القيوم
كلمةُ (القَيُّوم) في اللغة صيغةُ مبالغة من القِيام، على وزنِ...
Kuma dã lalle an saukar da wani littafi abin karatu wanda ake tafiyar da duwãtsu game da shi, kõ kuma aka yanyanke ƙasa da shi, ko kuwa aka yi magana da matattu da shi (dã ba su yi ĩmãni ba). Ã'a ga Allah al'amari yake gabã ɗaya! Shin fa, waɗanda suka yi ĩmãni ba su yanke tsammãni ba da cẽwa da Allah Yã so, dã Yã shiryar da mutãne gabã ɗaya? Kuma waɗanda suka yi kãfirci ba zã su gushe ba wata masĩfa tanã samun su sabõda abin da suka aikata, kõ kuwa ka saukã* kusa da gidãjẽnsu, har wa'adin Allah ya zo. Kuma lalle ne Allah bã ya sãɓã wa lõkacin alkawari.