda babu yadda zai kasance ga al’ummar ai sai Khalifa guda daya, kuma su (Mu’awiya da jama’arsa) sun ki su yi masa biyayya akan wannan wajibin kuma ga shi suna da karfi, sai ya ga abinda ya dace shi ne ya yake su harsai sun sauke wannan wajibin, wannan kuma zai sa al’umma ta dunkule karkashin shugabanci guda. Su kuma Mu’awiya t da jama’arsa cewa: Ai wannan ba wajibi ba ne akan su, kuma suna ganin har idan aka yake su akan haka to ai sun kasance wadanda aka zalinta. Suka kuma ce: Domin sayyidin Usman t ai an kashe shi ne kuma anzalince shi, wannan kuma dukkan al’ummar musulmai sun yi ittifaki akan haka, kuma wadanda suka kashe shi suna cikin dakarun sayyidina Aliyu t kuma suna da karfi, to idan muka yi musu mubaya’a sun zalince mu kuma za su yi mana aika-aika, kuma (Sayyidina) Aliyu ba zai iya hana su ba kamar yadda bai iya kare (Sayyidina) Usman t ba, kawai abinda yake a kan mu shi ne mu yi mubaya’a ga Khalifan da zai iya kare mu kuma ya yi kokarin yi mana adalci. Kuma shi mazhabin Ahlussunnah Wal Jama’a a wannan sabanin da ya auku da kuma fitinar da ta auku har yaki ya kasance a tsakanin sahabbai to ya dunkulu ne a abubuwa biyu:Abu Na Farko: Su suna yin shiru ne akan abinda ya faru tsakanin sahabbai, kuma basa zurfafa bincike akan haka, domin abinda ya fi zama lafiya shi ne mutum ya yi shiru dangane da irin wadannan bayanan, kuma su Ahlussunnah suna cewa ne:﴿وَالَّذِينَ جَاءُوا مِنْ بَعْدِهِمْ يَقُولُونَ رَبَّنَا اغْفِرْ لَنَا وَلِإِخْوَانِنَا الَّذِينَ سَبَقُونَا بِالْإِيمَانِ وَلَا تَجْعَلْ فِي قُلُوبِنَا غِلًّا لِلَّذِينَ آمَنُوا رَبَّنَا إِنَّكَ رَءُوفٌ رَحِيمٌ١٠﴾Ma’ana:“ (Ya) Ubangijin mu ka gafarta mana kuma da ‘yan’uwan mu wadanda suka riga mu da yin Imani, kuma kada ka sanya a zukatan mu wata damuwa na wadanda suka yi Imani, (Ya) Ubangijin mu lalle kai mai yawan tausasawa ne kuma mai yawan jinkai”. Suratul Hashr, aya ta: 10.Abu Na Biyu: Yadda suke bada amsa akan abubuwan da ake ruwaitowa na wasu abubuwa munana na su, daga cikin (yadda suke bada amsa) akwai fuskoki kamar haka:Fuska Ta Farko: daga cikin wadannan riwayoyi akwai abubuwan da suke karya ne, makiyan su ne suka kirkira domin su bata su.Fuska Ta Biyu: daga cikin wadannan riwayoyin akwai abinda aka kara kuma aka rage shi aka kuma canza shi daga yadda yake na gaskiya, sai karya ta shiga ciki, to wannan an juyashi ba za’a kallece shi ba.Fuska Ta Uku: lalle abinda ya inganta a wadannan riyayoyin kuma shi ne ma kadan, to su wadanda za’a baiwa uzuri ne, domin kodai su din sun yi ijtihadi kuma suka dace da daidai, ko kuma masu ijtihadi ne amma kuma suka yi kuskure, to ko wannan yana daga cikin abubuwa na ijtihadi wanda idan wanda ya yi ijtihadi a ciki kuma ya dace da daidai to yana da lada biyu, idan kuma ya yi kuskure to yana da lada daya kuma kuskuren an yafe. Saboda hadisin da yake cewa; lalle Ma’aikin Allah ﷺ ya ce: “Idan mai hukunci ya yi ijtihadi sai kuma ya dace da daidai to yana da lada biyu, idan kuma ya yi ijtihadi to sai ya kuskure yana da lada daya”.Fuska Ta Hudu: Su fa mutane ne, saboda haka kuskure yana iya samuwar daidaikun su, domin su bama’asumai bane daga zunubai (wadanda basa sabawa Allah; Kamar Annabawa da mala’iku) idan muka kalle su a daya-dayan su, saidai abindake faruwa daga garesu (na laifin) to yana da abubuwan da suka kankare shi masu yawa:1. Zai iya kasancewa ya tuba daga wannan abin, tuba kuwa tana share munanan ayyuka komai girmansa, kamar yadda dalilai suka nuna.2. Lallle suna da manyan ayyuka da falala wadanda suke tabbatar da gafarta musu abinda suka aikata – in sun aikata din-, Allah madaukakin sarki yana cewa:﴿ إِنَّ الْحَسَنَاتِ يُذْهِبْنَ السَّيِّئَاتِ ذَلِكَ ذِكْرَى لِلذَّاكِرِينَ١١٤﴾Ma’ana:“Lalle kyawawan ayyuka suna tafiyar da munana”. Suratu Hud, aya ta:114.3. Lalle su ana ninninka musu kyawawan ayyuka sama da wadanda ba su ba, kuma babu wani mutum wanda yake daidai da su a falala, kuma hakika ya tabbata daga Ma’aikin Allah ﷺ ya ce: “Lalle su sune mafi alherin zamani, kuma lalle mudu guda na dayansu idan ya bada shi sadaka to ya fi dutsan uhudu na zinari da wani wand aba su ba ya yi sadaka da shi”. Allah ya kara musu yarda, kuma ya yardar da su shi. Shehul Islam Ibnu Taimiya –Allah ya yi masa rahama- ya ce: Kuma sauran Ahlussunnah Wal Jama’ah da jagororin addini ba su da akidar cewar wani daga cikin sahabbai ma’asumi ne ko wani daga cikin ahlulbaiti ko cikin wadanda suka riga ko ma waninsu, saidai yana iya faruwa a tare da su aikata wani laifi, kuma Allah madaukakin sarki yana gafarta musu ta sanadiyyar tuba, kuma yana daga darajarsu, yana kuma gafarta musu ta sanadiyyar kyawawan ayyuka masu shafe laifuka, ko ma da wanin hakan na abubuwan da suke zama sabubba, Allah madaukakin sarki ya ce:﴿وَالَّذِي جَاءَ بِالصِّدْقِ وَصَدَّقَ بِهِ أُولَئِكَ هُمُ الْمُتَّقُونَ٣٣ لَهُمْ مَا يَشَاءُونَ عِنْدَ رَبِّهِمْ ذَلِكَ جَزَاءُ الْمُحْسِنِينَ٣٤ لِيُكَفِّرَ اللَّهُ عَنْهُمْ أَسْوَأَ الَّذِي عَمِلُوا وَيَجْزِيَهُمْ أَجْرَهُمْ بِأَحْسَنِ الَّذِي كَانُوا يَعْمَلُونَ٣٥﴾Ma’ana:“Duk wanda yazo da gaskiya kuma ya gasgata da shi to wadannan sune masu takawa. Sunada duk abinda suke so a wurin Ubangijin su, wannan ko shi ne sakamakon masu kyautatawa. Domin Allah ya kankare musu mummunan aikin da suka yi kuma ya sakanka musu da ladan su da mafi kyawun abinda suka kasance suna aikatawa”. Suratuz Zumar, aya ta: 33-35. Kuma Allah madaukakin sarki ya ce:﴿ حَتَّى إِذَا بَلَغَ أَشُدَّهُ وَبَلَغَ أَرْبَعِينَ سَنَةً قَالَ رَبِّ أَوْزِعْنِي أَنْ أَشْكُرَ نِعْمَتَكَ الَّتِي أَنْعَمْتَ عَلَيَّ وَعَلَى وَالِدَيَّ وَأَنْ أَعْمَلَ صَالِحًا تَرْضَاهُ وَأَصْلِحْ لِي فِي ذُرِّيَّتِي إِنِّي تُبْتُ إِلَيْكَ وَإِنِّي مِنَ الْمُسْلِمِينَ١٥ أُولَئِكَ الَّذِينَ نَتَقَبَّلُ عَنْهُمْ أَحْسَنَ مَا عَمِلُوا وَنَتَجَاوَزُ عَنْ سَيِّئَاتِهِمْ فِي أَصْحَابِ الْجَنَّةِ وَعْدَ الصِّدْقِ الَّذِي كَانُوا يُوعَدُونَ١٦﴾Ma’ana:“Har zuwa lokacin da ya kai karfinsa, kuma ya kai shekaru arba’in ya ce; (Ya) Ubangiji! Ka kimsamin da ingode wa ni’imarka wacce ka ni’imta a gareni da kuma mahaifana, kuma (ka kimsamin) in aikata aiki na kwarai wanda zaka yarda da shi, kuma ka kyautata min a cikin zuriyata. Lalle ni na tuba zuwa gareka kuma lalle ni ina cikin musulmai. Wadannan sune wadanda muke karba daga garesu mafikyawun abinda suka aikata, kuma muke yafe musu munanan ayyuka cikin ‘yan’aljanna”. Suratul Ahkaf, aya ta:15-16. Kuma hakika makiya Allah sun riki abinda ya faru tsakanin sahabbai na sabani da yaki wata kafa domin aibanta su da kuma zubar musu da mutunci, hakika wasu marubuta masu mugun nufi ‘yan zamani sun tafi akan irin wannan mummunan tsarin wadanda ma basu san me suke fada ba suka sanya kan su masu hukunci tsakanin sahabban Ma’aikin Allah ﷺ su ce su wane sune akan daidai su wane kuma su suka yi kuskure ba tare da wani dalili ba, kawai da jahilci da kuma bin son zuciya, da kuma maimaita abinda rudaddu masu mugun nufi cikin makiya Allah suke fada da ire-iren su, har su sanya shakku a zukatan samari masu tasowa wadanda suke fahimtarsu da ingantaccen tarihi da ma tarihin al’ummarsu mai daraja fahimtace kankanuwa, da ma tarihin magabatan su na kwarai wadanda suke su ne mafi alherin zamani, domin nan gaba su kai ga sukar musulunci da kuma raba kan musulmai, da kuma sanya kyama a zukatan mutanan karshe na wannan al’ummar su kyamaci mutanan farko, maimakon su yi ko yi da magabata na kwarai da kuma aiki da fadarsa Allah madaukaki:﴿وَالَّذِينَ جَاءُوا مِنْ بَعْدِهِمْ يَقُولُونَ رَبَّنَا اغْفِرْ لَنَا وَلِإِخْوَانِنَا الَّذِينَ سَبَقُونَا بِالْإِيمَانِ وَلَا تَجْعَلْ فِي قُلُوبِنَا غِلًّا لِلَّذِينَ آمَنُوا رَبَّنَا إِنَّكَ رَءُوفٌ رَحِيمٌ١٠﴾Ma’ana:“Kuma wadanda suka zo daga bayansu (wato bayan sahabbai) suna cewa ne: (Ya) Ubangijin mu ka gafarta mana kuma da ‘yan’uwan mu wadanda suka riga mu da yin Imani, kuma kada ka sanya a zukatan mu wata damuwa na wadanda suka yi Imani, (Ya) Ubangijin mu lalle kai mai yawan tausasawa ne kuma mai yawan jinkai”. Suratul Hashr, aya ta: 10.**** ***** ***** Fasali Na Shida:Akan hana aibanta sahabbai da kuma malaman musulunci.1. Hani Akan Aibanta Sahabbai.Yana daga cikin asalin tushen Ahlussunnah Wal Jama’ah tsaftatuwar zukatan su da kuma harsunan su ga sahabban Ma’aikin Allahr, kamar yadda Allah madaukakin sarki ya siffanta su da hakan a fadarsa:﴿وَالَّذِينَ جَاءُوا مِنْ بَعْدِهِمْ يَقُولُونَ رَبَّنَا اغْفِرْ لَنَا وَلِإِخْوَانِنَا الَّذِينَ سَبَقُونَا بِالْإِيمَانِ وَلَا تَجْعَلْ فِي قُلُوبِنَا غِلًّا لِلَّذِينَ آمَنُوا رَبَّنَا إِنَّكَ رَءُوفٌ رَحِيمٌ١٠﴾Ma’ana:“Kuma wadanda suka zo daga bayansu (wato bayan sahabbai) suna cewa ne: (Ya) Ubangijin mu ka gafarta mana kuma da ‘yan’uwan mu wadanda suka riga mu da yin Imani, kuma kada ka sanya a zukatan mu wata damuwa na wadanda suka yi Imani, (Ya) Ubangijin mu lalle kai mai yawan tausasawa ne kuma mai yawan jinkai”. Suratul Hashr, aya ta: 10. Da kuma biyayya ga Ma’aikin Allah ﷺ a fadarsa:“Kada ku zagi sahabbaina, to ina rantsuwa da wanda raina yake a hannunsa inda a ce dayanku zai ciyar da abinda ya kai dutsan uhudu na zinari to bai kai mudu guda na dayansu ba bai kai kuma rabinsa ba”. Bukhari da Muslim suka ruwaito. Kuma suna barranta daga hanyar Rafilawa (Shi’a) da kuma Khawarij wadanda suke aibanta sahabbai Allah ya kara musu yarda suke fishi da su suke yin musun falalarsu suke kuma kafirta su. Su Ahlussunnah suna karbar abinda ya zo ne daga littafin Allah da kuma karantarwar Ma’aikin Allah na falalarsu, kuma suna kudurcewa sune mafi girman al’umma, kamar yadda Annabi ﷺ ya ce: “Fiyayyanku su ne zamani na”. Bukhari da Muslim suka ruwaito. Kuma alokacin da Ma’aikin Allah ﷺ ya anbaci rarrabuwar al’umma zuwa kungiya saba’in da uku kuma ya bayyana cewar duk wuta ne saidai kwaya daya, kuma sahabbai suka tambaye shi wacce ce wannan dayar, sai ya ce: “Su ne duk wanda ya kasance akan irin abinda nake akan shi yau ni da sahabbai na”. Tirmizi ne ya ruwaito. Abuzur’ah ya ce –shi ne kuwa babban malamin Imam Muslim-: Idan ka ga mutum yana rage darajan wani daga cikin sahabbai to ka sani shi dinnan zindiki ne, saboda lalle Alkur’ani gaskiya ne kuma Manzo gaskiya ne kuma abinda ya zo da shi gaskiya ne, kuma babu wanda ya kawo mana wadannan bayanai bakidayansu sai sahabbai, to dukkan wanda ya muzanta su to yana son kawai ya lalata littafin Allan ne (Alkur’ani) da kuma Sunnar Ma’aikin Allah ﷺ, sai ya kasance shi ya fi cancantar a muzanta kuma a yi mishi hukunci da zindikanci da kuma bata. Ibnu Hamdan a cikin littafinsa Nihayatul Mubtadi’in yana cewa: Duk wanda ya zagi daya daga cikin sahabbai kuma ya halatta hakan to ya kafurta, idan ko bai halasta hakan ba to fasiki ne, kuma akwai wata riwayar daga gare shi cewar ya kafurta kawai, duk kuma wanda ya fasikantar da su ko ya sokesu a addini ko ya kafurta su to ya kafurta.2. Hani Akan aibanta Malamai magabata na wannan al’ummar: Wadanda suke biye da sahabbai a falala da daraja da matsayi sune jagorori na shiriya cikin Tabi’ai da kuma wadanda suke bin Tabi’an cikin wadanda suke a shekarunnan masu falala, da kuma wadanda suka zo bayan sahabban da kyautatawa, kamar yadda Allah madaukakin sarki ya ce:﴿وَالسَّابِقُونَ الْأَوَّلُونَ مِنَ الْمُهَاجِرِينَ وَالْأَنْصَارِ وَالَّذِينَ اتَّبَعُوهُمْ بِإِحْسَانٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمْ وَرَضُوا عَنْهُ وَأَعَدَّ لَهُمْ جَنَّاتٍ تَجْرِي تَحْتَهَا الْأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا أَبَدًا ذَلِكَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ١٠٠﴾Ma’ana:“Kuma wadanda suka riga na farko cikin wadanda suka yi hijira (Muhajirun) da kuma mutanan Madina (Ansar), da kuma dukkanin wadanda suka bi su da kyautatawa Allah ya yarda da su kuma sun yarda da shi”. Suratut Taubah, aya ta: 100. Bai halasta a aibanta su ko kuma a zage su, domin su jagorori ne na shiriya, kuma hakika Allah madaukakin sarki ya ce:﴿وَمَنْ يُشَاقِقِ الرَّسُولَ مِنْ بَعْدِ مَا تَبَيَّنَ لَهُ الْهُدَى وَيَتَّبِعْ غَيْرَ سَبِيلِ الْمُؤْمِنِينَ نُوَلِّهِ مَا تَوَلَّى وَنُصْلِهِ جَهَنَّمَ وَسَاءَتْ مَصِيرًا١١٥﴾Ma’ana:“Duk wanda ya sabawa Manzo bayan shiriya ta bayyana a gare shi, kuma ya bi hanyar da bata muminaiba to zamu juyar da shi abinda ya dauka kuma mu sa shi a jahannama, kuma ta yi muni ta zama makoma”. Suratun Nisa’i, aya ta:115. Mesharhin littafin Tahawiyya ya ce: To yana zama wajibi akan dukkan musulmi bayan ya so Allah ya kuma so Ma’aikin Allah to ya so muminai, kamar yadda Alkur’ani ya yi furuci da shi musamman wadanda sune magada Annabawa, wadanda Allah ya sanya su matsayin taurari da ake shiryuwa da su a cikin duhun dare ko duhun teku, kuma hakika musulmai sun yi ijima’i akan shiriyarsu da kuma kwarewarsu, domin su sune halifofin Ma’aiki ﷺ a cikin al’ummarsa, kuma masu rayar da abinda yam utu na sunnoninshi, da sune fa littafin Allah ya tsayu kuma da shi ne suka tsayu, kuma da su littafin Allah ya yi furuci kuma da shi ne suka yi furuci, kuma dukkanin su sun yi ittifaki na yankar shakku akan wajibcin bin Ma’aiki ﷺ, saidai idan aka sami daya daga cikin su yana da wata Magana da kuma hadisi ingantacce ya zo da sabanin wannan maganar, to ba makawa yana da wani uzuri na barinsa.Dukkanin uzurin nau’uka uku ne:Na Farko: Rashin kudurcewarsa lalle Ma’aikin Allah ﷺ ya fadi maganar.Na Biyu: Kudurcewarsa lalle shi ya nufaci wannan mas’alar da wannan maganar.Na Uku: Kudurcewarsa lalle wannan hukuncin an share shi. Suna da falala akam mu, da matsayi na sun riga mu, da kuma isar da abinda aka aiko Ma’aiki ﷺ da shi zuwa gare mu, da kuma bayyana abinda ya boyu a gare mu, to Allah ya yarda da su kuma ya yardar da su. ﴿وَالَّذِينَ جَاءُوا مِنْ بَعْدِهِمْ يَقُولُونَ رَبَّنَا اغْفِرْ لَنَا وَلِإِخْوَانِنَا الَّذِينَ سَبَقُونَا بِالْإِيمَانِ وَلَا تَجْعَلْ فِي قُلُوبِنَا غِلًّا لِلَّذِينَ آمَنُوا رَبَّنَا إِنَّكَ رَءُوفٌ رَحِيمٌ١٠﴾Ma’ana:“ (Ya) Ubangijin mu ka gafarta mana kuma da ‘yan’uwan mu wadanda suka riga mu da yin Imani, kuma kada ka sanya a zukatan mu wata damuwa na wadanda suka yi Imani, (Ya) Ubangijin mu lalle kai mai yawan tausasawa ne kuma mai yawan jinkai”. Suratul Hashr, aya ta: 10. Rage darajar malamai domin sun afkawa wani kuskure na ijtihadi na wasu daga cikinsu to wannan hanyace ta ‘yanbidi’ah, kuma yana daga cikin tsarin makiya domin sanya shakku a cikin addinin musulunci, da kuma sanya gaba tsakanin musulmi, kuma domin a raba tsakanin wannan al’umma da malamanta na farko, kuma a daidaita kiyayya tsakanin samari da malamai kamar yadda yake faruwa a yau, to anan dalibai masu tasowa su fahimci haka, wadanda wasu daga cikin su suke watsi da darajar malaman fikihu suke kuma watsi da fikihun musulunci, suke nesa da karanta shi suke kuma nesa da amfanuwa da gaskiyar da kuma daidai din dake cikinsa. Su sami matsayi da izza da fikihun su kuma su girmama malamansu, kada su yaudaru da wasu surakatai masu batarwa masu rudarwa, Allah shi ne mai datarwa.**** ***** **** BABI NA HUDU:Bidi’o’iKuma shi kuma wannan babin ya kunshi fasali kamar haka:Fasali Na Farko: Bayanin mecece bidi’a – Nau’ukanta-Hukunce hukuncenta.Fasali Na Biyu: Bayyanar bidi’o’i a rayuwar musulmai, da kuma sabubban da suka haifar da hakan.Fasali Na Uku:Matsayar al’ummar musulmi dangane da ‘yanbidi’ah, sannan kuma tsarin Ahlussunnah Wal Jama’a dangane da yi musu raddi.Fasali Na Hudu:Magana akan missalan bidi’o’i a wannan lokacin.1. Bikin Mauludin Annabi ﷺ.2. Neman albarka da wurare da kayaayaki da matattu da makamantan su.3. Bidi’o’i a fagen ibada da kuma neman kusanci zuwa ga Allah.**** ***** **** Fasali Na Farko:Bayanin mecece bidi’a – Nau’ukanta-Hukunce hukuncenta.Bayanin Bidi’a, a gundarin bakin Larabci: shi ne abinda aka kaga ba a wani kwatankwaci da ya gabata ba, akan wannan ne Allah madaukakin sarki ya ce:﴿بَدِيعُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ١١٧﴾Ma’ana:“Wanda ya kagi halittar sammai da kassai”. Suratul Bakara, aya ta: 117.Wato wanda ya kageta ba wai ya kwaikwaya daga wani ba, fadin Allah madaukakin sarki:﴿قُلْ مَا كُنْتُ بِدْعًا مِنَ الرُّسُلِ ٩﴾Ma’ana:“Ka ce; ban kasance sabo ba daga cikin Manzanni”. Suratul Ahkaf, aya ta:9.Wato ban kasance farkon wanda ya zo da sako daga wurin Allah ba zuwa ga bayinsa, ai manzanni masu tarin yawa sun gabace ni da zuwa da manzanci. Akan ce; wane ya fara bidi’a, idan ya zo da wata hanya da babu wanda ya riga shi. Shi kagar abubuwa ya kasu kashi biyu:Kashi Na Farko: Kaga a al’amuran yau-da-kullum, kamar sababbin kere-kere, wannan halasne.Kashi Na Biyu: Kagawa a cikin addini, to wannnan haramun ne, domin abinda asali a ibada shi ne; tsayawa tukunna (sai ance ka yi). Ma’aikin Allah ﷺ ya ce: “Duk wanda ya kirkira a cikin wannan al’amarin na mu abinda babu shi to an mayar masa”. Bukhari da Muslim ne suka ruwaito. A wata ruwayar: “Duk wanda ya aikata wani aiki da babu umarnin mu a kai to an mayar masa”. Bukhari da Muslim suka ruwaito.Nau’ukan kagowa (bidi’o’i).bidi’a a addini ta kasu kashi biyu:Nau’i Na Farko: bidi’a ta Magana da kuma kudirin zuci, kamar maganganun Jahamawa (jahamiyya) da Mu’utazilawa da Shi’a da dai sauran kungigyoyi da suke akan bata da kuma akidun su.Nau’i Na Biyu: bidi’o’i a cikin ibada, kamar bautawa Allah da wata ibadar da bai shar’anta ta ba, wannan ko ya kasu kashi-kashi.Kashi Na Farko: Abinda yake kasancewa a asalin ibada, kamar mutum ya farar da wata ibada wacce bata da wani asali a shari’a, kamar ya farar da wata sallah wacce ba shar’antacciya ba ko azumi wanda ba shar’antacce ba tun asali, ko kuma wasu bukukuwa wadanda ba shar’antattu ba kamar bukukuwan maulidi.Kashi Na Biyu: Abinda yake kasancewa na kari a ibadar da aka shar’anta, kamar mutum ya kara raka’a ta biyar a sallar azahar da la’asar misali.Kashi Na Uku: Abinda yake kasancewa na siffar gabadar da ibadar da take shar’antacciya ta yadda zai gabatar da ita a wata siffar ba shar’antacciya ba, wannanko kamar shar’antaccan zikiri da aka gabatar da shi da murya daya da rausayawa, haka kuma kamar tsanantawa kai a ibada har hakan ya kai ga fita daga karantarwar Ma’aikin Allahr.Kashi Na Hudu: Abinda yake kasancewa na kebanci wani lokaci domin gabatar da ibada wacce take shar’antacciya wacce shari’a bata kebanceba, kamar kebance ranar shabiyar ga Sha’aban da azumi daran kuma da salloli, (kada a manata) ai asalin azumi da sallar dare shar’antattune, saidai kebance shi da wani lokaci daga cikin lokuta yana da matukar bukatar dalili.Hukuncin bidi’a a cikin addini a dukkan nau’ukanta.Dukkan wata bidi’a a cikin addini haramunce kuma bata ce, saboda fadin Ma’aikin Allahr: “Ku kiyayi fararrun al’amura, domin dukkan abinda yake fararre to bidi’ane, kuma dukkanin bidi’a batace”. Abudawud da Tirmizi suka ruwaito. Da kuma fadinsa ﷺ: “Duk wanda ya farar a cikin wannan al’amarin na mu abinda babu shi to an mayar masa”. Bukhari da Abudawud suka ruwaito. A wata ruwayar kuma: “Duk wanda ya aikata wani aiki da ba mu muka umarce shi ba to an mayar masa”. Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi. Sai wadannan hadisai guda biyu suka yi nuni akan dukkan abinda aka farar a cikin addini to bidi’a ne, kuma dukkan bidi’a batace kuma ba’a karbarta. Abinda wannan yake nufi lalle bidi’o’i a cikin ibada da kuma akidah haramunne, saidai haramcin wani ya fi wani gwargwadon nau’in bidi’ar, daga cikinta akwai wacce take kafirci ce a bayyane, kamar yi wa kabarbura dawafi domin neman kusanci ga wadanda ke cikin kabarin, da gabatar da yanke-yanke da kuma alwashi, da kiran wadanda suke cikin kabarin, da ma neman agajin su, hakanan kuma kamar maganar manyan jahamiyyah da mu’utazila. Daga cikin (bidi’o’in) kuma akwai wadanda su tsani ne zuwa ga shirka, kamar yin gini a kabarurruka da yin sallah a kabari da yin addu’a a inda kabarin yake. Daga cikin (bidi’o’in) kuma akwai abinda yake fasikancine na akida, kamar bidi’ar Khawarij da Kadariyya da Murji’ah a maganganunsu da akidunsu wadanda suke sabawa dalilai na shari’a. Daga cikin (bidi’o’in) kuma akwai wadanda suke laifi ne, kamar bidi’ar kin yin aure, da kuma azumi tare da tsayuwa a rana, da dandaka domin yanke sha’awar jima’i.Fadakarwa: Dukkan wanda ya raba bidi’a zuwa bidi’a mai kyau da mara kyau to wannan ya yi kuskure, kuma ya sabawa fadin Ma’aikin Allah ﷺ“Dukkan bidi’a batace”. Abudawud ya ruwaito shi. Domin Ma’aikin Allah ﷺ ya yi hukunci akan bidi’o’i da cewa bakidayanta bata ce, shi kuma wannan yana cewa ba kowacce bidi’a ba ce bata! Har ma akwai wata bidi’a wai mai kyau. Babban malami Ibnu Rajab yana cewa a sharhin da ya yi wa Arba’una Hadis: To fadin shi ﷺ: “Dukkan bidi’a batace”. Yana cikin tararrun maganganu da babu wani abu da zai fita daga ciki, kuma babban tushe ne mai girma daga cikin tushen addini, kuma ya yi kama da fadinsa ﷺ: “Duk wanda ya farar a cikin al’amarin nan na mu abinda babu shi to an mayar masa”. To dukkan wanda ya farar da wani abu kuma ya jingina shi ga addini, alhali kuma ba shi da wani asali a addini to za’a mayar masa kuma bata ne. addini kuma ya barranta da shi, abin daidai ne yana cikin abinda ya shafi akida ne ko ayyuka ko kuma zantuttuka na zahiri ne ko na badini. Nan maganar Ibnu Rajab ta kare. Wadannan fa ba su da wata hujja na cewar akwai wata bidi’a mai kyau saidai maganar Umar t a sallar tarawihi; “Madalla da wannan bidi’ar”. Suka kuma ce; Ai wadansu abubuwa sun faru, wadanda yake magabata ba su yi inkarin su ba, kamar hada Alkur’ani a littafi guda, da kuma rubuta Hadisi da hada shi. To amsar da za’a bayar akan haka ita ce; Lalle wadannan al’amura suna da asali a addini ba kagaggu ba ne. maganar Umar t ‘madalla da wannan bidi’ar’. Yana nufin bidi’a agundarin bakin Larabci ba wai ma’anarta a shara’a ba, kuma duk abinda ya kasance yana da asali a shari’a da za’a koma masa, to idan akace shi bidi’a ne to anan ana nufin bidi’a a yaran Larabci ba didi’a a yaran addini ba, domin bidi’a a shar’ance shi ne abinda ba shi da asali a shari’a da za’a iya komawa zuwa gare shi. Hada Alkur’ani da aka yi a littafi guda yana da asali a shari’a, domin Ma’aikin Allah ﷺ ya kasance yana umartar a rubuta Alkur’ani, saidai ya kasance arubuce ne daban-daban sai sahabbai –Allah ya kara musu yarda- suka hada shi a littafi guda, domin a kare shi. Ita kuma sallar tarawihi hakika Annabi ﷺ ya sallace ta tare da sahabbansa wasu darare, kuma bai fito ba daga karshe domin gudun kada a faralanta ta akan su, sai sahabbai suka ci gaba da sallatar ta daban-daban a wawware a lokacin Annabi ﷺ da bayan rasuwarsa har zuwa lokacin da Umar dan Khaddab t ya hada su a bayan liman guda, kamar yadda suka kasance a bayan Annabi ﷺ a tare da shi, wannan ko ba bidi’a ba ne a addini. Rubutun Hadisi yana da asali a addini, domin hakika Annabi ﷺ ya yi umarni da rubuta wasu hadisai ga wasu cikin sahabbansa a lokacin da aka nemi hakan, kuma babban abinda aka ji wa tsoro na rashin rubuta shi a zamanin Annabi ﷺ shi ne gudun kada a hada shi da Alkur’ani alhalin ba Alkur’ani ba ne, to alokacin da Ma’aikin Allah ﷺ ya rasu sai wannan abin tsoron ya kau, domin Alkur’ani ya cika an kuma haddaceshi kafin rasuwar Ma’aikin Allah ﷺ, sai al’ummar musulmi suka rubuta Hadisi bayan haka domin ba shi kariya daga bacewa, to Allah ya saka musu da alheri akan wannan aiki da suka yi wa Musuluunci da kuma Musulmai, yadda suka kare littafin Ubangijinsu da kuma sunnar Annabinsu ﷺ daga bacewa da kuma wasan masu wasa. Fasali Na Biyu:Bayyanar bidi’o’i a rayuwar musulmai, anan akwai abubuwa biyu:Abu Na Farko: Lokacin bayyanar Bidi’a:Shehul Islam Ibnu Taimiyah –Allah ya yi masa rahama ya ce: Ka sani! Lalle daukacin bidi’o’i da suke da alaka da ilimomi da kuma ibada, abin sani kawai sun faru ne a cikin al’umma a karshen Halifofi masu shiryarwa, kamar yadda Annabi ﷺ ya bada labara, inda ya ce: “Duk wanda ya rayu daga cikinku da sannu zai ga sabani mai yawa, to na umarceku da Sunna ta da kuma Sunnar Halifofi masu shiryarwa kuma shiryayyu”. Tirmizi da Abudawud suka ruwaito. Farkon bidi’ar da ta bayyana ita ce bidi’ar ‘Kadar’ da kuma bidi’ar ‘Murji’a’, da bidi’ar Shi’a da kuma Khawarij, a lokacin da aka sami rabuwar kai bayan kashe sayyidina Usman sai bidi’ar Haruriyyah ta bayyana, sannan a karshen zamanin sahabbai sai Kadariyyah ta faru a karshen lokacin Abdullahi dan Umar da Abdullahi dan Abbas da Jabir da makamantansu, Murji’a kuma ta faru kusa da haka. Amma Jahamiyyah to ita ta bayyana ne akarshen zamanin Tabi’ai bayan rasuwar Umar dan Abdul’aziz, hakika an ruwaito cewa ya yi gargadi akan su, kuma bayyanar Jaham ta kasance ne a Khurasan a zamanin Khalifa Hisham dan Abdulmalik. Wadannan bidi’o’in sun bayyana ne a karni na biyu, kuma sahabbai na nan sun kuma yi inkarin hakan ga masu su, sannan sai bidi’ar Mu’utazilanci, futuntunu suka auku tsakanin al’ummar Musulmi, banbance-banbancen akida ya bayyana, da kuma karkata zuwa ga bidi’o’i da kuma son zuciya, bidi’ar sufanci ta bayyana, da kuma bidi’ar gini akan kabari bayan karnoni masu daraja, kuma hakan abun yake aduk lokacin da aka kara nisa (da zamani Annabta) sai bidi’o’i su karu kuma su nau’anta. Abu Na Biyu: Wurin da bidi’ar ta bayyana:Kasashen Musulunci sun sha banban wurin bayyanar bidi’a a cikin su, Shehul Islma Ibnu Taimiyah ya ce: Domin manyan kasashe wadanda sahabban Ma’aikin Allah ﷺ suka zauna a ciki, kuma ilimi da Imani suka kafu a cikinsu biyar ne: Harami biyu (Makkah da Madina) da Iraki biyu (Basrah da Kufah) da kuma Sham, daga nan ne Alkur’ani da Hadisi da Fikhu da kuma ibada suka fita, da sauran abinda yake bin hakan na al’amuran musulunci, kuma daga wadannan birane ne bidi’o’i a tushen addini suka bayyana in banda birnin Madinan Manzan Allah ﷺ. To ita Kufah Shi’anci da Murji’anci daga nan ya fita kuma ya yadu bayan hakan a wasu garuruwa. Basrah kuma masu inkarin Kaddara da kuma Mu’utazilanci daga nan ya fita, da mummunan aiki ya kuma yadu bayan hakan a wasu garuruwa. Sham kuma anan Nasibawa suke da kuma Kadariyyah. Amma shi kuma Jahamiyanci ya bayyana ne ta bangaren Khurasan shi ne kuwa mafisharrin bidi’a. Bayyanar bidi’o’i ya kasance ne gwargwadon nisan wurin da garin Annabta, a lokacin da aka samu rabuwarkai bayan kashe sayyidina Usman sai kuma bidi’ar Haruriyyah ta bayyana. Amma birnin Madina ya kasance a tsaftace babu bayyanar wadannan bidi’o’in, dudda akwai wadanda suke boye da su, sai suka kasance wulakantattu kuma wadanda ake zargi, domin akwai mutane da suke da akidar Kadariyya da wasunsu, saidai sun kasance an fi karfin su sai suka kasance akaskance, sabanin Shi’anci da Murji’anci da yake a Kufah, da kuma Mu’utazilanci da bidi’o’in ibada da suke a Basrah, sai kuma Nasibanci da yake a Sham, wannan ko ya kasance a bayyane yake (a can wuraran). Hakika ya tabbata a Hadisi ingantacce daga Annabi ﷺ cewa lalle Jujal ba zai shigeta ba (Madina), kuma ilimi bai gusheba hakanan ma Imani bai gushe a bayyane har zuwa zamanin almajiran Malik, su ko suna cikin karni na hudu. Amma lokutannan uku masu falala to babu wata bidi’a da ta kasance a bayyane kwatakwata a Madinar Annabi ﷺ, kuma babu wata bidi’a a tushen addini da ta fita daga Madina kwata-kwata, kamar yadda ta fita daga sauran birane.Sububban bayyanar bidi’o’i. Yana daga cikin abinda babu kokwanto a kai lalle ruko da littafin Allah da kuma Sunnah shi ne tsira daga afkawa bidi’o’i da kuma shiga bata, Allah madaukakin sarki yana cewa:﴿وَأَنَّ هَذَا صِرَاطِي مُسْتَقِيمًا فَاتَّبِعُوهُ وَلَا تَتَّبِعُوا السُّبُلَ فَتَفَرَّقَ بِكُمْ عَنْ سَبِيلِهِ ذَلِكُمْ وَصَّاكُمْ بِهِ لَعَلَّكُمْ تَتَّقُونَ١٥٣﴾Ma’ana:“Kuma lalle wannan (Alkur’ani) tafarki na ne mikakke ku bi shi, kada ku bi wadansu hanyoyi sai su raba ku daga barin hanya ta”. Suratul An’ama, aya ta:153. Hakika kuma Annabi ﷺ ya yi bayanin a cikin abinda Abdullahi dan Mas’ud t ya ruwaito, ya ce: “Ma’aikin Alah ﷺ ya yi mana zane, zane na hakika sa kuma ya ce: “Wannan ita ce hanyar Allah, sannan sa ya zana wasu hanyoyi ta damansa da kuma ta hagunsa, sannan sai ya ce; Wadannan hanyoyin akan kowacce hanya shaiddani ne, yana kira zuwa gareta. Sannan sai ya karanta:﴿وَأَنَّ هَذَا صِرَاطِي مُسْتَقِيمًا فَاتَّبِعُوهُ وَلَا تَتَّبِعُوا السُّبُلَ فَتَفَرَّقَ بِكُمْ عَنْ سَبِيلِهِ ذَلِكُمْ وَصَّاكُمْ بِهِ لَعَلَّكُمْ تَتَّقُونَ١٥٣﴾Ma’ana:“Kuma lalle wannan (Alkur’ani) tafarki na ne mikakke ku bi shi, kada ku bi wadansu hanyoyi sai su raba ku daga barin hanya ta. Wannan (bayanin da aka yi muku) wasiyya ce aka yi muku ita domin ku ji tsoron (Allah)”. Suratul An’ama, aya ta: 153. Duk wanda ya kau-da-kai daga littafin Allah (Alkur’ani) da Sunnah to ko hanyoyi masu batarwa sai sun ja shi, da kuma bidi’o’i wadanda suke fararru.A dunkule sabubban da suka sa bidi’o’i suka bayyana sune kamar haka:Jahiltar hukunce-hukuncen addini, bin san-zuciya, makalkalewa wadansu ra’ayoyi da wasu mutane, kamanceceniya da kafirai da kuma kwaikwayonsu. Za mu dauki wadannan domin yin bayani akan su: (1) Jahiltar hukunce-hukuncen addini. A duk lokacin da zamani ya yi nisa, kuma mutane suka yi nesa da sakon Annabta to ilimi zai zama kadan, kuma jahilci zai yadu, kamar yadda Annabi ﷺ ya bada labarin haka: “Duk wanda ya rayu daga cikinku to da-sannu zai ga sabani mai yawa”. Tirmizi da Abudawuda suka ruwaito. Da kuma fadinsa ﷺ: “Lalle Allah ba ya danke ilimi da ze fizge shi daga bayi, saidai yana karbe ilimi ne ta hanyar karbe malamai, har zuwa lokacin da babu wani malami da ya rage, sai mutane su riki shugabanni jahilai, sai a tambaye su sai su yi fatawa bada ilimi ba, su bata su kuma batar”. Bukhari da Muslim ne suka ruwaito. Babu abinda yake yakar bidi’o’i sai ilimi da kuma malamai, to idan aka rasa ilimi da malamai an baiwa bidi’o’i damar su bayyana kuma su watsu masu ita kuma su yi ta walwala.(2)Bin san-zuciya. Duk wanda ya kau da kai daga littafin Allah da Sunnah to son zuciyarsa zai bi, kamar yadda Allah madaukakin sarki ya fada: ﴿فَإِنْ لَمْ يَسْتَجِيبُوا لَكَ فَاعْلَمْ أَنَّمَا يَتَّبِعُونَ أَهْوَاءَهُمْ وَمَنْ أَضَلُّ مِمَّنِ اتَّبَعَ هَوَاهُ بِغَيْرِ هُدًى مِنَ اللَّهِ إِنَّ اللَّهَ لَا يَهْدِي الْقَوْمَ الظَّالِمِينَ٥٠﴾Ma’ana:“To idan har ba su amsa maka ba, to ka sani kawai suna bin son zuciyarsu ne, babu ko wanda ya bata kamar wanda ya bi son zuciyarsa ba tare da wata shiriya ba daga wurin Allah”. Suratul Kasas, aya ta:50. Kuma Allah madaukakin sarki ya ce:﴿أَفَرَأَيْتَ مَنِ اتَّخَذَ إِلَهَهُ هَوَاهُ وَأَضَلَّهُ اللَّهُ عَلَى عِلْمٍ وَخَتَمَ عَلَى سَمْعِهِ وَقَلْبِهِ وَجَعَلَ عَلَى بَصَرِهِ غِشَاوَةً فَمَنْ يَهْدِيهِ مِنْ بَعْدِ اللَّهِ أَفَلَا تَذَكَّرُونَ٢٣﴾Ma’ana:“Ka ba ni labarin wanda ya riki son zuciyarsa abinbautarsa, kuma Allah ya batar da shi akan ilimi kuma ya rufe jinsa da kuma zuciyarsa, ya kuma sanya yana a ganinsa, to waye zai shiryar da shi bayan Allah?. Suratul Jathiya, aya ta: 23. Bidi’o’i saka ce son zuciya wacce ake bi.(3) Makalkalewa wadansu ra’ayoyi da wasu mutane.makalkalewa wadansu ra’ayoyi da wasu mutane shi ne abinda yake shamakancewa tsakanin mutum da kuma bin dalili, Allah madaukakin sarki ya ce:﴿وَإِذَا قِيلَ لَهُمُ اتَّبِعُوا مَا أَنْزَلَ اللَّهُ قَالُوا بَلْ نَتَّبِعُ مَا أَلْفَيْنَا عَلَيْهِ آبَاءَنَا أَوَلَوْ كَانَ آبَاؤُهُمْ لَا يَعْقِلُونَ شَيْئًا وَلَا يَهْتَدُونَ١٧٠﴾Ma’ana: “Kuma idan aka ce da su; ku bi abinda Allah ya saukar, sai su ce a’a, muna bin abinda muka samu iyayan mu ne akai”. Suratul Bakara, aya ta: 170. To wannan shi ne sha’anin dukkan wadanda suke makalkale a yau, kamar wasu daga cikin mabiya mazahabin sufaye da masu bautar kabari idan aka kira su su bi littafin Allah da Sunnar Ma’aiki ﷺ, da kuma watsi da duk abinda suke akai wanda ya sabawa littafin na Allah da kuma Sunnar ta Ma’aikin Allah, sai su yi ta kafa hujja da mazahabobinsu da kuma shehunan su da iyayansu da kuma kakanninsu. (4) Kamanceceniya da kafirai. Yana kuwa daga cikin mafi tsananin abinda yake shigar da mutum bidi’a, kamar yadda yake a Hadisin Abuwakid Allaisi, ya ce: “Mun fita tare da Ma’aikin Allah ﷺ zuwa Hunaini, a lokacin muna sababbin musulunta, su kuma mushirikai suna da magarya da suke lizimtarta kuma suke rataye makamansu, ana kiranta magaryar neman sa’a. Sai muka wuce wata magarya, sai muka ce ya Ma’aikin Allahr! Muma ka sanya mana magarya kamar yadda suke da magarya, sai Ma’aikin Allah ﷺ ya ce: Allahu Akabar, lalle haka hanyar take, kuka fada. Na rantse da wanda raina yake a hannunsa kamar yadda Banu Isra’ila suka fadawa Annabi Musa:﴿ اجْعَلْ لَنَا إِلَهًا كَمَا لَهُمْ آلِهَةٌ قَالَ إِنَّكُمْ قَوْمٌ تَجْهَلُونَ١٣٨﴾Ma’ana:“Ka sanya mana abin bauta kamar yadda suke da abin bauta, ya ce; Lalle ku mutane ne masu jahiltar (Ubangiji)”. Suratul A’araf, aya ta: 138. “Hakika za ku hau hanyar wadanda suka zo kafin ku”. Tirmizi ne ya ruwaito. A wannan Hadisin akwai cewa lalle kamanceceni da kafirai shi ne abinda ya dauki Banu Isra’ila akan su wannan neman da yake mummuna, shi ne kuma da a sanya musu wani abin bauta da zasu dinga bauta masa, shi ne kuma abinda ya dauki wasu daga cikin sahabban Ma’aikin Allah ﷺ da su tambaye shi akan ya sanya musu wata bishiya da za su dinga neman albarka a wurinta koma bayan Allah, wannan ko shi ne abinda yake aukuwa a yau, domin mafi yawan musulmai sun kwaikwayi kafirai a ayyukan bidi’a da shirka, kamar bukukuwan mauludi, da ware wasu kwanuka ko makwanni domin yin wasu ayyuka kebantattu, ko tarurruka ta sanadiyyar addini ko tuna wasu abubuwa, da sanya mutum-mutumi, da kafe su domin tunawa, da bidi’o’i a wurin jana’iza, da gini akan kabari da wanin haka. **** **** **** Fasali Na Uku:Matsayar al’ummar musulmi dangane da ‘yanbidi’ah, da kuma tsarin Ahlussunnah Wal Jama’a dangane da yi musu raddi. Ahlussuna Wal Jama’ah ba su gushe ba suna mayar da martini ga ‘yan-bidi’a, suna kuma yi musu inkarin bidi’o’in na su suna kuma hana su ci gaba da yenta, yanzu ga misalai akan hakan:(a) Daga Maman Darda’a (Ummu Darda’a) ta ce: Abu Darda’u ya zo wurina cikin fushi, sai nace masa; Me ya sameka? Sai ya ce: Wallahi ban san su da wani abu ban a al’amarin (Annabi) Muhammad ﷺ saidai su suna yin salla ne gaba daya.(b) Daga Umar dan Yahya ya ce: na ji baba na yana cewa shi ma daga babansa ya ce; Mun kasance muna zama a kofar gidan Abdullahi dan Mas’ud t kafin sallar asubah, to idan ya fito sai mu tafi tare da shi masallaci, sai Abu Musa Al’ash’ari ya ce; Ko baban Abdurrahman ya fito kuwa ? (wato Abdullah dan Mas’udu), sai mukace; a’a – sai ya zauna tare da mu har ya fito-, lokacin da ya fito sai muka tashi baki-daya zuwa wurinsa, sai Abu Musa Al’ash’ari ya ce; ya baban Abdurrahman ni fa dazu na ga wani abu a masallaci abinda yake ban yarda da shi ba, amma dai banga wani abu ba –الحمد لله – saidai alheri, sai Abdullahi dan Mas’ud yace menene shi? Sai Abu Musa ya ce: in Allah ya sa mun je zaka gani, sai ya ce: Na ga mutane a masallaci suna zaune sun yi halka suna sauraron sallah, a kowacce halka akwai mutum guda a hannayansu kuma akwai tsakuyoyi sai mutumin ya ce; Ku yi kabbara dari, sai su yi kabbara dari. Sai ya ce ku yi hailala dari, sai su yi hailala dari. Sai ya ce; ku yi tasbihi dari, sai su yi tasbihi dari, sai (Abdullahi dan Mas’ud ya ce da Abu Musa) me kace da su? Sai ya ce; bance komai ba domin sauraron me zaka ce, ko me zaka yi umarni, baka umarce su su lissafa munanan ayyukan su ba, kuma ka amintar da su don kada wani abu na kyakkyawan aikinsu ya baci. Sannan sai ya tafi, sai muma muka tafi tare da shi, har ya je wata halka daga cikin wadannan halkokin ya kuma tsaya a kanta, sai ya ce; me kuma nag a kuna aikatawa? To ku lissafa munanan ayyukan ku, ni kuma na amince muku don kada wani kyakyyawan aikinku ya lalace, tir da ku! Ya ku al’ummar (Annabi) Muhammad ﷺ ya kuka yi gaggawar halaka? Ga sahabbansa nan masutarin yawa, ga tufafinsa basu lalace ba, ga koransa nan ba su karye ba, ina rantsewa da wanda raina yake a hannunsa lalle ku kuna wani addini da shi ya fi zama shiriya akan addinin (Annabi) Muhammadr, ko kuma kun bude kofar bata, sai suka ce; wallahi ya baban Abdurrahman ba abinda muka yi nufi sai alheri, sai ya ce: da yawa akwai mai neman alheri kuma bai same shi ba. Lalle Ma’aikin Allah ﷺ ya karantar da mu lalle wadansu mutane za su dinga karanta Alkur’ani ba ya wuce wuyansu, ina rantsuwa da Allah ban sani ba ko mafi yawansu daga cikinku ne, sannan sai ya juya ya bar su. Sai Umar dan Salama ya ce: munga wadannan baki-dayan suna sukar mu da mashi a ranar Nahrawan suna tare da Khawarijawa.(c) Wani mutum ya zo wurin Imamu Malik dan Anas Allah ya yi masa rahama, sai ya ce: daga ina zan yi harami? Sai ya ce: Daga mikatin da Ma’aikin Allah ﷺ ya sanya kuma ya yi harami daga nan, sai mutumin ya ce: Amma ni zan yi harami ne daga inda ya fi shi nisa?, sai Malik ya ce; Niko ba na ganin dacewar hakan? Sai ya ce: mekake kyama akan hakan? Sai ya ce: ina ji maka tsoron fitina, sai ya ce: wacce fitina kuma a wurin neman Karin alheri?! Sai ya ce, to Allah madaukakin sarki yana cewa:﴿ فَلْيَحْذَرِ الَّذِينَ يُخَالِفُونَ عَنْ أَمْرِهِ أَنْ تُصِيبَهُمْ فِتْنَةٌ أَوْ يُصِيبَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ٦٣﴾Ma’ana:“To wadanda suke sabawa umarninsa (ﷺ) su kiyaye kada wata fitina ta same su ko kuma azaba mairadadi ta same su”. Suratun Nur, aya ta:73. To wacce fitina ce mafi girma kamar ka kebance wata falala wacce Ma’aikin Allah ﷺ bai kebanceta ba. To wadannan wasu misalai ne, kuma malamai ba su gushe ba suna yi wa ‘yan-bidi’a inkarin a kowanne lokaci, dukkan godiya ta tabbata ga Allah.2. Tsarin Ahlussunnah Wal Jama’a dangane da yi musu raddi.Tsarinsu akan haka ya ginu ne akan littafin Allah da kuma Sunnah, shi ne kuma tsari mai kosarwa, ta yadda suke kawo shubuhohin ‘yan-bidi’a suke kuma warware su. Suke kuma kafa hujja da Alkur’ani da Hadisi akan wajibcin riko da sunnoni da kuma hani akan aikata bidi’oi da fararrun abubuwa, hakika kuma malamai sun wallafa littattafai masu yawa akan haka, sun yi raddi akan akidun Shi’a da Khawarij da kuma Jahamiyyah da Mu’utazila da Asha’ira a maganganunsu na bidi’a akan abinda ya shafi asalin Imani da kuma akida, sun wallafa littattafai na musamman akan haka, kamar yadda Imam Ahmad dan Hanbali ya wallafa “Arraddu Alal Jahamiyyah” (wato raddi akan akidun Jahamiyawa), kuma wasu ma daga cikin jagorori na musulunci sun wallafa akan hakan, kamar; Usman dan Sa’id Addarimi, kamar kuma yadda yake a littattafan Shehul Islam Ibnu Taimiya, da almajirinsa Inbu Kayyim da kuma Sheikh Muhammad dan Abdulwahhab da wasunsu, na abinda ya shafi yin raddi akan kungiyoyin masu bautar kaburbura da kuma sufanci, amma littattafai na musamman akan maida martini ga ‘yan-bidi’a to suna da yawa, ga wasu daga cikinsu domin bada misali daga cikin littattafan magabata:1. Littafi “I’itisam” (الاعتصام) na Imamus Shatibi.2. Littafin “Iktidha’us siratil Mustakim” (اقتضاء الصراط المستقيم ) na Shehul Islam Ibnu Taimiya, hakika kuma ya ware juzu’i guda babba domin maida martini ga ‘yan-bidi’a.3. Littafi “Inkarul Hawadith Wal Bida’u) (إنكار الحوادث والبدع) na Ibnu Waddhah.4. Littafin “Alhawadith Wal Bida’i” (الحوادث والبدع)na Dardushi.5. Littafin “Aba’ithu Ala Inkaril Bida’i Wal Hawadith (الباعث على إنكار البدع والحوادث)na Abu Shama.Daga cikin littatafai na wannan zamanin kuma akwai:1. Littafin “Al’ibda’u Fee Madharril Libtida’i” (الإبداع في مضار الابتداع) na Sheikh Aliyu Mahfuz.2. Littafin “Assunan Wal Mubtadi’at Almuta’allika Bil Azkar Wassalawat” (السنن والمبتدعات المتعلقة بالأذكار والصلوات) na Sheikh Muhammad dan Ahmad Shkairi Hawamidi.3. Littafin “Risalatut Tahzir Minal Bida’i” (رسالة التحذير من البدع ) na Sheikh Abdul’aziz dan Baz.Malamai basu gushe ba cikin taimakon Allah suna inkarin bidi’oi, kuma suna maida martini ga ‘yan-bidi’a kama daga jaridu ko mujalla ko kuma gidajan radiyo, da kuma hudubobin juma’a da tarurruka da laccoci, wanda yake yana da matukar tasiri a wurin wayar da kan al’ummar musulmi, da kuma yadda ake yi wa bidi’oi kwab-daya da yadda ake murkusheta.**** ***** ***** Fasali Na Hudu: Magana akan missalan bidi’o’i a wannan lokacin.1. Bikin Mauludin Annabi ﷺ2. Neman albarka da wurare da kayayyaki da matattu da makamantan su.3. Bidi’o’i a fagen ibada da kuma neman kusanci zuwa ga Allah.Bidi’o’in wannan zaman kuma suna da yawa, lura da yadda lokacin ya zo daga karshe, kuma ga karancin ilimi, sannan ga yawan masu da’awa zuwa ga bidi’o’in da kuma sama wa dokokin Ubangiji, da gaggawar son kamanceceniya da kafirai a al’adunsu da kuma dabi’unsu, domin tabbatar da maganar Ma’aikin Allah ﷺ da ya ce: “Hakika za ku bi hanyar wadanda suka zo kafin ku”. Bukhari da Muslim ne suka ruwaito. 1. Bikin Mauludin Annabi ﷺ a watan Rabi’ul Awwala.Wannan kuwa kamanceceniya ce da Nasara a abinda suke yin a bukukuwan kirsimeti, sai ka ga jahilan musulmi ko kuma malamai masu batarwa suna biki a watan Rabi’ul Awwal a kowacce shekara saboda zagayowar haihuwar Ma’aikin Allah Annabi Muhammad ﷺ, daga cikin su akwai wadanda suke wadannan bukukuwan a masallatai, daga cikin su kuma akwai wadanda suke yi a gidaje, ko kuma wasu wurare da aka kebe domin hakan, sai mutane masu tarin yawa su halarta daga cikin gamagarin mutane, suna yin hakan domin kwaikwayon Nasara a bidi’arsu ta taro domin bikin haihuwar Almasihu (Annabi Isa) Alaihissalam, kuma mafi yawan wadannan bukukuwa babban abinda zaka gane bidi’antakarsa da kuma kamanceceniya da Nasara ba ya rabuwa da shirka da munanan ayyuka, kamar rera wake wadda a ciki akwai wuce iyaka akan hakkin Ma’aikin Allah ﷺ, har ya kai yadda ake kiranshi koma-bayan Allah, da kuma neman agajinsa, hakika kuwa Annabi ﷺ ya hana wuce iyaka a wurin yabon shi, sai ya ce: “Kada ku kambamani kamar yadda Nasara suka kambama dan Maryam (Annabi Isah), abin sani kawai ni bawa ne, ku ce; Bawan Allah kuma Manzan shi”. Bukhari da Muslim suka ruwaito.Ma’anar: wuce iyaka, shi ne ketare iyaka wurin yabonsa, saudayawa ma sukan kudurce cewa wai hakika Ma’aiki ﷺ yana zuwa wurin tarurrukan na su, yana kuma daga cikin munana ayyukan da suke kasancewa tare da wadannan bukukuwa wakoki da ake rerewa da murya daya da kuma buga ganguna, da wanin haka wadanda suke ayyukka ne na zikiran sufaye wadanda suke na bidi’a, wani lokacin ma akan sami cakuduwa maza da mata, abinda yake kawo fitintinu har ya kai ga afkawa alfasha. Ko da ace wadannan bukukuwan sun kasance babu wadannan munanan ayukkan kawai ya takaitune akan a taru a ci abinci a nuna farin ciki – kamar yadda suke cewa- to fa bidi’ane wacce aka kaga ((kuma dukkanin bidi’a bat ace)). Kuma dadin-dadawa hakan wani tsani ne da zai habbaka har ya kai ga an samu a wannan taron irin abinda ake samu a sauran tarurrukan na munanan ayyuka. Kuma mun ce: bidi’ane, domin ba shi da wani asali a littafin Allah da kuma Sunnah, hakanan ba shi daga cikin ayyukan magabata nakwarai, da kuma shekaru masu falala, kuma abin sani kawai ya faru ne daga baya, bayan karni na hudu daga hijira, wadanda kuma suka farar da shi su ne ‘yan-shi’a, babban malamin nan Iman Abu Hafsa tajuddin Alfakihani –Allah ya yi masa rahama-: bayan haka, hakika tambayoyi sun maimaitu daga jama’a masu albarka dangane da taron da mutane suke yi a watan Rabi’ul Awwal, suna kuma kiranshi da mauludi, wai shin yana da asalai a addini? Kuma suke neman bayyanannan bayani akan hakan tare kuma da fayyace shi a hakika, to sai na ce –ina neman dacewa daga Allah-: ban san inda wannnan mauludi yake da asali ba ko a littafin Allah ko kuma a Sunnar Ma’aiki ﷺ, kuma ba’a ruwaito yin shi ba daga wani malami daga cikin malaman wannan al’ummar wadanda suke su ne abin koyi a addini, wadanda suke ruko da karantarwar magabata, kawaidai shi (mauludi) bidi’ane wasu suka kirkiro, kuma wata dama ce da masu bin son rai su ke dukiyar mutane kawai. Shehul Islam Ibnu Taimiya –Allah ya yi masa rahama- ya ce: Haka nan kuma abinda wasu mutane suka kirkiro, kodai don koyi da Nasara a bikin haihuwar Annabi Isa alaihissalam, ko kuma son Annabi ﷺ da girmama shi, duk wanda ya riki mauludin Annabi ﷺ wani biki na duk shekara tare da sabanin da aka yi akan ranar haihuwar ta sa, domin hakikanin sa magabata ba su aikata shi ba, kuma da ya kasance alheri ne tsantsa kuma abu ne da ake komawa ga reshi to da magabata – Allah ya kara musu yarda- da sun fi mu cancata da shi, domin su sun fi kowa son Annabi ﷺ da kuma girmama shi sama da mu, su sun fi kowa son alheri, abin sani kawai son shi da girmama shi yana kasan cewa ne akan yi mi shi biyayya da binshi da kuma bin umarninsa, da rayar da sunnar sa a zahiri da kuma badini, da kuma yada abinda aka aiko shi da shi da yin jihadi akan hakan da zuciya da hannu da kuma harshe, domin wannan itace hanyar wadanda suka gabata na farko daga cikin wadanda suka yi hijira da kuma mutanan Madina, da kuma dukkanin wadanda suka bi su da kyautatawa’. Nan maganar ta kare. Hakika an wallafa littattafai da makaloli a da da yanzu akan inkarin wannan bidi’ar, wannan ko alamace akan kasancewarsa bidi’a da kuma kamanceceniya (da wasu), domin yana kuma sanya yin wasu mauludan daban, kamar mauludan waliyyai da shehunnai da kuma wasu jagorori, sai kofofin sharri masu yawa su bude. 2. Neman albarka da wurare da kayayyaki da mutane rayayyu da matattu. Yana daga kagaggun bidi’o’i meman albarka da halittu, shi ma wannan wani nau’ine na maguzanci, kuma wata hanyace da ‘yankore suke tara kudade daga hannun mutane. Shi neman albarka shi ne tabbatuwar alheri a wani abu da kuma karuwarsa, neman tabbatuwar alheri da kuma karuwarsa to kawai yana kasancewa ne daga wanda yake mallakar hakan kuma yake da iko akan hakan, shi ne kuwa Allah madaukakin sarki, domin shi ne wanda yake saukar da alheri yake kuma tabbatar da shi, amma wanda aka halitta to shi ba shi da ikon bayar da albarka da kuma samar da ita haka nan ba shi da ikon wanzar da ita da kuma tabbatar da ita. To meman albarka da wurare da kuma suture da mutane rayayyu ko matattu bai halatta, domin hakan shirka ne, idan ya kudurce hakan yana bayar da albarka ko kuma hanyace ta shirkar idan ya kudurce hakan yana karata, taba shi da shafarshi kuma cewar sababi ne na samar da ita daga wurin Allah. Amma abinda sahabbai suka kasance suna aikatawa na neman albarka da gashin kan Annabir da kuma yawunshi da ma duk abinda ya fita daga jikinshi –kamar yadda bayani ya gabata- to wannan ya kebantune da shi ﷺ a lokacin yana raye, yana nan a tsakanin su, ta yadda sahabbai ba su kasance suna neman albarka da dutsansa ba ko da kabarinsa ba bayan rasuwarsa. Haka kuma ba su kasance suna nufatar wuraran da ya kasance ya yi sallah a wurin ba ko kuma ace ya zauna ba domin neman albarka. Hakanan kenan wuraran waliyyai shi ya fi (cancantar rashin neman albarka ko kabarin su ba), kuma su sahabbai ba su kasance suna neman alabarka da salihan bayi ba, kamar Abubakar da Umar da wasunsu da sauran manyan sahabbai ba su yi hakan alokaci suna raye haka kuma ba su yi bayan mutuwarsu ba. Kuma ba su kasance suna tafiya kogwan hira ba domin su yi sallah ba ko don su yi addu’a ba, kuma ba su kasance suna tafiya dutsen durusina’a ba, wanda Allah ya yi Magana da (Annabi) Musa ba, domin su yi sallah ba ko domin su yi addu’a ba, ko kuma zuwa wasu wurare ko duwatsu ba wadanda ake cewa akwai wuraran Annabawa a wurin ba ko kuma wanin su. Ko kuma zuwa wurin wani kabari ginanne na Annabi daga cikin Annabawa ba, kuma dai lalle wurin da Annabi ﷺ ya kasance yana yin sallah a wurin a birnin Madinar Annabi ﷺ a koda-yaushe babu wani daga cikin magabata da yake shafa shi ko yake sunbartar shi ba, hakanan kuma wurin da ya yi sallah a shi a birnin Makkah ko kuma wasu wuraran ba, to idan ya kasance wurin da yake takawa da kafafuwansa masu daraja kuma ya yi sallah a wurin ba’a shar’anta wa al’ummar sa ba su shafa ba ko su sunbanta ba, to yaya zai kasance ace waninsa ya yi sallah a wurin ko kuma ya kwanta, domin sunbantar wani abu anan da kuma shafar sa ai hakika malamai sun sani cewa wannan ba shi daga cikin shari’ar Annabi ﷺ (shi yasa basu kawo hukunce-hukuncen hakan a cikin littattansu ba). 3. Bidi’o’i a fagen ibada da kuma neman kusanci zuwa ga Allah.Bidi’o’in da aka farar a fagen ibada kuma a wannan zamanin suna da yawa, kuma abinda yake asali a ibada shi ne tsayawa tukunna (sai an ce ka yi), domin ba abinda ake shar’anta shi a ibada saida dalili, to dukkanin abinda dalili bai yi nuni akan shi ba to bidi’a ne, saboda fadin sa ﷺ“Duk wanda ya aikata wani aiki da babu umarnin mu akai to an mayar masa”. Bukhari da Muslim suka ruwaito. Ibadun da ake yinsu a yau wadanda babu wani dalili akan su suna da yawa, daga ciki akwai:Bayyana niyyah a sallah, kamar ya ce; Na yi niyyar yin sallah kaza da kaza domin Allah, to wannan bidi’ane domin ba shi daga cikin karantarwar Annabi ﷺ, ko saboda Allah madaukakin sarki ya ce:﴿قُلْ أَتُعَلِّمُونَ اللَّهَ بِدِينِكُمْ وَاللَّهُ يَعْلَمُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْضِ وَاللَّهُ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيمٌ١٦﴾Ma’ana:“Ka ce; yanzu kuna sanar da Allah addininku ne? Allah yana sane da abindake cikin sammai da kuma abindake cikin kassai, kuma Allah masani akan komai”. Suratul Hujurata, aya ta: 16. Ita niyya fa wurin yinta zuciyane, domin tana cikin ayyukan zuciyane ba tana cikin ayyukan harshe ba ne. kuma yana daga cikin hakan yin zikiri na bai-daya bayan sallah, domin abinda aka sani shi ne kowanne mutum ya yi zikirin da aka ruwaito shi kadai. Yana daga cikin haka neman a karanta fatiha a tarurruka da yin addu’a da kuma mamata. Yana daga cikin haka yin bukukuwa ga mamata da yin abinci da dakko masu karatun Alkur’ani da biyansu, wai suna ganin wannan duk yana cikin ta’aziyya, ko kuma zai anfanar da mamaci, kuma dukkanin wadannan bidi’o’ine ba su da asali kuma bala’ine, Allah bai saukar da wani dalili ba akan su. Yana daga cikin haka yin tarurruka na addini, kamar bikin ranar isara’i da mi’iraji, da kuma tarurruka akan hijira (sabuwar shekarar musulunci), wadannan tarurruka da ake yi domin wadannan bukukuwa ba su da wani asali a shari’a, yana daga cikin haka abinda ake yi a watan Rajab, kamar umarar watan Rajab, da ma abinda ake yi na ibadoji na musamman, kamar Tadawwu’i da sallah da azumi, na wannan watan, domin ba shi da wata falala akan sauran watannin, ba’a umara ba hakanan kuma ba’a azumi ba ba kuma a sallah ba, ba kuma a yanka, ba kuma a wanin haka ba. Yana daga cikin haka zikiran sufaye da dukkan nau’ukansu, duk gaba-daya bidi’ane kuma kirkirarrune, domin wadannan zikiran sun sabawa zikirai shar’antattu a sigar da ake yinsu da kuma yadda ake yi haka nan kuma da lokutan da ake yi. Yana daga cikin hakan kebance daren shabiyar ga watan Sha’aban domin yin sallolin, da kuma kebance yinin da yin azumi, domi babu wani abu kebantacce da ya tabbata ba daga Annabirakan hakan. Yana daga cikin hakan yin gini akan kabubura da kuma mayar da su wuraran sallah da ziyararsu domin neman albarka, da neman kamun-kafa (tawassuli) da matattu, da ma wasu banda wadannan da suka kunshi shirka. Da kuma yadda mata suke ziyartarsu tare da cewa Ma’aikin Allah ﷺ ya la’anci mata masu yawan ziyartar kaburbura da kuma wadanda suka daukesu masallatai da kuma masu sanya musu fitilu.Kammalawa: Anan muke cewa; Lalle bidi’o’i hanyace ta kafirci, kuma ita bidi’a kari ce a addini wanda Allah da Manzanshi ba su shar’anta ba, kuma bidi’a ta fi babban laifi sharri, kuma shaidan yana farin ciki da ita sama da yadda yake farinciki da mai aikata babban laifi, domin shi mai laifi yana aikata laifinne kuma yana sane cewa wannan laifine sai ka gay a tuba ya bari, amma mai aikata bidi’a yana aikata bidi’arne yana kuma kudurcewa addini yake yi yana neman kusanci da ita zuwa ga Allah, saboda haka ba zai tuba ya bari ba. Su bidi’o’i suna share sunnoni ne, kuma suna samasu ita kyamar Sunnah da masu bin Sunnah, kuma bidi’a tana nisantar da mutum daga Allah, tana kuma sa Allah ya yi fushi da mutum ya kuma yi masa ukuba, kuma tana sa karkatar zuciya da kuma bacin zuciyar.Yadda ake mu’amalantar ‘yan-bidi’a. Haramun ne ziyartar dan’bidi’a da kuma zama da shi sai dai idan za’a yi masa nasiha ne, ko kuma za’a masa inkarin abinda ya yi, domin sharrin cudanya da shi yana tasiri ga wanda ya cudanya da shi din, kuma adawar da ake da shi zaya watsu zuwa ga waninshi, kuma yana zama wajibi a tsoratar da mutane su da kuma sharrinsu idan ba zai iya yiwuwa a kama su ba, kuma ba zai iya yiwuba a hana su bidi’o’insu ba, idan ko zai yiwu to yana zama wajibi akan malaman musulmi da shuwagabanni su hana wadannan bidi’o’i su kuma rike hannayan ‘yan-bidi’a su kuma yi maganin sharrin su, domin irin hatsarin da suke da shi a musulunci yana da tsanani, sannan kuma yana zama wajibi a sani cewa kasashen da suke kafirai suna karfafar ‘yan-bidi’a ne akan yada bidi’o’insu kuma suna taimaka musu akan haka ta hanyoyi daban-daban, domin ahakan akwai (abinda suke so) na gamawa da musulunci da kuma muzanta tsarinsa. Muna rokon Allah mai girma da daukaka da ya taimaki addininsa, kuma ya daukaka kalmarsa, ya kuma kaskantar da makiyansa, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabimmu Muhammad da iyalansi da kuma sahabbanshi. **** ***** *****